Wasu Shugabannin Turai Sun Yi Barazanar Ladabtar Da Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 20th, May 2025 GMT
Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta
Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar matakin hukunta Isra’ila.
Wannan bayani dai ya samu karbuwa daga fadar shugabancin hukumar cin kwarya-kwaryan gashin kan Falasdinawa da kungiyar Hamas, amma fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi. Wannan dai ya zo daidai da gargadin da kasashen duniya suka yi na fuskantar bala’in jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza sakamakon killace yankin da bullar masifar yunwa da ake ci gaba da yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Kan Tsibiran Kasarta
Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa.
Isma’il Baqa’i ya tabbatar a jiya Litinin 19 ga watan Mayu cewa: Tsibiran nan uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa wasu bangarori ne na kasar Iran, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin duk wani da’awar a wannan fanni ya sabawa ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma keta mutuncin yankunan kasa da ka’idojin kasa da kasa a matsayin makwabciyar kasa. Yana ganin gabatar da irin wannan batu a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa ba abu ne da za a amince da shi ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya shawarci kungiyar kasashen hadin kan Larabawa da ta yi la’akari da tabbatattun hujjoji na tarihi da na kasa a lokacin da suke tsara matsayinsu, maimakon yin zarge-zargen da ba su da tushe, da kuma kokarin kara fahimtar juna da alaka a tsakanin kasashen yankin.