2025-08-16@10:43:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7893
«sabon Fafaroma»:
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna. A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci. A wata sanarwa da kakaki rundunar,...
A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin kwanciyar hankali Ƙananan hukumomin Batsari, Jibiya da Ɗanmusa na daga cikin wuraren da aka samu wannan ci gaba. Wasu manoma da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana farin cikinsu da yadda rayuwa ke dawowa dai-dai. Malam Rabe, manomi daga Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Jibiya, ya ce: “Mu kam yanzu sai mu ce Alhamdulillahi. Lallai sulhu alheri ne a tsakanin al’umma. Ni rabon da na...
An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani. Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin taron ya yi kyau. Putin ya jaddada aniyar kasashen biyu na kawo karshen kiyayyar da suke yi da kuma bukatar cimma matsaya domin kawo karshen yakin Ukraine. Ya yaba da yadda Trump ya fahimci muradun Rasha da kuma burinsa na fahimtar ainihin rikicin. A nasa bangaren, Trump ya tabbatar da cewa tattaunawar ta kai ga cimma matsaya a kan batutuwa da dama, yayin da wasu...
Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli. “Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu...
Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar da “duk wata dama ta yin sulhu.” Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyyay a bayar da rahoton cewa, al-Burhan ya ce sojojin za su ci gaba da yaki ko ta halin kaka, kuma ba za su ci amanar sadaukarwar wadanda aka kashe a rikicin ba. Al-Burhan ya yaba da irin tsayin dakan da sojojin suka yi a manyan garuruwa irinsu El Fasher, Babanusa, da Kadugli, yana mai cewa suna ci gaba da kare kasar ta kowace fuska. Majiyar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Al-Burhan ya gabatar da wani fayil na tsaro da ke...
Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi. Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana hakan ta gidan talabijin na kasar a yammacin jiya Alhamis, inda ya ce an shawo kan lamarin gaba daya, kuma an fara gudanar da bincike. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula na siyasa, kuma ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ‘yan kwanakin nan kan tsare jami’an soji. Hukumomi sun bayyana dan kasar Faransa...
Wata kotun tarayya a kasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar. A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba. “A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike gurbin jagoranci bayan tafiyar Cif Nwosu ita ce, ta hanyar taron kwamitin zartarwa na kasa.” Tsaagin jam’iyyar ta sake tabbatar da cewa Alhaji Nafiu shi ne halastaccen shugabanta na kasa tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da hadin kai. Ya kuma bayyana kwarin giwa kan ikon hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na kiyaye...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Gwiwa. Yace a lokacin irin wannan ziyarar, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi domin tabbatar da gudanar harkokin kananan hukumomi kamar yadda ya kamata, ta hanyar aiki da tanade-tanade da kuma ka’idojin kashe kudade. Alhaji Aminu Zakari ya kuma lura cewar Kwamatin yana kafa kananan kwamitoci domin ziyarar gani...

Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun. “Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa. Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin domin jajantawa iyayensa da ‘yan uwansa . “kwamishinan ya Kara da cewa ‘Mai girma gwamna Uba Sani Yaso yazo da kansa amma bisa wasu abubuwa da suka bijiro hakan ya sanya ya wakilto mu saboda haka gwamna ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Abubakar”. Maiyaki, yace domin ganin an dakile matsalar yawaitar tu’ammali da muyagun kwayoyi, gwamnatin jihar Kaduna ta Kafa wani...
Al’ummar unguwar Sharada da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun ƙirƙiro dokoki 29 domin gyara halayyar jama’a da kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu. Daga cikin dokokin akwai hana saurayi da budurwa yin zancen dare, musamman a cikin mota, da kuma hana su wuce ƙarfe 10 na dare suna hira a waje. Ba mu da tabbas na ci gaba da rijistar kaɗa ƙuri’a a Borno — INEC Mutum 12 sun rasu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a Kano Mahukuntan yankin sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda damuwa kan lalacewar tarbiyya, ƙaruwa matsalolin tsaro, da kuma rashin bin al’adun da suka dace musamman a tsakanin matasa. Wannan ba shi ne karon farko da aka taɓa kafa irin...
Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye. 2. Kula da walwalar sojoji da karfafa musu gwiwa Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta...
