Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200
Published: 19th, May 2025 GMT
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi bankwana da maniyyata 966 da za su je aikin Hajjin bana, inda ya buƙace su da su kiyaye dokoki da tsarin ƙasar Saudiyya.
Gwamnan, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, wanda ya gargaɗi maniyyatan da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci.
Gwamnan ya bai wa kowane maniyyaci kyautar Riyal 200 a matsayin goron Sallah.
An kuma ja hankalin maniyyatan da ka da su karɓi kaya ko rigar wani, ko da ’yan jiharsu ne, don kauce wa matsala.
Malaman addini da suka halarci taron sun shawarci maniyyatan da su yi aikin Hajji da nufin samun lada, su nemi ƙarin haske idan ba su fahimci wani abu ba, sannan su yi addu’a don samun zaman lafiya a Najeriya.
Hakazalika, an tunatar da su, su kula da kayansu don kaucewa shiga matsala.
Sakataren hukumar Alhazai na jihar, Alhaji Sa’adu Hassan, ya bayyana cewa aikin Hajji ibada ce, ba yawon shaƙatawa ba, don haka ya buƙace su, da su mayar da hankali wajen gudanar da ibadarsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bankwana kyauta maniyyata Riyal
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro
Gwamnatin Jihar Yobe, ta sanar da rufe kasuwannin garuruwan Katarko, Kukareta da Buni Yadi saboda barazanar matsalar tsaro.
Wannan mataki na ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnatin ke ɗauka domin inganta tsaro a yankunan.
Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a KwaraSanarwar ta fito ne daga babban mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya).
Ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne domin a samu damar gudanar da wasu ayyuka na musamman da suka shafi tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce wannan matakin na ɗan lokaci ne, kuma yana da nufin tabbatar da ci gaba da samun nasara a yaƙi da ‘yan ta’adda a jihar.
“Ko da yake hakan zai kawo ƙalubale ga al’umma, amma wajibi ne domin a cimma babban burin tsaro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin na aiki tuƙuru don ganin an rage wa mutane raɗaɗin da wannan mataki zai haifar.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ba da haɗin kai da fahimta don a samu nasarar ayyukan tsaro da kuma wanzar da zaman lafiya gaba ɗaya a jihar.
Har ila yau, ya tabbatar wa al’umma cewa da zarar abubuwa sun daidaita, za a sake buɗe kasuwannin.