Fransa Ta Kira Yi Kasashen Turai Da Sake Bitar Alakarsu Da “Isra’ila”
Published: 20th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Faransa ya kira yi tarayyar turai da ta sake bitar alakarta da Isra’ila saboda ci gaba da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza da kuma hana shigar da kayan agaji.
Matakin na Faransa dai ya biyo bayan na kasashen Spain, Ireland da kuma Holland, da suke son ganin an gudanar da bincike akan ko hare-haren Gaza din sun karya wani sashe na yarjejeniyar tasu.
Tun a cikin watan Yuni na 2000 ne nahiyar turai din ta kulla yarjejeniyar ayyuka a tsakaninta da HKI a fagage da dama, da hakan ya bai wa Tel Aviv fifiko na musamman a cikin kasuwannin turai. Harkokin kasuwanci a tsakaninsu ya kai dala biliyan 46.8 a 2022.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya bayyana cewa; Saboda matsayar Isra’ila akan gaza, ya zama wajibi a yi bitar alakarta da tarayyar turai.
Barrot ya bayyana tsananta hare-haren akan Gaza da kuma hana shigar da kayan abinci da cewa ” Ba abu ne da za a lamunta da shi ba.”
Haka nan kuma ya bayyana hare-haren na Isra’ila da cewa; cin zarafin Karaman dan’adam ne da kuma keta dokokin kasa da kasa, kuma yana cin karo da tsaron Isra’ila da Faransa ta yi alkawalin karewa,to amma duk abinda mutum ya shuka shi zai girba.
Gabanin Faransa, Faransa, kasar Holland ta yi kira irin wannan na yin bitar alaka da Isra’ila,wacce ministan harkokin wajen na Faransa ya ce, yana goyon baya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ayatullah Khamenei : “Ba inda Rundunar Amurka ta taba shinfida zaman lafiya “
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya caccaki kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan a ziyarar da ya kai a kasashen yankin Gulf na Farisa, yana mai cewa kalaman abin kunya ne a gare shi da dukkan Amurkawa, kuma bai cancanci amsa ba.
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar masu bayar da ilimi daga sassan kasar.
Ya kara da cewa wasu kalaman na Trump ba su ma isa a mayar da martani ba, yana mai kiransu da cewa abin kunya ne ga shi kansa shugaban Amurka da kuma wulakanci ga al’ummar Amurka.
‘’Ikirarinsa na cewa yana son samar da zaman lafiya da tsaro, zencen banza ne’’ inda ya kara da cewa Amurka na baiwa gwamnatin sahyoniya tan-tan na bama-bamai tana jefa su kan yara, asibitoci da gidajen jama’a a Gaza, Lebanon da kuma duk inda ta ga dama.
A yayin rangadin da ya ke a kasashen yankin Gulf, shugaban na Amurka ya yi jawabai da dama na sukar Iran.
A ziyarar da ya kai kasar Saudiyya, Donald Trump ya bayyana cewa “shugabannin Iran sun mayar da hankali wajen sace dukiyar al’ummarsu domin tallafawa ayyukan ta’addanci da zubar da jini a kasashen waje.”
Bayan hakan kuma, ya bayyana a Qatar cewa Amurka da Iran na daf da kulla yarjejeniyar nukiliya, kafin ya bukaci Iraniyawa da su “tashi” kan wannan batu “in ba haka ba wani mummunan abu zai faru.”, kallaman da jagoran juyin juya hali da shugaban kasar ta Iran sukayi fatali dasu.