Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta
Published: 18th, May 2025 GMT
Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar?
Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare?
Akwai wani kirkirarren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan.
Wannan rahoton kadai, zai iya fusata gwamnatin Amurka, ganin cewa, kasar tuni ta yi wa kasar Sin bakin fenti da cewa, ita ce babbar abokiyar hamayyarta a bangaren kasuwanci a duniya.
In ba a manta ba, da ma tun bayan rantsar da gwamnatin Trump, ya sha alwashin kakaba haraji kan duk hajojin da ake shigowa da su Amurka. Hukuncin da gwamnatin ta yanke, lallai ba shakka ba ta canja ra’ayi ba kamar yadda ta yi da sauran sanarwar haraji, wanda hakan ya tabbatar da cewa, yakin cinikayyar duniya har da fina-finai.
Tun ba a yi nisa ba, Amurkawa sun fara dandana kudar yakin cinikayya, inda farashin kayayyaki suka fara tsauri ga ‘yan kasar.
Don haka, akwai yiwuwar Amurkawa za su nisanta daga duk wani fim da aka shirya a ketare da zarar sun ga farashin tikitin ya yi tsada. Shin hakan zai iya zama abin da gwamnatin ke so?
Irin wannan hukunci da Amurka ke dauka, hakan yana da mummunan tasiri akan ‘yan kasarta ko da kuwa lamarin zai shafi sauran ‘yan kasashen waje.
Wai mu tambayi kanmu mana, Amurka ta rasa Dattawa da Masana ne wanda za su ba ta shawara kan harkokin tattalin arziki ne, ko kuwa Gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da shawarwarin su ne?
Masana da dama na ganin cewa, wannan mataki na zabga harajin kashi 100 bisa 100 a fina-finai zai haifar da mummunan sakamako ga masana’antar Hollywood, sannan kuma zai gurgunta kyakkyawar alakarta da takwarorinta na duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga mutanen kasar da daukaka. Don haka gwamnati mutanen kasar ba zasu taba yarda a barshi ba.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da tashar talabijin ta CBS news na kasar Amurka dangane da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar a cikin watan yuni da ya gabata. Hare-haren da aka kaiwa kasar a dai-dai lokacinda take tattaunawa da Amurka.
A wani bangare a maganars Aragchi ya bayyana cewa baya ganin Iran zata farfado da tattaunawa da kasar Amurka nan kusa.
Ya ce: Idan har zamu sake shiga tattaunawa da Amurka sai mun tabbatar da cewa Amurka ba zata kuma kai mana hare-hare a dai-dai lokacinda muke tattaunawa ba.
Ya kara da cewa, tare da wannan tunanin muna ganin sake zama da Amurka kan teburin tattauna ba nan kusa ba. Daga karshe ya ce: a duk sanda muka ga dama ta samu, bama rufe kofar tattaunawa da kowa .
Da aka tamabaye shi dangane da shirin makamashin Nukliya na kasar bayan bom da aka jefa masu. Ministan ya ce: Ai ba’a kauda shirin nukliya da bom. Ko babu shi kwata-kwata zamu sake gina wani daga farko. Sannan idan sun baci ne muna iya sake gyaransu sai mu ci gaba.