Aminiya:
2025-11-27@21:15:20 GMT

ISWAP ta yi wa manoma 15 yankan rago a Borno

Published: 17th, May 2025 GMT

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi wa manona da masunta aƙalla 15 yankan rago a yankin Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kulawa ta Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan na ISWAP sun kutsa yankin ne bayan zagargaza da tarwatsa sojoji suka yi wa maɓoyarsu da ke Dajin Sambisa.

Shaidu sun bayyana cewa a ranar Laraba da manoman da masunta suka tafi gonakinsu da wurin yin su ne suka yi arba da mayaƙan ƙungiyar da suka yi musu kisan gilla.

Sun bayyana cewa dai da mayaƙan suka tafi da manoman zuwa ƙauyen Malam Karanti, da suka kwace, sa’annan sun yi musu yankan rago.

Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas

 

 

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba.

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna

Waɗanda aka zaɓa su haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke.

Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.”

Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu.

Mutane da dama sun daɗe suna ƙorafin kan jinkirin naɗa jakadun.

Amma wasu na ganin aike sunayen jakadun na da alaƙa da barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na ɗaukar matakin soji a kan Najeriya, kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

A wata hira da aka yi da shi a watan Satumba, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce babu wata matsala game da jinkirin.

Ya ce, “Dukkanin ofisoshin jakadancinmu suna aiki yadda ya kamata. Kowace ofishi yana gudanar da ayyukansa yadda ya dace. Rashin jakadu ba zai haifar da giɓi ba.”

Ya ƙara da cewa duk da cewa jakada shi ne shugaban ofishin jakadanci, akwai kwamishinoni, wakilai da ma’aikatan diflomasiyya da ke tafiyar da harkokin yau da kullum.

A cewarsa, “Diflomasiyya ba aikin mutum ɗaya ba ne. Tsarin ya tanadi irin wannan yanayi.”

Tuggar, ya kuma ce shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon naɗa jakadu, kuma zai yi hakan a lokacin da ya dace.

Ya bayyana cewa, “Shugaban ƙasa yana duba batun, kuma za a sanar da sunayen a lokacin da ya dace.”

Ya ƙara da cewa, “’Yan Najeriya a ƙasashen waje har yanzu suna samun ayyuka, kuma mu’amala da ƙasashen da muke hulɗa da su ba ta ragu ba.”

Ya ce kuma akwai ƙasashe da dama da suka shafe dogon lokaci ba tare da jakadu ba, amma hakan bai lalata dangantakarsu da wasu ƙasashe ba.

Ya ce, “Wannan ba sabon abu ba ne. Diflomasiyya tana da tanadin irin wannan yanayi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne aiki, ba kwaikwayo ba.”

A ƙarshe ya ce Najeriya tana aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran ƙasashen duniya.

“Manufofin ƙasashen waje na Najeriya sun bayyana, kuma ana jinmu a duniya. Abin da muke yi shi ne tabbatar da cewa ofisoshinmu suna samar da sakamako mai amfani ga ’yan Najeriya.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina