Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro
Published: 16th, May 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa.
An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a YobeTinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu ƙirar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Bikin ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin.
Ya ce Najeriya na buƙatar ingantaccen tsaro domin ’yan ƙasa su samu damar yin harkokin rayuwa cikin kwanciyar hankali.
“Dimokuraɗiyya da tattalin arziƙin Najeriya na buƙatar cikakken tsaro. Dole ne a murƙushe waɗanda ke barazana ga zaman lafiya.
’Sojoji masu ƙarfi da kayan aiki masu inganci na da muhimmanci ga makomar ƙasar nan,” in ji Tinubu.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sabunta kayan aikin soji tare da saka hannun jari a fannin tsaro don tunkarar barazanar ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.
“Wannan ci gaban zai taimaka wajen jawo saka hannun jarin a cikin gida da waje, sannan ya samar da cikakken tsaro a ƙasa,” in ji shi.
Ya kuma buƙaci rundunar soji da ta kasance a shirye don samar da zaman lafiya.
A nasa jawabin, Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya bayyana cewa sabbin jiragen suna da amfani matuƙa ga harkokin soji da na jin-ƙai.
Ya ƙara da cewa, tuni aka karɓi sabbin jirage tara tun daga shekarar 2024, kuma ana sa ran samun wasu 49 cikin shekaru biyu masu zuwa, ciki har da jiragen yaƙi na zamani da na ɗaukar kaya.
Abubakar, ya bayyana cewa an riga an horar da matuƙa jirage takwas da injiniyoyi 18 don aiki da sabbin jiragen, yayin da wasu ke ci gaba da karatu a ƙasashen waje.
Tinubu, ya buƙaci rundunar sojin sama da ta kula da sabbin jiragen da ƙwarewa domin amfanin ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: matsalar tsaro Sabbin Jirage Tsaro yaƙi sabbin jiragen
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…