Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa
Published: 6th, February 2025 GMT
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ishaq Yunus Almadany, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin 44 Army Reference da ke Kaduna.
An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti Tinubu ya sauke shugabar Jami’ar Abuja, ya yi sauye-sauye a jami’o’in NajeriyaJami’in hulɗa da jama’a na na kafafen sada zumunta na ƙungiyar Izalatul Bidia Waikamatus Sunnah (JIBWIS), Ibrahim Shehu Giwa ne, ya tabbatar da rasuwar.
Shugaban JIBWIS reshen Jihar Kaduna, Alhaji Adamu Ibrahim, ya bayyana alhininsa, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta masa Ya kuma Aljanna makomarsa.
Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, shi ma ya sanar da rasuwar malamin a shafinsu na Facebook, inda suka yi addu’ar Allah Ya jiƙansa.
Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5 na yamma a filin idi na Sultan Bello, da ke Kaduna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rashin lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp