Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu
Published: 19th, May 2025 GMT
Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce duk da matsi sakamakon dalilai na ciki da na waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa daidaito a watan Afirilun da ya gabata.
Alkaluman da NBS din ta fitar a Litinin din nan sun nuna karuwar hajojin da manyan masana’antun kasar ke samarwa da kaso 6.1 bisa dari a shekara, yayin da alkaluman samar da hidimomi suka karu da kaso 6.
Kazalika, alkaluman sun nuna daga watan Janairu zuwa Afirilu, darajar jarin ajiyayyun kadarori a kasar ya kai yuan tiriliyan 14.7, adadin da ya nuna karuwar kaso 4.0 bisa dari a shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan
Rasha ta zama ƙasa ta farko da a hukumance ta amince da gwamnatin ƙungiyar Taliban da ke mulkin ƙasar Afghanistan.
Wannan na zuwa ne bayan Rashar ta karɓi takardun shaidar kama aiki na sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar.
Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar“Mun yi imani cewa wannan matakin na amincewa a hukumance da gwamnatin Daular Musulunci ta Afghanistan zai ba da damar haɓaka haɗin gwiwa mai amfani tsakanin ƙasashenmu a fannoni daban-daban,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Afghanistan ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa jakadan Rasha Dmitry Zhirnov ya gana da Ministan Harkokin Wajen Taliban Amir Khan Muttaqi, inda ya isar da wannan matakin na gwamnatin Rasha da ke nuna “muhimmancin wannan mataki”.
Zhirnov ya bayyana wannan a matsayin “mataki mai tarihi wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Afghanistan ta ce: “Da wannan mataki, dangantakar ƙasashen biyu za ta ƙara faɗaɗa.”
Muttaqi ya nuna fatan cewa wannan zai haifar da ƙarin haɗin gwiwa da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Afghanistan da Rasha.
Zhirnov ya shaida wa tashar talabijin ta gwamnati Rossiya-1 Shugaba Vladimir Putin ne ya ɗauki wannan matakin bisa shawarar Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov. “Wannan yana nuna burin gaskiya na Rasha na kafa haɗin gwiwa mai ƙarfi da Afghanistan,” in ji shi.
Zuwa yanzu dai babu wata ƙasa mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya da ta amince da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Taliban tun dawowarta kan mulki a watan Agustan 2021.