Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci
Published: 16th, May 2025 GMT
Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma.
Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar ke yi, wajen bayar da tallace-tallacen da suka shafi bangaren aikin noma, inda suka yi nuni da cewa, kafafen yada labarai; sun dogara ne kacokan a kan samun tallace-tallace, wanda akasari shi ne ke rike da su.
Sun kuma bukaci a samar wa da kafafen yada labaran kasar, wata hanyar sadarwa ta bai daya, musamman domin su kara wallafa rahotannin da suka shafi ayyukan gwamnatin kasar na aikin noma.
Mahalarta taron, sun kuma amince da kara daga matsayin aikin noma na kasar, ciki har da bai wa ‘yan jarida horo a kai-kai kan abin da ya shafi wallafa rahotannin aikin noma.
Sahen na PFSCU, ya mayar da hankali ne wajen ganin yin hadaka da cibiyoyi, musamman domin gwamnatin tarayya ta cimma burin samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kara habaka fannin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Farming kafafen yada
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…