Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
Published: 20th, May 2025 GMT
Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu na daban
Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hulan Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu na daban tun daga wayewar garin ranar yau Talata, sakamakon luguden wuta da jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.
Shafin yanar gizo na Palestine Today ya nakalto daga majiyoyin lafiya na cewa: A kalla Falasdinawa 10 ne suka yi shahada sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan makarantar Musa bin Nusair da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar Al-Daraj da ke tsakiyar birnin Gaza.
Wasu 15 na daban kuma sun yi shahada a lokacin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai hari kan gidan mai na Radi a yammacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila suka
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka.
A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma.
Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen more rayuwa da labarin ƙasa ke wakilta a zahiri, ana nufin nazarin abubuwa uku: Wuri, mutane da lokaci. Wato fahimtar nazarin al’amuran ɗan adam a lokuta daban-daban yana samuwa ne ta hanyar nazarin fifikon wuri. Don haka, a cikin binciken a fagen siyasa, za a dogara da wuri a matsayin tushen abubuwan more rayuwa.