Tawagar NAHCON Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Jihar Jigawa
Published: 18th, May 2025 GMT
Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya karɓi tawagar jami’an Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) tare da kamfanin Max Air domin duba kayayyakin aikin hukumar.
A jawabinsa, mataimakin mai kula da ofishin hukumar da ke Kano, Mista Barnabas Anderson, ya ce manufar wannan ziyarar ita ce don yin binciken gaggawa da tabbatar da ingancin kayan aikin hukumar kula da alhazai ta jihar.
Ya ƙara da cewa, tawagar ta tantance kayan aiki, shirin jigilar maniyyata na jihar, takardun tafiya, fasfo da kuma kayan aikin sansanin Alhazai.
Ya bayyana cewa, za a yi jigilar rukuni na farko na maniyyata 550 daga jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayun 2025, yayin da rukuni na biyu za su tashi ranar 21 ga watan Mayun.
Mista Anderson ya nuna gamsuwarsa da yadda hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da aikin hajjin bana.
Shi ma da yake jawabi, Daraktan Janar na Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya jaddada cewa an samu nasarori da dama a shirye-shiryen aikin hajjin 2025 a jihar.
Ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar wajen tabbatar da jin daɗin maniyyata daga Jigawa, a gida Najeriya da kuma ƙasar Saudiyya.
Labbo ya yaba wa NAHCON bisa goyon baya da haɗin kai da take bai wa hukumar domin nasarar aikin hajjin bana.
Tawagar ta ziyarci sansanin horaswar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC na Yakubu Gowon da ke Fanisau, inda nan ne sansanin Alhazai na wucin gadi da kuma Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa Muhammadu Sunusi.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa, Daraktan Janar din ya kuma kaddamar da tawagar ‘yan jarida na aikin hajjin 2025 a ofishinsa.
Ya yi kira ga ‘yan jaridar da aka zaɓa da su tabbatar da kiyaye dokoki da ka’idojin aikin jarida yayin da suke a Ƙasa Mai Tsarki.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Nada Kwamishina Na Farko A Ma’aikatar Cigaban Kiwon Dabbobi
Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma.
Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, baya ga noma, kiwon dabbobi shi ne babban abin da mutanen jihar Jigawa suka sanya a gaba.
Malam Umar Namadi ya kara da cewa kafa wannan ma’aikata na cikin shirin gwamnati na bude manyan damarmaki da ke cikin wannan bangare.
“Mun dauki mataki na musamman domin ingantawa da bunkasa bangaren kiwon dabbobi. Mun yi hadin gwiwa da dama, mun yi tuntuba da dama, kuma nan gaba kadan za a fara ganin sakamakon wannan tuntuba. Bisa wannan dalili muka ga ya dace mu kafa ma’aikatar da za ta jagoranci wannan aiki gaba.”
Game da zaben kwamishina na farko, Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwa a kan kwarewar Farfesa Salim Abdurrahman.
“Mutumin da aka rantsar a matsayin kwamishina na kiwon dabbobi, kwararre ne kuma masanin a wannan fannin. Daga digirinsa na farko zuwa na biyu har na uku (PhD), duk ya yi su ne akan ilimin dabbobi. Don haka babu wani da ya fi dacewa da wannan aiki fiye da Farfesa Salim.”
Yayin da yake taya Farfesa Salim Abdurrahman murna, Gwamnan ya tunasar da shi muhimmancin wannan mukami na farko da yake rike da shi, yana mai kira gare shi da ya yi aiki domin amfanin jama’ar jihar Jigawa.
“Ina sanar da kai cewa kana daf da kafa tarihi domin kai ne kwamishina na farko na wannan ma’aikata. Don haka idan ma’aikatar ta yi tasiri ga rayuwar mutanen jihar Jigawa, tarihi zai yi alfahari da kai”.
Namadi ya yi addu’ar samun nasarar wannan ma’aikata wajen inganta rayuwar al’umma a fadin jihar.
Usman Mohammed Zaria