Aminiya:
2025-05-19@17:38:57 GMT

Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma

Published: 19th, May 2025 GMT

‍‍‍‍‍‍

Seyi Tinubu, ɗan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na cikin tawagar mahaifinsa da ta ziyarci fadar Vatican a ranar Lahadi domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo XIV.

A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya gana da Fafaroma har suka gaisa.

Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5 NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a?

Amma abin da ya ja hankalin mutane shi ne lokacin da Seyi ya yi ƙoƙarin zuwa wajen mahaifinsa yayin da yake gaisawa da Fafaroma.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wani jami’in tsaro ya dakatar da Seyi cikin ladabi, yana nuna masa cewa bai kamata ya matsa kusa da wajen da suke ba.

Seyi na sanye da baƙar kwat kamar yadda mahaifinsa ya sanya, ya yi ƙoƙarin isa waje shugaban ƙasa, amma jami’in tsaron ya hana shi.

Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane ke yabawa da yadda jami’an tsaron Vatican ke aiki da tsari da ƙa’ida.

Shugaba Tinubu ya kuma gana da tsohon abokin hamayyarsa a zaɓen 2023, Peter Obi, wanda ya kayar da shi a Jihar Legas a lokacin zaɓen.

Kalli bidiyon a nan ƙasa:

https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/05/vid-20250519-wa0023.mp4

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fadar Vatican Jami an Tsaro Sabon Fafaroma

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa

Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa.

Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038.

An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso

Kuɗin mallakin Maimuna Salihu, wata maniyyaciya daga Jihar Taraba da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana.

Jami’in ya mayar mata da kuɗin a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025.

An gudanar da bikin miƙa kuɗin a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ciki har da jami’in Taraba, Daraktan Tsare-tsare, da wasu manyan jami’ai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata ‘Yar Jarida Ta Nuna Mamaki Kan Nuna Damuwa Da Ciwon Biden Maimakon Kisan Gillar ‘Yan Sahayoniyya
  • An kashe ’yan kasuwa 15 a wani sabon hari a Binuwai
  • Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa
  • Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina
  • Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma
  • Jami’ar FUDAMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina
  • Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya
  • Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno
  • Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa