Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani
Published: 17th, May 2025 GMT
Tsafta tana kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar mace. Duk da cewa galibi ana alaƙanta tsafta da kyawun gani ko ƙamshi, sai dai a zahirin gaskiya tsafta ta wuce gaban haka ce.
Ita ce turbar zaman lafiya a gidan aure, makamin janyo soyayya, da ginshiƙin lafiyar jiki da tunani.
Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aureWasu matan na iya cika ido da kwalliya a wajen biki ko taro, amma su kan bar gidansu cikin ƙazanta da rashin tsafta.
Tsafta na nufin gyara da killace jiki, gida da muhalli daga datti da duk wani abu da zai iya haifar da wari, cuta ko gurɓata. Tsafta ba wai gyaran jiki kawai ba ce, tana shafar jikinmu, tunaninmu, lafiyarmu da zamantakewarmu.
Kamar yadda wani tsohon karin magana ke cewa, “namiji ƙazami ba ya dawwama da matar tsafta”. A nan za mu fahimci cewa idan mace na da tsafta da ladabi, hatta ɗabi’ar mijinta na iya sauyawa.
Nau’o’in ƙazanta a tsakanin matan aureKamar yadda ake da mata masu tsafta, akwai nau’o’i daban-daban na matan da rashin tsafta ya yi wa ƙatutu. Ga wasu nau’o’in da ke da illa sosai ga zaman aure:
1. Ƙazama ta farko:Ita ce wadda za ka ganta cikin ado da kwalliya a wajen taro, riga ɗauke da ado tsaf, humra da turare, har mutum na iya tsoron kusanci da ita saboda kyan gani. Amma idan Allah Ya kai ka gidanta, sai ka ruɗe: tsakar ga datti, ɗaki da kicin cikin wari da ɗaukar hankali. Wannan na nuni da cewa ado ba yana nufin tsafta ba.
2. Ƙazama ta jiki:Wannan ita ce wadda ko uwa ba za ta so zama kusa da ita ba. Hammata da gaɓoɓin jiki duk sun cika da wari. Rashin wanka akai-akai, rashin amfani da turare ko sabulu mai ƙamshi, duk sun zame mata jiki. A nan, har mijinta zai iya ɗaukan matakin ƙin kusantarta ko ya bar mata gidan gaba ɗaya.
3. Kazama ta zuciya da muhalli:Wannan ita ce mafi hatsari. Ba wai kawai jiki da gida ne suke kasancewa cikin ƙazanta ba, har zuciyarta cike take da gori, tsegumi, rashin ladabi da yawan shiga rayuwar wasu. Gidanta tamkar filin yaƙi yake, yara na yawo da datti, kayan wanki a kowane lungu, ko da dare ko rana babu bambanci. Wannan mace ce da har zuciyarta ba ta son tsafta.
Illar ƙazanta a zaman aureƘazanta tana haifar da matsaloli da dama a gidan aure, kamar haka:
Rage sha’awa da kusanci tsakanin ma’aurata. Hana mijin jin daɗin zaman gida. Sa mijin yanke hukuncin ƙaro mata ko ficewa daga gidan gaba ɗaya. Ƙara zaman ƙunci da rashin nishaɗi. Sa yara su taso cikin halin rashin tsafta da sakaci.Akwai karance-karance da dama da ke tabbatar da cewa tsafta tana rage yiwuwar kamuwa da cututtuka irin su cututtuka masu yaɗuwa, UTI, ko ma zazzabin taifod da ya kan faru sakamakon rayuwa cikin datti.
Muhimmancin tsafta ga mace a gida Tsafta na ƙara daraja da martabar mace a idon mijinta da al’umma. Tana sa yara su taso cikin kyawawan ɗabi’u. Tana ƙara jin dadi da soyayya a tsakanin miji da mata. Ita ce ginshiƙin lafiya da nishaɗi a gidan aure. Gargaɗi da tuni’Yan uwana mata, a yau mace ce ginshiƙin gidanta. Tsaftace jiki, muhalli da zuciya na daga cikin nauyin da ya rataya a kanmu. Idan kin bar kanki cikin halin ƙazanta, ki sani ba mijinki kaɗai za ki sa a wahala ba, har da yaranki da kuma makomar zamantakewarsu.
Ki duba a yau, idan ke ce ke yawan zagi, gori da shisshigi, ko ke ce ke yawan barin gida cikin datti, ki gyara kafin a kai ga faduwa ƙasa babu nauyi. Ka da ki zamo uwa wadda ’yarta ke jin kunya a faɗi cewa ke ce mahaifiyarta.
Tsafta alamar tarbiyya ce, tsafta alamar soyayya ce, kuma tsafta alamar lafiya ce. Idan har muna son zaman lafiya da jin daɗi a gidanmu, musamman a tsakanin ma’aurata, to lallai tsafta ce gaɓar farko da ya kamata mu tsaya mu gyara. Idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira.
“Tsafta na daga cikin sirrin ɗorewar soyayya da martaba a gidan aure.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kwalliya soyayya yara rashin tsafta
এছাড়াও পড়ুন:
Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi
Kishi halak ne kuma so ne yake kawo kishin. Masu irin wannan kishin karshensu nadama ce. Kishi wani abu ne da ake jinsa a cikin rai, kuma kishi ba sai akan aure ake yin sa ba.Hanyoyin da ya kamata abi wajen magance irin wannan shi ne; muna tuna komai yayi farko to yana da karshe, sannan ba kanta farau ba kuma ba kanta karau ba. Muna saka hakuri da tawakkali mu yi kiyayya ba mai zurfi ba, sannan mu yi soyayya ba mai zurfi ba, a karshe sai abin ya zo mana da sauki. Allah ya sa mu dace, amin.
Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:
Abubuwa da dama na haifar da kishi amma mafi lura shi ne rashin godiya a wajen Allah subahanahu wata’ala da kuma son zuciya tare da son rai irin na mata. Kishi shi ne son kasancewa da namiji a matsayin abokin tarayya ko zamantakewar Aure ba tare da wata ta ji ra’ayin hakan ba ko kuma ta nuna bukata tare da ra’ayin akan namijin da wata ke rayuwa da shi ba. Hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin kishi musamman a lokacin da miji zai karo abokiyar zama sun hada da hakuri, danne zuciya, tare da juriya hadi da biyayya ga duk wani umarni daga wajen miji don kuma kaucewa sabawa umarnin Allah da Manzon sa (S.A.W).
Sunana Nabila Dikko, Argungun Jihar Kebbi:
To mafi akasarin dalilai da ke sa mata irin wannan kishi shi ne; karancin fahimta da rashin hakuri, da son mallaki namiji su kadai, da son zuciya, kuma hakan na kawo rashin zaman lafiya da rikici da lalacewar dangantaka. Kishi wani abu ne da ke sa zuciya ta dinga son mallakar wani abu ita kadai ko abin da kake da shi ko tsoron rasa shi. A musulinci, kishi halas ne idan bai kauce wa ka’ida ba. Domin magance kishi dole sai mace ta dogara ga addu’a, ta daidaita tunaninta, ta rungumi gaskiyar cewa mijinta yana iya kara aure, sannan ta mayar da hankali wajen kyautatawa maigidanta ba tare da yin abubuwan da ba su dace ba. Shawarata ga mata su kasance masu natsuwa, su guji haddasa rigima. Sai maza ku kasance masu adalci, ku bayyana gaskiya, ku kiyaye hakkin kowace mata, a daidaita adalci ku daina haddasa tsananin kishi a tsakanin matanku.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To, da farko dai akwai jahilci domin shi ke jawo mutum ya kashe kan sa, don indai mutum yana da ilimi ya san illar kashe kai. Sai na biyu kuma rashin rungumar kaddarar da Allah ya kaddarawa mutum domin ita kaddara bata canjawa. To, kishi wani abu ne da Allah yake halittar mutane da shi maza da mata to a lokuta da dama maza su kan yi kokari wajen sarrafa nasu sabanin wasu daga cikin mata da kishin yake sa su aikata aikin da-na-sani ko ma su hallaka kan su.
Sunana Hafsat Sa’eed, daga Neja:
Kishi yana cikin addinin musulunci amma kuma akwai kishin hauka irin wanda mace za ta je ta hallaka ‘yar’uwarta ko abin da ‘yar’uwarta ta yi sai ta yi. Mutum yana da wahala ya daukowa kansa babban aiki. Idan namiji zai karo aure ya kamata ka bashi goyan baya, ka yi masa fatan alkhairi, haka idan ta shigo ka samu ku zauna lafiya dole akwai abin da zai sa ka yi kishi sai ka yi daidai misali ba wanda ya haura ka’ida ba.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi, daga Jihar Kano:
Babbar magana ai wadanan dai sun hada kansu da wahala da kuma da-na-sani dan kishi dai babu komai a cikinsa sai wahala. To, shashanci ne da rashin sanin ciwon kai. Kishi dai wani halitta ne wani kuwa dorawa kaine, kishiya babu dadi amma ayi hakuri a kau da kai. Sun yi hakuri su kara hakuri.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:
Babu shakka kishi na zama guba a wajen easy matan, musamman a lokacin da mazajen su za su kara aure. Wasu kan nemi jefa kansu ga fushin ubangiji ta hanyar kokarin tilastawa mazajen su jingine bukatar su, ta kara aure, amma kuma su kawar da kai daga halayyar sa ta neman mata a waje. Sannan su a karan kansu, idan ma ba su sha guba sun hallaka kansu ba, suna shiga malamai, matsafa, da ‘yan tsibbu, wadanda ke aikata shirka, don neman biyan bukatun su. Akwai wadanda sanadiyyar kishi suke gamuwa da ciwon hawan jini da ciwon zuciya, ko matsalar kwakwalwa.
Sunana Princess Fatima Mazadu, Goben Nijeriya:
Kishi kam masifa ce babba, soyayya da kauna ke janyo wa wasu kishi, wasu kuma kwadayin dukiya da kyle-kyelen duniya. Danganta kansu ga mutuwa a kowani lokaci namiji bai zamo lallai ya rigata mutuwa ba, sannan mace ta sani lallai kishi halitta ce, amma bai halarta akan auren wata har ya zamo kin iya kashe kanki ba ko saboda abun duniya. Shawarata a nan su rage mummunan kishi, su nemi na kansu, su zamo masu godiya da kulawa a rayuwa wasu matan ko auren ma babu bare kwadayin dukiya da kishi.
Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:
Tabbas ana samun mata masu kishin da ya wuce hankali saboda son zuciya kuma gaskiya makomarsu bata kyau. Kishi dabi’ace da Allah ya halicci mata akai har ma wasu mazan ya kamata su nuna kishinsu ta hanya mafi kyau lokacin da mijinsu zai kara aure kuma su sani da ba a auren da suma ba a aurosu ba. Shawara a nan ita ce kowa ya ji tsoron Allah akan hakan.
Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja Jihar Neja:
Kishiya halitta ce sai dai kowa da yadda yake sarrafa nasa kalar kishin, har kullum muna kira ga matan da suke da tsanani kishi da kar su bari kishi ya rufe masu ido har ya kai ga sun aikata abun da za su zo suna da-na-sani. Biyewa Zuciya, kuma sannan a dabi’ar dan namiji baya son macen da ta cika tsanani kishi. Kishi wata aba ce da ubangiji ke halittar bawa da shi ba tare da ya sani ba. Tsananta addu’a da mika al’amura ga ubangiji a yayin da mijinki ya zo maki da zancen kara aure, dole za ki ji babu dadi a ranki amma in ki ka dage da addu’a sai komai ya zo cikin sauki. Shawara ta kada mu bari zukatanmu ya zamana ita ke sarrafa mu ba mu ke sarrafa ta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA