Gwamnatin Kano ta dakatar da haska shirin Labarina da Dadin Kowa da wasu 20
Published: 19th, May 2025 GMT
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da haska shirin Labarina, Dadin Kowa da wasu ƙarin fina-finan Hausa guda 20 a kafafen Internet ko gidajen talabijin.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne a ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara dora masana’antar Kannywood a kan saiti.
A cewar wata sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar da daren Lahadi, fina-finan da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Labarina, Dadin Kowa, Manyan Mata, Garwashi, Jamilun Jidda da kuma Gidan Sarauta.
Sanarwar ta ce umarnin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, bayan wani zamanta da kuma tattaunawar da ta gudanar.
An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Jerin fina-finan da aka dakatarSanarwar ta bayyana jerin fina-finan da dakatarwar kamar haka:
Ɗakin Amarya Mashahuri Wasiyya Tawakkaltu Mijina Wani Zamani Mallaka Kuɗin Ruwa Boka Ko Malam Wa Ya San Gobe Rana Dubu Manyan Mata Fatake Gwarwashi Jamilun Jiddan Shahadar Nabila Daɗin Kowa Tabarma Kishiyata da kuma Rigar Aro.Hukumar ta ce ta ɗauki gagarumin matakin ne domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne fim gabanta a tantance shi kafin a sake shi.
Sanarwar ta kuma ce doka ce ta ba Hukumar damar tace duk wani fim tare da lura da ayyukan ’yan masana’antar Kannywood matukar suna da rajista da hukumar a ko ina suke.
“A saboda haka, ana shawartar masu ɗaukar nauyin waɗannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen talabijin ko kafar internet.
“Haka kuma ana sanar da su cewa su miko fina-finansu ga hukumar domin tantance su tare da ba su shaidar inganci ta tacewa nan da sati ɗaya mai zuwa wato daga Litinin, 19 ga watan Mayu, 2025 zuwa 25 ga Mayu, 2025 domin gujewa fushin doka,” in ji sanarwar.
Tun bayan canjin da kasuwar fina-finai dai ta samu da ya sa kuɗaɗen da ake samu a sayar da fina-finai suka yi ƙasa sosai, galibin ’yan masana’antar Kannywood suka koma shirya fina-finai masu dogon zango domin a ci gaba da damawa da su.
Akan ɗora fina-finan ne a dandalin YouTube da wasu gidajen talabijin a mako-mako.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kannywood
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
Daga Usman Mohammed Zaria
Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar.
Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya.
A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali.
A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa taimakon ya zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙata.
A yayin hudubarsa ga fursunonin, Babban Limamin Babura, Imam Salisu Aliyu, ya shawarce su da su nemi gafarar Allah, su kuma kara kusanci gare Shi, tare da rungumar canji mai kyau.
Kayan tallafin da aka bayar sun haɗa da buhunan masara, gero, shinkafa, garin rogo, man gyada, sinadaran dandano, gidan sauro da maganin kwari.
Manyan baƙin da suka raka shugaban ƙaramar hukumar a lokacin ziyarar sun haɗa da Hakimin Babura, Sarkin Bai Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin, CSP Abdu Jinjiri, da jami’in Hukumar Tsaro ta Civil Defence, CSC Sunusi Usman Chamo, da sauransu.