Leadership News Hausa:
2025-10-13@19:34:59 GMT

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Published: 16th, May 2025 GMT

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Haramun ne ga mai harama namiji ya daura duk wani abu dinkakke, sai dai hirami kawai. Amma idan bai samu hirami ba, babu laifi ya daura wando kamar yadda Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito daga cikin hudubar da Annabi (SAW) ya yi a ranar Arfa.

Idan mai harama bai samu silafas ba, zai iya sanya takalmi sawu-ciki, amma ya yanke shi zuwa karkashin idon sawunsa kamar yadda ake wa khuffi.

Wannan duk an haramta ne ga namiji. Amma ita mace babu abin da ya haramta mata illa sanya turare, nikabi da safar hannu, kamar yadda Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW). Haka nan kar ta sanya kayan da aka yi musu rini da turare, amma idan rini ne kawai babu turare shikenan. Bayan wannan, za ta iya sanya duk abin da take so.

Akwai Malaman da suka yi shisshigin cewa mace za ta iya sanya nikabi, amma kuma ya kamata a fahimci cewa idan Shari’a ta zo da abu, namu bi ne kawai. Don wandanda suke ganin za a iya rufe fuskar saboda kishin matan ai ba su kai Annabi (SAW) kishi ba. Ya kamata a yi hattara.

Haramun ne mai harama da Hajji ya yi aure ko ya daura wa wani ko wakilta wani. Idan kuma aka yi, to ya baci.

Ba a yarda mai harama ya yanke farce ko cire gashinsa a ko wace gaba ba (askewa ko ragewa). Amma an yi sauki idan farcen ya karye, babu laifi a cire gutsiren da ya rage shi kadai. Idan kuma yana cutuwa da gashin wani wuri a jikinsa, zai iya cirewa amma sai ya ba da hadaya.

Game da gashin gira, sauran Maz’habobi sun ce za a iya cirewa babu komai, amma Imam Malik ya ce shi ma sai an ba da hadaya.

Haramun ne sanya turare walau ga namiji ko mace. Za a iya sanyawa ne kafin a yi harama. Hatta Alhajin da ya mutu a wurin Aikin Hajji ba a sanya ma sa turare bayan an ma sa wanka. Annabi (SAW) ya ce “Idan Alhaji ya mutu, kar a rufe ma sa kai, kar a sanya ma sa turare, zai tashi ranar kiyama a matsayin Alhaji.”

Babu laifi idan turaren da ake shafa wa Ka’aba ya shafi mayafin Alhaji, ba sai ya wanke ba. Amma dai kar mutum ya je da gangar da nufin shafawa.

Haramun ne ga mai harama ya yi farauta a kan kasa ko ya nuna wa wani abin farautar ko ya taimaka wa mai yi, amma ya halasta ya yi a cikin ruwa kuma ya ci. Hukuncin wanda ya aikata daya daga cikin abubuwan nan da aka hana bisa uzuri (ban da saduwa da iyali) shi ne, ya ba da hadayar akuya. Idan ba shi da ita sai ya ciyar da miskinai shida. Ko wane miskini a bashi rabin sa’i. Ko kuma ya yi azumin kwana uku. Wanda ya yanke gashinsa guda uku ko abin da ya fi haka, zai yi fidiya da akuya. Imamus Shafi’i ya ruwaito cewa idan mutum ya tsige gashi daya, hukuncinsa shi ne ya ba da abinci cikin tafi daya (Muddan Nabiy daya), idan ya tsige biyu; zai ba da biyu, idan yawansu ya kai uku; sai ya ba da jini (akuya).

Haka nan ba a so Alhaji ya shafa mai (mai kamshi ko mara kamshi) lokacin da yake cikin harami. Idan ya shafa, hukuncin ba da jini (akuya) ya hau kansa. Imam Abu Hanifa ya ce a ko wace gaba aka shafa; wannan hukuncin ya hau kan mutum, ba a kebe wasu gabobi da aka amince a shafa musu ba. Amma a wurin Imam Shafi’i, idan an shafa wa kai ko gemu ne hukuncin jinin yake aukuwa. Koda yake shi ya yi sauki a kan shafa mai mara kamshi, sai dai shi ma ban da kai da gemu.

 

Hukuncin Saduwa Da Iyali A Hajji

Babu abin da yake bata Aikin Hajji kada’an da ba za a iya gyarawa da kaffara ba sai Saduwa da iyali.

Sayyidina Aliyu (RA) da Sayyidina Umar (RA) da Sayyidina Abu Huraira (RA) sun ba da fatawar cewa duk wanda ya sadu da iyalinsa bayan ya yi harama da Aikin Hajji, Hajjinsa ya baci. Kuma wajibi ne ya ci gaba da aikin har ya kammala. Sannan zai ba da rakumi ko saniya, ya kuma dawo wata shekarar ya sake yin wani Hajjin.

Abul Abbasid Dabari, ya ce idan mai Aikin Hajji ya sadu da iyalinsa kafin halastawa karama, Hajjinsa ya baci. Ma’anar halastawa karama ita ce daga lokacin da mutum ya yi harama zuwa tsayuwar Arfa har zuwa Jifa na ranar Sallah da hadaya da aski ko saisaye, sai bai samu ya tafi Makka ya yi Dawafi ba, to an halasta ma sa abubuwan da aka haramta ma sa lokacin da ya yi harama (irin su sanya kayan gida, aski, shafa turare, shafa mai da sauran su) amma ban da saduwa da iyali.

Ita ma matar da aka sadu da ita alhali ta yi harama da Hajji, Hajjin nata ya lalace, kamar yadda wasu malamai suka bayyana. Ita ma za ta karasa sauran ayyukan da suka rage, kuma za ta ba da jini (rakumi ko saniya). Koda yake akwai Malaman da suka ce idan ita da mijin suka ba da daya (rakumin ko saniya) ya isar musu, ba sai ita matar ta bayar da nata daban ba.

Idan za su dawo wata shekarar su rama Hajjin, shari’a ta ce a raba tsakaninsu domin rigakafin sake aukuwar hakan.

Idan wanda ya sadu da iyalinsa ya kasa ba da rakumi; sai ya ba da saniya, idan ya kasa; sai ya ba da awaki, idan ya kasa; sai a yi ma sa kimar kudin rakumin ko lissafin adadin abinci ya bayar. Ko wane Miskini zai ba shi Muddan Nabiy daya. Idan kuma bai samu ba, sai ya yi azumi na adadin yawan Muddan Nabiy da zai bayar.

Amma su a wurin Ma’abota Zahiri, idan mutum ya sadu da iyalinsa Hajjinsa ya baci sai dai zai ba da akuya ne kawai.

A wani hukuncin kuma, idan mutum ya sadu da iyalinsa bayan halastawa karama, to babu komai a kansa, kamar yadda galibin Malamai suka tafi a kai. Sai dai wani sashen na Malamai sun ce mutum zai rama kuma hadaya ta wajaba a kansa, kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bin Umar (RA), Hasanul Basri, Ibrahimun Naka’i. Abdullahi bin Abbas (RA) ya karfafa batun ba da rakumi kamar yadda shi ma Ikrimah ya fada. Imamu Malik da Imamu Shafi’i su kuma sun yi sauki inda suka ce a ba da akuya.

Idan Alhaji ya yi mafarki ya sadu da iyalinsa har maniyyi ya fito, ko ya dinga tunanin saduwa har maziyyi ya fito ma sa ko kuma saboda kallo na sha’awa ya fitar, Hajjinsa bai baci ba kuma babu komai a kansa. Saboda yin hakan ba saduwa ba ce. Amma kuma duk wanda ya shafa mace da nufin sha’awa ko ya sumbace ta da sha’awa; zai ba da akuya, walau ya fitar da maniyyi ko maziyyi ko bai fitar ba. An ruwaito wannan ma daga Abdullahi bin Abbas (RA).

Yana da matukar kyau kowa ya kiyaye wadannan abubuwa domin a samu Hajjin da ya kubuta daga dukkan aibi, ma’ana Hajjan Mabrur.‎ Allah ya ba da iko.

Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa, in sha Allahu za mu zo da bayani a kan abubuwan da ake so mai shiga Makka ya aikata. Allah ya nuna mana cikin koshin lafiya.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Umrah ya sadu da iyalinsa sai ya ba da a yi harama kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka

Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje.

 

A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi.

 

Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga.

 

Idan ma Masar ta yi rashin nasara a wasan, za ta fatata da Guinea-Bissau a ranar Lahadi. Burkina Faso kuma wadda take kokarin zuwa ta biyu za ta buga wasa ne da kasar Saliyo, sai kuma kasar Habasha, amma tana bukatar samun nasara a wasannin kafin samun gurbin buga wasannin raba-gardama.

 

A rukunin (B) kuwa nasarar da Senegal ta samu a kan DR Congo ce ta ba ta damar darewa teburin rukunin, inda yanzu ta ba da tazarar maki daya. Tawagar ta Teranga Lions za ta je wasa da Sudan ta Kudu wadda ke karshen teburi, sai ta buga wasan karshe da Mauritania, inda take bukatar nasara biyu domin samun shiga gasar.

 

DR Congo dai na fatan Senegla ta yi rashin nasara, ita kuma ta samu nasara a wasannin biyu a gidan Togo da kuma Sudan a gida. Sudan na bukatar nasara a duka wasanninta, sannan Senegal ta yi rashin nasara wasanninta biyu domin samun gurbin zama ta daya a teburi, amma tana da damar zuwa ta biyu idan ta doke Congo.

 

A wannan rukunin kuma bayan hukuncin da FIFA ta dauka a kan kasar Afirka ta Kudu na cire mata maki uku saboda sanya dan wasan da bai cancanta ba a wasanta da kasar Lesotho.

 

Yanzu Benin ce kan gaba a rukunin, inda take saman Afirka ta Kudu da bambancin kwallaye, sai Nijeriya da Rwanda suke da maki da na hudu, amma duk suna da damar samun gurbi.

 

Benin na da wasa a gidan Rwanda da Nijeriya, sai tawagar Afirka ta Kudu za ta buga da Zimbabwe, sai Rwanda a gidanta. Nijeriya tana da wasa a gidan Lesotho sai Benin, kuma dole ne ta ci wasanninta guda biyu, amma ko da ta lashe wasannin, sai yadda ta wakana a sauran wasannin kafin sanin matsayarsa.

 

Nasarar da Cape Berde ta samu a kan Kamaru da ci daya mai ban haushi a watan jiya ta sa kasar ta kama hanyar kafa tarihin zuwa gasar cin Kofin Duniya na farko a tarihinta.

 

Yanzu kasar na bukatar nasara daya kacal a wasanta da Libya ko kuma a wasanta a gida da kasar da ke karshen teburi, wato tawagar ‘yan wasan kasar Eswatini. Kamaru za ta iya samun nasara da bambancin zura kwallaye idan ta doke Mauritus da Angola, ita kuma Cape Berde ta yi canjara a wasannin biyu, ko kuma idan Kamaru ta samu maki hudu a wasannin biyu,

 

ita kuma Cape Berde ta yi rashin nasara. Sai kuma Libya ce ta uku, kuma maki uku ne tsakaninta da Kamaru, kuma za ta iya bayar da mamaki.

 

Kasar Morocco ta riga ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniyar.

 

A cikin rukuni na E kuma kasashen Tanzania da Nijar da Zambia ne sauran kasashen da ke rukunin, kuma yanzu suna ta fafatawa ne domin samun gurbi na biyu wanda zai iya buga wasan raba-gardama.

 

A cikin rukuni na (F) kuwa, Ibory Coast na gaba da Gabon da maki daya bayan canjaras da ta yi da kasar Gabon a Francebille a watan Satumba. Kasar za ta je gidan Seychelles a ranar Juma’a, sai kuma ta fafata da Kenya a ranar Talata. Gabon za ta je gidan Gambia, sai kuma Burundi ta bakunce ta.

 

A cikin rukuni na G kuwa Algeria ita ma ta ba da tazarar maki hudu a saman teburi, kuma tana bukatar maki uku ne a wasanta da kasar Somalia wadda ta riga ta fita ko kuma ta biyu Uganda zai ta ba gurbi. Uganda ta zarce Mozambikue ne kawai da bambancin zura kwallo a matakin na biyu.

 

Can kuwa a cikin rukuni na H, Tunisia ta riga ta tsallake bayan samun gurbi duk da cewa akwai sauran wasaNNI biyu da za ta buga, inda ita kuma Namibia ta dage wajen neman zama ta biyu a rukunin. Namibia za ta je gidan Liberia a ranar Alhamis kafin ta karkare a birnin Tunis.

 

Daga rukuni na I kuma kasashe uku ne ke fafutikar samun gurbin na kai-tsaye, amma Ghana ce a sama da tazarar maki uku a saman Madagascar da Comoros. Ghana za ta samu gurbi idan ta yi nasara sannan Madagascar ta gaza samun maki uku. Wasan karshe na Ghana shi ne a gida da Comoros, ita kuma Madagacar za ta je gidan Mali a wasan na karshe.

 

Kamar yadda FIFA ta tsara, kasashe hudu da suka fi maki a cikin kasashen da suka kare a na biyu daga rukunoni tara din ne za su fafata wasannin raba-gardama a watan Nuwamba.

 

Zuwa yanzu dai kasashen Gabon da Madagascar da DR Congo da Burkina Faso ne a gaba a cikin tawagogi na biyu. Sakamakon za su iya canjawa bayan wasanni biyu na karshe, sannan kuma ba a riga an sanar da tsarin wasannin na raba-gardama ba.

 

Amma kasashen da suka samu nasara a wasannin na raba-gardama ne za su sake fafatawa a wasanin na raba-gardama da wasu kasashen na duniya kafin samun gurbi a gasar ta duniya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola October 12, 2025 Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
  • Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara
  • Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato