Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara
Published: 18th, May 2025 GMT
Wani hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 37 a ƙauyen Gbajibo-Mudi da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.
Hatsarin wanda ake fargabar ya auku ne a sanadiyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata.
Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo AwoniyiLamarin na zuwa ne watanni bakwai bayan aukuwar makamancinsa wanda ya janyo asarar fiye da mutum 106 a jihar.
A cewar wani mazaunin yankin, kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji kimanin 150 ya kife ne a tsakiyar ruwa.
Bayanai sun ce waɗanda lamarin ya rutsa da su na komawa gida ne bayan cin kasuwa a tsallake kogin.
Sai dai kuma an alaƙanta faruwar lamarin da saukar mamamkon ruwan sama da iska mai ƙarfi da suka sanya kwale-kwalen ya riƙa tangal-tangal ɗauke da fasinjojin da suka haɗa har da mata da ƙananan yara.
Aminiya ta ruwaito cewa an ceto mutane 47, yayin da ragowar da suka iya ruwa suka fidda kansu zuwa gaɓar kogin.
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kaiama, Saidu Baba ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun ziyarci ƙauyen tare da Sarkin Kaiama da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar.
Ya ce mazauna ƙauyukan Tungamaje da Gelewa abin ya fi shafa, yayin da limamin ɗaya ƙauyen Tungamaje ya ce sun yi asarar rayukan mutane 27 da ciki har da mata bakwai da yara biyu.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Kaiama, Abdullahi Danladi, ya ce ba za su zuba ido ba a riƙa samun aukuwar hatsarin kwale-kwale kusan duk shekara.
Ya bayyana cewa sun fara shirin kafa wani kwamiti da zai tilasta ɗauka da kuma tanadar matakan kariya yayin hawa kwale-kwale ciki har da sanya rigar ruwa da kuma haramta tafiyar dare da makamantansu.
Sarkin Kaiama, Alhaji Muazu Umar, ya nanata muhimmancin wayar da kan fasinjoji da masu jiragen ruwa dangane da kiyaye matakan kariya yayin duk wani sufuri da za su yi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kwara Kifewar kwale kwale kwale kwale
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna.
Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan NajeriyaYa bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.
Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu.
Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda.
A gefe guda kuma, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ra lamunci tashin hankali ko rikicin siyasa a Kano ba.