Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027?
Published: 18th, May 2025 GMT
Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan.
Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar.
Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon FafaromaShin ko hakan zai kawo ƙarshen matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan faɗuwa zaɓen 2023?
Daga cikin matsalolin da suka kunno kai a cikin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP tun bayan faduwarta zaɓe a 2023 shi ne yin baram-baram a kan yadda za ta dinke barakar da aka samu a lokacin zaben fidda-gwani da rikicin shugabanci a matakai daban-daban da kuma kasa tsayawa da kafarta domin samar da adawa mai nagarta a siyasar kasar nan.
Sau tari dai an sha jin masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar na cewa, suna ƙoƙarin ɗinke ɓarakar tasu da kuma dawowa da ƙarfi, har ma a wasu lokutan sukan sha alwashin ƙwace mulki daga hannun Jam’iyyar APC.
A tsakanin ranar Lahadi da daddare zuwa wayewar garin Litinin da suka gabata ma an ga yadda masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar ta PDP ɗin suka yunƙura domin samar da mafita ga ɗimbin matsalolin nasu, inda har suka kafa kwamitin da zai jagoranci cim ma nasarar hakan.
Tuni dai masana harkokin siyasa, irin su Dakta Yakubu Haruna Ja’e na Jami’ar Jihar Kaduna suka fara sharhi a kan wannan batu.
Ya ce, gaskiya abu ne da ya kamata a ce sun yi shi tun a baya duk da kuma cewa akwai barazana mai ƙarfi da ke fuskantar su, kasancewa shi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ɗan Jam’iyyar APC ne ɗan siyasa kuma yana zagaye da ’yan siyasa da suke ƙoƙarin ganin sun janyo duk wani mutum daga cikin duk wata jam’iyya da take fama da rikicin cikin gida da domin ya bar ta, ya dawo cikin ita Jam’iyya mai mulki ta APC.
Dangane da hasashen da ake ta yi cewa, ’yan adawar ciki har da PDP suna neman kulla hadaka domin fuskantar zaben 2027 kuwa, Yakubu Ja’e na ganin cewa har yanzu ba a makara ba.
Ya ce, ‘‘shugaban da yake kai gaskiya yana da ƙarfi duk da ana ganin kamar ba a son sa, amma yana da abin da zai sa a so shi saboda yana da kuɗi mutane kuma ba a raba su da kuɗi idan siyasa ta taso.
To amma idan da waɗannan jam’iyyu za su iya haɗa kai ƙwarai da gaske, za su iya kaiwa ga nasara tun da aƙalla idan ka lura masoya APC sun yi rauni a wasu manyan jihohi kusan biyar, domin ka ga sam ba ta ci zaɓe a Jihar Legas ba, kuma sun samu rauni, kuma har yanzu suna da wannan raunin, ga Jihar Ribas abin da suka yi na cire zaɓaɓɓen gwamna suna sa nasu wannan zai iya sa su rasa jihar, ga Kano shi ma haka ne ga ma Kaduna haka ne.
“To idan ka dubi wadannan manyan jihohi lallai da Jam’iyyar PDP za ta haɗa kai da wasu jam’iyyu zai iya ba ta dama ta ci zabe in an cire kwadayi’’.
Me ya janyo jinkiri wajen ɗinke ɓarakar PDP ɗin?
Sanata Umar Tsauri, mamba ne a kwamitin amintattu na jam’iyyar cewa ya yi, Jam’iyyar PDP ta yi amanna cewa ko yanzu aka shiga zabe tana da hajar tallata wa al’ummar kasar nan.
“Ba za ka iya gane mutum fari ba ne sai akwai baƙi a tare da shi; ba za ka iya gane mutum gajere ba ne sai akwai dogo a tare da shi.
“Idan mutane suka kwatanta yadda mulkin Jam’iyyar APC na shekara biyu ya kasance da kuma mulkin PDP na shekara 16 sai su yanke wa kansu hukunci,’’ in ji shi.
Masu sharhi dai na ganin cewa, duk wadannan dabaru da salon tade kafafun juna da ke gudana a tsakanin jam’iyyun siyasar ba su wuce fafutukar neman mulki a 2027 ba, wanda kuma lokaci ne kawai zai iya tabbatar da bangaren da ya fi iya allonsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɓaraka zaɓen 2023 Zaɓen 2027 a Jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin Sin kadai ba, har da nuna yanayin sauyawar abubuwan dake haifar da ci gaba a duniya. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ta kafar intanet, ya nuna yadda masu bayar da amsa daga fadin duniya suka yi imanin cewa, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba ta kowace fuska ba tare da tangarda ba, lamarin da ya samar da tabbaci ga tattalin arzikin duniya.
Karfin tattalin arzikin Sin ya dagora ne da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi da ke samun ci gaba cikin sauri, wadda ake ganin saurin ci gabanta ta hanyar kirkire-kirkire. Nazarin ya nuna cewa, kaso 93.6 na wadanda suka bayar da amsa, sun yi imanin cewa, kirkire-kirkire na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki mai inganci na Sin. Wasu kaso 96.6 kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin na jagorantar manyan sauye-sauye a tsare-tsaren tafiyar da masana’antu da na tattalin arziki ta hanyar kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.
A matsayinta na kasa ta biyu mafi yawan masu sayayya, kasar Sin ce ke da mutane masu matsakaicin kudin shiga mafi yawa a duniya, inda take da gagarumin karfin sayayya da na zuba jari. Nazarin ya nuna cewa, kaso 82.3 na masu bayar da amsu sun yi imanin cewa, kamfanonin kasashen waje za su iya amfani da fa’idojin da suke da shi wajen shiga kasuwar kasar Sin domin kara samun karfin takara a duniya. (FMM)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA