Kotu A Iran Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan ‘Yan Ta’adda Da Suka Kai Hari Kan Hubbaren Shah Cheragh
Published: 18th, May 2025 GMT
An zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane 3 da ake zargi da kai harin ta’addanci a hubbaren Shah Cheragh
Shugaban hukumar shari’a ta lardin Fars (a kudancin Iran) ya sanar da cewa: Kotun Musulunci a birnin Shiraz ta yanke hukunci kan wasu mutane 7 da ake tuhuma da hannu a harin ta’addancin da aka kai a hubbaren Shah Cheragh (Ahmad ibn Imam Musa al-Kazim, amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Haka nan kuma yayin da yake ishara da hukuncin da aka yanke wa mutanen bakwai da suka kai harin ta’addanci a hubbaren Shahragh, Hujjat al-Islam Sayyid Sadrullah Raja’i Nasab ya ce: A cikin hare-haren ta’addancin da aka kai a hubbaren Shahragh, baya ga manyan wadanda suka kai harin da aka hukunta bisa ayyukansu; An kuma hukunta wasu mutane saboda goyon baya da kuma tarayya da suka wajen samar da makamai da alburusai. Sannan bisa taimakon matakan leken asirin da aka sanya a cikin ajandar mai bincike na musamman da jami’an tsaro bayan faruwan wadannan al’amura, an gano wadannan mutane, an kama su, kuma sannan an dakile shirinsu na ta’addanci.
Hukunce-hukuncen sun hada da hukuncin kisa ga wasu mutane uku da aka samu da laifin “taimakawa wajen yada barna a kan doron kasa,” kuma an bayyana wadanda ake tuhumar a matsayin “masu kitsa” ayyukan ta’addanci. An kuma yanke musu hukuncin daurin shekaru 25 a kan kowane wanda ake tuhuma bisa zargin “taimakawa wajen gudanar da barna.”
An yanke wa wani dan ISIS hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari, wani kuma shekaru 10 da kwana daya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wasu mutane
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.
Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku.
Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar.
Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shawarwari domin biyan muradun kasashen uku wajen tinkarar manufofin kasashen yamma, musamman takunkuman Amurka.
Tawagogin sun amince su ci gaba da bude hanyoyin karfafa alakokinsu da kuma ci gaba da gudanar da taruka a nan gaba a matakai daban-daban a cikin makonni masu zuwa, a wani bangare na abin da suka bayyana da “kokarin hadin gwiwa na tallafawa zaman lafiyar yankin da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.”