HausaTv:
2025-05-01@04:07:46 GMT

Argentina Ta Sanar Da Ficewarta Daga Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO

Published: 6th, February 2025 GMT

Gwamnatin kasar Argentina ta sanar da ficewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO.

Mai magana da yawun shugaban kasar Manuel Adorni ya fadawa taron manema labarai cewa, shugaban kasar Javier Milei, ya umarci ministan harkokin wajen kasar Gerardo Werthein, da ya dauki matakin janye Argentina daga hukumar lafiya ta duniya.

Adorni ya ce, ” ‘yan Argentina ba za su kyale wata kungiya ta kasa da kasa ta tsoma baki a harkokin da suka shafi ‘yancin kasarmu ba. “

Ya kara da cewa,”Ya kamata a fayyace cewa Argentina ba ta karbar kudade daga hukumar ta WHO don kula da lafiya, don haka, wannan matakin, kamar yadda wasu ke cewa, a kalla a shafukan sada zumunta, ba ya wakiltar asarar kudade ga kasar, kuma ba ya shafar ingancin ayyuka da  hidimomi.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura

Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.

Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana.

A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar.

Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar.

Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu.

Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin dadinsa game da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a yankin, yana mai kira gare su da su ci gaba da gudanar da rayuwa cikin fahimta da hadin kai.

Haka zalika, yayin taron, Shugaban Sashen Noma da Albarkatun Kasa, Malam Lawan Sabo Kaugama, ya bayyana cewa an ware cibiyoyi guda goma sha biyu domin gudanar da aikin rigakafin wanda ake sa ran zai dauki kwanaki hudu.

Ya yaba da kokarin gwamnatin jiha da ta karamar hukuma wajen samar da allurar rrigakafn da kuma duk wasu kayan aiki da ake bukata.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya
  • Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar