Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce Ba Ta Tsoron Duk Wata Barazana Don Neman Tauyaye Mata Hakki
Published: 17th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki.
A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai jaddada cewa; Ya ku masoya, hangen nesa na sojojin ruwa da dukkanin masu kare wannan kasa mai tsarki suke dauke da shi abin alfahari ne a gare kasar Iran.”
Ya kara da cewa: A kodayaushe ya yi imanin cewa: Iran ba za ta amince da kasance kasa da sauran kasashe a kowane fanni ba. Nasarorin da Iran ta samu wajen samar da jiragen ruwa na karkashin ruwa, masu dauke manyan makamai masu tarwatsa jirgi, da makamai da aka kera a cikin gida, ba tare da dogaro da bangarorin ketare ba, da mayar da Iran ta zama mai fitar da kayan soja zuwa kasashen waje, abin alfahari ne.
Shugaban ya yi gargadi kan yunkurin makiya na yada dabi’ar nuna gajiyawa a tsakanin al’ummar Iran, da haifar da sabani a tsakanin jami’ai, yana mai cewa: A karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci, hadin kai ya fi karfi a yau fiye da kowane lokaci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shuagabn Kasar Amurka Ya Sanar Da Kusancin Kulla Yarjejeniya Da Iran
Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita.
Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da ake yi a tsakanin Amurka da Iran akan shirinta na makamashin Nukiliya.
Shugaban kasar ta Amurka dai ya bayyana hakan ne dai a lokacin da yake Magana da manema labaru a birnin Doha na kasar Katar.
Da yake Magana akan yakin kasar Ukiraniya da Rasha, shugaban kasar ta Amurka ya kuma bayyana imaninsa da kusancin kawo karshen yakin tare da cewa yana kokarin ganin an kawo karshen rikici a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana yadda jiragen sama marasa matuki suke taka rawa a fagen yakin kasar Ukiraniya da sauran yake-yake.