2025-05-13@21:02:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«jam iyyun siyasa»:

    A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance. bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar. An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa ko kuma su fuskanci takunkumi. Gwamnatin rikon kwarya ta ayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan soke kundin tsarin mulkin jam’iyyun siyasa. Dole ne a samar da sabuwar doka musamman don tafiyar da harkokin siyasar Mali, inji karamin minsitan kula da sauye-sauyen al’amuran siyasa a gidan talabijin na kasar.
    Majalisar koli ta sojojin kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa da duk wasu kungiyoyi masu alaka da su. A ranar Larabar da ta gabata ne dai majalisar sojan kasar ta Mali ta fitar da dokar wacce shugabanta janar Assimi Goita ya rattaba wa hannu, wanda kuma aka sanar ta kafafen watsa labarun kasar. Sanarwar ta ce, an dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasar har illa masha Allahu. Dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasar bai shammaci ‘yan siyasar kasar ta Mali ba, bayan da a baya a taron kasa da aka yi, aka gabatarwa da gwamnatin sojan shawarar dakatar da jam’iyyun siyasar da kuma nada shugaban majalisar koli ta sojan kasar a matsayin shugaban rikon kwarya na tsawon shekaru...
    Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon wannan shekarar, don tunkarar zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 25 ga watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki. Kawancen CAP gamayyar jam’iyyun adawa da dama ne na kasar, in banda Jam’iyyar da Lauranta Bagbo a kafa don tunkarar zaben na watan Octoba. Har’ila yau kawancen na zargin hukumar zaben kasar da rashin adalci a yadda take amincewa da yan takara a...
    A yayin da jam’iyyun hamayya ke ci gaba da shirye-shirye tunkarar babban zaɓen shekara ta 2027, a bayabayan nan an ga yadda suke haɗuwa da juna, inda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa duniya cewa, suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen mai zuwa. Ko da yake yaƙi ɗan zamba ne, abi da har yanzu bai fito fili ba zuwa yanzu shi ne dabarar da ’yan adawar ke son yin amfani da ita wajen tunkarar APC a 2027, ganin yadda Jam’iyyar ke ta ƙara karɓar masu sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu. Guguwar APC ta girgiza ’yan adawa Wasu na ganin sauyin sheƙar na iya kawo babban...
    Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi.   Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya gano ra’ayinsa ko ya iya hasashen yanayin siyasarsa.   “Gwamna Buni bai tsaya kawai dan jam’iyyar APC ba; ko kawai gwamnan APC ba. Shi ne APC gaba dayanta, saboda sanannen abu ne cewa APC ta ratsa jijiyoyin jininsa.   “Sannan gudunmawar da ya bayar wajen gina APC a matsayinsa na Sakatarenta na kasa sau biyu, kuma ya rike ragamar Shugaban kwamitin tsara taron jam’iyyar; ya...
    Da alama tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana nema karbe kambun ɗaukaka da ’yan siyasa a baya suka riƙa bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar nan biyu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obansanjo, wajen neman tabarrakinsu musamman a lokacin da zabe ya karato a kasar nan. Buharin wanda ya mulki kasar nan a tafarkin soja da kuma na farin hula daga bayabayan nan, a yanzu haka tauraronsa na haskawa, kuma yana ƙamshin turaren Ɗan goma, inda jiga-jigan ’yan siyasa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da SDP da kuma jam’iyyarsa mai mulki ta APC, suke nikar gari takanas zuwa gidansa da ke birnin Kaduna, tare da nuna irin kyakkyawan kusancinsa da su. Hakan dai na zuwa ne...
    Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Congo Democradiyya da mayakn M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo nan gaba. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban yana kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta da misalign tsakiyar daren jiya Lahadi don a tattauna batun samar da zaman lafiya cikin Nutsuwa. Majiyar fadar shugaba Lourenco na cewa yakamata tsagaita wutan ya hada har da rashin kokarin mamayar karin iko a wasu wurare. Da kuma dakatar da fada. Da kashe fararen hula da sauransu. An shiya cewa gwamnatin kongo Democradiyya da kuma wakilan yan...
    Kudirin ya kuma nemi kafa wata hanyar warware takaddama don magance rikice-rikicen da suka shafi jam’iyyun siyasa, mambobinsu, ‘yan takara masu zaman kansu, da kuma kawance. Bugu da kari, ta tanadi hukunci kan keta haddi da bayar da shawarar gyara ga dokar zabe ta 2022 don cire rajistar jam’iyyun siyasa daga hukumar INEC. Bayan gabatar da shawarwari, an mika kudirin ga kwamitin majalisa mai kula da harkokin zabe da kwamitin jam’iyyun siyasa domin ci gaba da tattaunawa a kansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.” Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy? Kwanakin baya...
    Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.   “Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal   Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.”   A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya. Daga kanmu, magana...
    A yau Litinin ce aka sanya Sayyid Safiyyuddeen shugaban kungiyar Hizbullah wanda yayi shahada a hannun sojojin HKI a yakin Tufanul Aksa a makwanccinsa ta karshe a garinsu Deir-Qannoon Al-nahr dake kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dubban duruwan mutane ne suka halarci Jana’izar sa, sannan mutanen kauyuka a yankin da dama sun halarci jana’izar. Mutane daga kasashen duniya da dama wadanda suka halarci jana’izar a jiya Lahadi a Beirt sun  halarci jana’izar Sayyid shahid Hashim safiyyudeen a yau a kudancin kasar ta Lebanon.
    Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba.  Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba. Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye yankin. Na baya-bayan nan ita ce Hukumar Raya yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan bayan da ’yan yankin suka nace da yin ƙorafin cewa an mayar da su saniyar ware. NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan...
    A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari. Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP, jam’iyyun adawa sun yi yunkuri da dama amma ba su samu nasara ba. Na baya-bayan nan shi ne samar da wata sabon jam’iyyar siyasa mai suna ‘The Alternatibe’, domin tabbatar da madafun iko a babban zabe na 2027. Wani tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na kasa, Segun Sowunmi, wanda ke tallata wannan sabuwar jam’iyyar, ya ce an kafa jam’iyyar ne saboda ‘yan Nijeriya sun...
۱