A jiya Alhamis ne aka kaddamar da gasar wasanni ta mutum mutumin inji ta duniya a birnin Beijing na kasar Sin, wadda ke gabatar da sabbin ci gaban da aka samu a bangaren aiki da basira da motsi, wajen kera mutum mutumin inji. Kungiyoyi 280 daga kasashe 16, ciki har da Amurka, da Jamus, da Italia ne za su fafata a gasar da za a yi daga Juma’a zuwa Lahadi, a dakin wasan gudun kankara na kasa. Mutum mutumin injin za su fafata ne cikin wasanni 26 na motsa jiki, kamar gudu, da dogon tsalle, da sarrafa jiki, da kwallon kafa, da ma wasu ayyukan da suka shafi basira a fannoni daban-daban kamar jigilar kayayyaki, da ware magunguna, da aikin...
Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu. Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani. “Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance. “’Yan kasuwa da ke habaka...
Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara bukatun al’umma, da tabbatar da dorewar samar da aikin yi da daidaiton farashin kaya, da kuma raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, inda aka cimma sabbin nasarori kan neman ci gaba mai inganci. A fannin masana’antu kuma, yawan kayayyakin da aka samar ya karu da sauri, kana, aikin kera na’urori da aikin samar da kayayyaki da fasahohin zamani suna bunkasuwa kamar...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sheikh Na’im Kasim ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata ajiye makamanta kamar yadda gwamnatin kasar Lebanon take son tayi kafin karshen wannan shekarar. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto sheikh Qasim yana fadar haka a jiya Alhamis da yamma, a lokacinda yake jawabi don raya ranar 40 na Imam Hussain (a). Malamin yayi kira ga sauran kungiyoyin kasar Lebanon su kasance tare da ita don kare kasar Lebanon. A wani wuri a jawabinsa shugaban Hizbullah ya bayyana cewa ba zasu amince da ajiye makamansu a dai-dai lokacinda HKI tana kaiwa kasar hare-hare tana kuma tana mamaye da kasar. Yace shawarar da 5 ga watan Augusta saida kasar Lebanon ga HKI...
Gwamnatin kasar China ta bayyana cewa ba zata taba amincewa a sake dorawa JMI takunkuman tattatalin arziki wadanda MDD ta dauke mata su a watan octoban da ya gabata ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Lin yana fadar haka ya kuma kara da cewa kasashen turai guda uku faransa Burtaniya da kuma Jamus wadanda ake kiransu E3 suna son ya yi amfani da wani tsarin da ake kiran SnapBack da ya zo cikin yarjeniyar JCPOA ta shekara 2015 don sake maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa JMI kafin yarjeniyar JCPOA dangane da shirinta na makamashin nukliya. Lin ya kara da cewa a ganinta ba za’a taba warware...
An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar HKI da yaren Hebru mai suna Yedioth Ahronoth yana fadar cewa an gano gawar sojan dan shekara 28 wanda ba’a bayyana sunansa ba a dajin dajin sweezland kusa da yankin tiberias a yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, idan ya tabbata sojan ya kashe kansa ne to kuwa shi ne 17 da suka kashe kansu tun bayan fara yaki a gaza a shekara ta 2023. Ahronoth ya cewa sojan ya yi aiki da runduna ta 99 a gaza a cikin yan makonnin da suka gabata. Sannan a halin yanzu...
Bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya karawa kayakin da suke shiga Amurka daga kasar Indiya kudaden fito har na kasha 50% Narendra Mudi ya ki sauraran kiraya-kiraye na kada yayi m haka. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ya ce, kiraye-kirayen kasar Indiya ta hana wasu kayakin Amurka shiga kasar yana kara karfi a cikin mutane. Firai ministan ya bayyana cewa, a halin yanzu kamfai yayi nisa a cikin mutanen kasar na kauracewa kayakin Amurka wadanda suke shiga kasar kamar McDonald’s, Coca-Cola, Amazon, da Apple da sauransu, sannan mutane su koma wajen bunkasa na gida. Labarin yace kamfanoni masu girma na Amurka suna samun kasuwa mai yawa a kasar india wacce take da jama’a fiye...
Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta Ƙasa a Jihar Borno ta bayyana cewa, babu tabbas na gudanar da aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a na shekarar 2025/2026 a wasu Ƙananan hukumomin Jihar huɗu don matsalar tsaro. Ƙananan hukumonin sun haɗa da: Ƙaramar Hukumar Abadam da Guzamala da Marte da Kala-Balge Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan zaɓe na Jihar Borno, Abubakar Ahmad Ma’aji a jawabinsa ga manema labarai a Maiduguri, a wani ɓangare na shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistar masu kaɗa kuri’a a ranar Litinin da ke tafe. Kamar yadda Kwamishinan Hukumar zaɓen ke bayyanawa, INEC ta mayar da rijistar...
Mutum 12 sun rasu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Samawa, da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano. Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:40 na daren ranar Juma’a a kan titin Zariya zuw Kano. Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tirela ƙirar DAF mai lambar KMC 931 ZE, wadda ke ɗauke da kaya da fasinjoji ta yi hatsarin. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta ce bincike ya nuna cewar matsala ce ta haddasa hatsarin. Tirelar na ɗauke da mutum 19, wanda 12 daga cikinsu suka rasu, sai wasu biyar da suka...
A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya. A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa. Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa....
Ita ma da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai bukatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa. Hakazalika Maryam ta jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya babu yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani. “Ba maganar talauci idan zaman lafiya da adalci sun tabbata.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin. Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar daren Alhamis ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje da dama, inda wasu gine-gine suka ruguje ƙarƙashin ruwan. An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil Sakamakon ambaliyar ruwan ya sa mazauna wasu unguwanni da dama suka rasa matsugunansu inda suke hijira ya zuwa gidajen ‘yan uwa da makarantu, inda suke kokawa kan yadda iftala’in ta afku....
“Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar raya kasashe ta KOICA, Garba ta ce wannan hadin gwiwa ya taimaka wa kasar wajen sake tunanin koyo, tare da dakile rarrabuwar kawuna, da bai wa makarantu da malamai kwarin gwiwa domin samar da sauyi mai dorewa. Mataimakin Babban Sakatare na UBEC (Technical), Mista Razak Akinyemi Olajuwon, ya bayyana cewa, wannan shiri ya kara wa malamai kwarin gwiwar yin amfani da su da bunkasa abubuwan...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita ce ranar 20...

Firaministan Sin Ya Bukaci A Zage Damtse Wajen Bude Sabon Babin Gina Wayewar Kai Ta Fuskar Kare Muhallin Halittu A Sabon Zamani
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaro sun kuɓutar da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Itobe – zuwa Ochadamu – Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu a Jihar Kogi. Fasinjojin da aka kuɓutar an yi garkuwa da su ne a ranar 11 ga watan Agusta a ƙauyen Ugbakpedo da ke kan titin, lokacin da wata mota ta yi wa fasinjojin kwanton ɓauna. Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Jami’an tsaron da suka haɗa da: ’yan sanda da ’yan banga da mafarautan yankin sun bayyana cewa sun afkawa dajin da ke yankin kafin ceto matafiyan. “A ranar 13 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 4:30 na Asubahi ne...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita ce ranar 20...
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan 1.6, wanda ya haura daga kaso 3 na harajin ilimi da aka dora wa ribar kamfanonin da ke kasuwanci a Nijeriya kamar yadda dokar TETFund ta tanada. Masari ya bayyana cewa, daga cikin Naira Tiriliyan 1.65, an fitar da Naira biliyan 225 zuwa asusun bayar da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND), domin shirin rancen daliban gwamnatin tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC Manyan jami’an gwamnati da suka raka shi, sun haɗa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu. Sauran sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; da Ministan Kuɗi, Wale Edun. A Japan, Shugaba Tinubu zai halarci Taron Ci Gaban Afirka karo na tara (TICAD9)...
Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da hakan ne daga shugabar ƙungiyar, Rasheedat Ajibade, da kuma hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa (NFF). Olopade ya ce ba daidai ne a yi iƙirarin cewa ba a biya kuɗin ba, inda ya ƙara da cewa bai kamata a jefa Ajibade cikin matsalar musanta kalaman da ba ta faɗa ba. Ya bayyana cewa waɗanda ke da matsalar asusun banki su kaɗai ba su samu ba, amma...
Kamfanin jirgin sama na British Airways ya hana fasinjoji 58 hawa jirginsa da zai tashi daga Abuja zuwa Landan saboda matsala da ƙofar jirgin ta samu. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce kamfanin jirgin ya bar wasu kujeru babu kowa saboda dalilan tsaro. Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda Daraktan Yaɗa Labarai da Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya wallafa a shafinsa na X cewa matsala ce ta sa aka hana fasinjojin hawa jirgin. Ya ce an bai wa fasinjoji 30 wajen kwana a wani otel, yayin...
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce matsalar tsaro na iya hana ta gudanar da aikin rijistar masu zabe a kananan hukumomin jihar Borno guda hudu. Kananan hukumomin da lamarin zai iya shafa su ne Abadam, Guzamala, Marte da Kala-Balge. Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan Zabe na jihar, Abubakar Ahmad Ma’aji a jawabin sa ga manema labarai a Maiduguri, a wani vangare na shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistar masu kada kuri’a a ranar Litinin da ke tafe. A cewar shi, INEC ta mayar da rijistar masu zaben a...
A farkon wannan shekarar da ta gabata, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, a wani taro ya bai wa kungiyoyin na Sufurin Jiragen Sama tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bi ka’ida wajen sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman kasa. Keyamo ya kuma bai wa shugabannin kungiyoyin tabacin cewa, suma a sanya kan batun na yarjejeniyar ta sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman. Kazalika, ba su tabbacin cewa, zai umarci hadiminsa domin ya ci gaba da sanar da shugabannin kungiyoyin kan abinda ke tafiya game da yarjejeniyar. Sai dai, a jawabin da shuwagabbin kungiyar da kuma na ma’aikatan suka gabatar a wani babban taronsu a shalakwar Tashar Jiragen Sama da ke...
Sojojin Nijeriya a Lokoja, tare da haɗin gwuiwar sauran hukumomin tsaro, sun kuɓutar da mutane shida da aka yi garkuwa da su a yankin Obajana na Jihar Kogi. Cikin waɗanda aka ceto akwai Sarkin Fulani na Asinwe a ƙaramar hukumar Okehi, wanda aka sace a gidansa, tare da wasu mutum huɗu da aka sace a ranar 12 ga Agusta, da kuma mutum biyu da aka sace a ranar 28 ga Yuli a Apata, Lokoja. Kwamandan bataliya ta 12, kuma Kwamandan Operation Accord III, Birgediya Janar Kasim Sidi, wanda Commanding Officer na bataliya ta 126, Laftanar Kanal Francis Nwoffiah ya wakilta, ya ce an samu nasarar kuɓutar da fursunonin ne bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri, inda dakarun suka bi sawun...

Babban Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Iran Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi kan duk wani wuce gona da iri kanta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ita ce babban jari kuma wata dabara mai kima ga yankin, yana mai jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da aka kai mata, kuma babu wata tattaunawa da za ta yi tasiri a karkashin tunanin Amurka na “zaman lafiya da nuna karfi.” Ali Larijani ya jaddada a shirye Iran take a koda yaushe ta mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai kan...

Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama Ta Human Rights Watch Ta Ce; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin na Iran laifi ne na yaki Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin da ke birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar 23 ga watan Yuni yana matsayin laifin yaki. A cikin wani rahoto da ta buga jiya alhamis, kungiyar ta yi bayanin cewa hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gine-gine da dama a cikin rukunin, sun kuma kashe mutane akalla 80, a cewar sanarwar da Iran din ta fitar, da suka hada da fursunoni da ‘yan uwansu, da...

Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza Tare Da Rusa Gidajen Mutane A Khan Yunis
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai wani mummunan farmakin kan birnin Gaza tare da janyo ruftawar gidaje a Khan Yunis Falasdinawa da dama sun yi shahada tare da jikkata a yau Juma’a a wani kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza a rana ta hudu a jere, yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila take ci gaba da mamaye birnin. A halin da ake ciki kuma an ci gaba da rusa gidaje a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza. Majiyar Asibitin Al-Shifa ta sanar da cewa: Falasdinawa biyu sun yi shahada yayin da wasu suka jikkata a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai unguwar Al-Rimal da ke yammacin birnin Gaza. Wakilin gidan talabijin na Aljazeera ya bayar da...
An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da suka kashe kansu tun farkon wannan shekara zuwa 18, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka bayyana. Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: Rundunar sojin ta bude bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa jami’in da ya kashe kansa yana shiyya ta 99 da ke yaki a zirin Gaza. Jaridar Yedioth Ahronoth ya watsa rahoton cewa: Jami’in dan shekaru 28 ya...
Gwamnatin Mali ta sanar da dakile wani shiri na hargitsa kasar tare da goyon bayan wata kasar waje Gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali ta sanar da cewa: Jami’an tsaro da na leken asiri sun dakile wani yunkuri na tada zaune tsaye a kasar, wanda sojoji da fararen hula da ke samun goyon bayan wata kasar ke shirin shiryawa. Sanarwar da gwamnatin Mali ta fitar ta hannun ministan tsaron kasar ta Mali ta bayyana cewa: Wadanda ke da hannu a harin sun hada da jami’an soji biyu Abbas Dembele da Namma Sangare da wani dan kasar Faransa da ke aiki da hukumar leken asirin kasarsa. Mahukuntan kasar Mali sun bayyana cewa: Halin da ake ciki a kasar na cikin halin kaka-ni-kayi,...
Ya ce: “A Inugu, mun sami damar cika duk abin da muka yi wa mutanen mu alƙawari a lokacin kamfen, godiya ga jarumtar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, wadda ta samar mana da albarkatun da ake buƙata don aiwatar da manyan ayyuka.” Ya kuma bayyana ayyukan da ake yi a halin yanzu a jihar, waɗanda suka haɗa da gina ajujuwa 7,000, samar gadajen asibiti 3,300, da samar da gonakin gwamnati hekta 2,000 a cikin gundumomi 260 na jihar. Gwamna Mbah ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa manufofin Gwamnatin Tarayya baya, yana mai cewa suna da amfani ga al’ummar jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Amana a cikin sanarwar da Hukumar ta NPA ta fitar mai taken daukar matakai ga masu amfani da Tashoshin Jiragen Ruwan kasar biyo bayan bullar annobar Korona wadda kuma Janar Manaja na sashen Kula da walwalar jama’a da dabarun samar da bayanai na Hukumar ta NPA Jatto Adams ya fitar ta umarci daukacin masu Kula da harkokin Hukumar da su dakatar da cazar duk wasu kudaden na shigo da kayan zuwa cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar har zuwa wasu Kwanuka 14. Wannan umarnin ya biyo bayan umarnin da tsohuwar gwamatin marigayi Shugaban kasa Muhammad Buhari ta yi ne bayan bullar annobar Korona a na fadadar da aka yi ne, bayan bullar annobar Korona a ranar 12 ga watan Afirilun shekarar...
Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce galibin jama’a ba sa yaba wa kokarin jami’ansu na hana aikata laifi a cikin al’umma, duk da yana daya daga cikin manyan ayyukansu. Kayode, wanda Mataimakin Babban Sufeto mai kula da sashen sayo kayayyaki na rundunar, A.A. Hamza ya wakilta, ya fadi hakan ne a Abuja ranar Alhamis, yayin taron kaddamar da wani littafi mai suna “Fraud unmasked”, wanda Dr Preal Ogbulu ya wallafa. Kotun kasar Kanada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya A cewarsa, “Duk laifin da aka dakile aikatawa, dole akwai namijin kokarin da aka yi a kan hakan. Kundin tsarin mulki da...
Bugu da kari kuma, gudummawar da Nijeriya ke bayarwa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya ba za su misalta tu ba, wanda hakan ke jaddada aniyarta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Manufofinta na kasashen waje a al’adance suna nufin ingantawa da kuma kare muradun Nijeriya tare da tallafa wa hadin kan Afirka. Gabatar da ajandar “4D”, a sakamakon haka, yana wakiltar sauyin da aka samu a lokacin da ya dace, wanda hakan zai bude damar karfafa hadin gwiwar da kasashen duniya, tabbatar da zaman lafiya na duniya, da kuma bunkasa matsayin Nijeriya a idon duniya. Sai dai, nasarar wadannan manufofin ya ta’allaka ne a kan aiwatarwar su mai inganci. Ya kamata a lura da...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauyen jagoranci a Hukumar Talabijin ta ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro a matsayin sabon Darakta-Janar. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Karimah Bello a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Tallace-Tallace, Stella Din a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Labarai, da Sophia Essahmed a matsayin Manajing Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited. Pedro, ɗan asalin jihar Lagos, ƙwararren mai ba da shawara ne a harkar kafofin watsa labarai, mai gogewa sama da shekaru 30 a fannoni da suka haɗa da talabijin, haƙƙoƙin watsa wasanni, da dabarun tallace-tallace a Afrika, da Birtaniya da Gabas ta Tsakiya. Kwararre ne a fannin nishaɗi da mallakar fasaha, tare da digirin na biyu a Gudanar da Zuba...
Akwai wasu tsaffin ‘yan siyasa daga yankin Arewacin Najeriya,wadanda ke ci da gumin ‘yan Arewa. Wadannan tsaffin ‘yan siyasa, yanzu alkadarinsu ya riga ya karye, ba su da wani abu da ya rage illa su rungumi siyasar kabilanci da bangaranci. Ba tsaffin ‘yan siyasa kawai ba ne. Gungu-gungu ne. Wasun su, tsaffin ‘yan boko ne. Wasu ‘yan Kasuwa. Wasu ma ba wata sana’a ko wani aiki da suka taba yi a rayuwarsu da ya wuce ci da gumin Arewa . Wani abu da ya hade su shi ne, mafi yawansu sun samu damar da za su taimaki Arewa ko mutanen Arewa, amma suka ki. Misali, a cikin irin wadannan mutane, babu maras sa kunya,irin wadanda suka rike mukamai a gwamnatin...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya ta yaba wa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa nada Alhaji Muhammad K. Dagaceri a matsayin shugaban ma’aikata na jiha. Shugaban ƙungiyar na kasa, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa TUC, Kwamared Shehu Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga shugaban ma’aikata, Alhaji Muhammad Dagaceri, a ofishinsa. Ya tabbatar wa shugaban ma’aikatan da cikakken goyon baya da haɗin kan ƙungiyar wajen cimma manufofin da aka tsara a matsayinsa na shugaban ma’aikatan jiharta Jigawa. “Kungiyarna sa ran yin haɗin gwiwa da zai ƙara inganta aikin ma’aikata da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.” In ji shugaban ƙungiyar. A jawabinsa, Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana godiyarsa bisa wannan...
Ministan Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara. Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar a Ilori babban birnin Jihar Kwara. Da yake wakiltar Ministan, Richard Mbaram ya bayyana wannan shiri a matsayin babbar nasara a tarihi wajen samo mafita ta dindindin ga rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan. Ya ce aikin na daga cikin tsare-tsaren Shirin Sauya Hanyar Kiwo na Kasa (National Livestock Transformation Plan) na tsawon shekaru goma (2019-2028) wanda ya mayar da hankali kan gyara harkar kiwo a Najeriya....
Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma. Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, baya ga noma, kiwon dabbobi shi ne babban abin da mutanen jihar Jigawa suka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kara da cewa kafa wannan ma’aikata na cikin shirin gwamnati na bude manyan damarmaki da ke cikin wannan bangare. “Mun dauki mataki na musamman domin ingantawa da bunkasa bangaren kiwon dabbobi. Mun yi hadin gwiwa da...

Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa
A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa. Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce ta yi wannan gargadin a madadin gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa dole ne a dauki matakan da suka dace a cikin al’ummomin da abin ya shafa. Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta ce, biyo bayan hasashen da ta yi na samun ruwan sama mai karfi a jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa tsakanin 10 ga Agusta zuwa 14...
Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar. A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita...
Daga cikin wadannan alkaluman na yara miliyan 1.65 sun kasance suna a jihohin Zamfara, Bauchi, Sokoto, Borno, Kebbi, Kano, da kuma wadanda kuma suke a jihohin da Kungiyar ta MSF ke gudanar da ayyukanta kuma jihohin da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro. Bugu da kari, akasarin kungiyoyi, sun yi ittifakin cewa, batun kula da lafiya, abu ne, da ya kamata matan Gwamatin uku na kasar, su bayyana dokar ta baci a kai. Wannan rashin ayyana dokar ta bacin a fannin, mussaman a Arewacun Nijeriya, za a iya cewa, babbar gazawar rashin iya gudanar da shugabanci na gari ne, inda a Katsina irin wannan sakacin, mussaman na gazar samar wa yaran abinci mai gina jiki, ya bayyana karar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da aka kai kasar Japan. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto wasu bayanai daga cikin sanarwar da masu rajin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan bikin cika shekaru 80 da hare-haren nukiliyar da Amurka ta kai a garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan. Hare-haren nukiliya na Amurka, wanda ya kashe mutane 150,000 a Hiroshima da 80,000 a Nagasaki, ba...

Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen Ya Ce; Yahudawan Sahayoniyya Suna Yakar Al’ummar Falasdinu Duka Ne
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun aikata kowane irin laifi da kowane nau’i na wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza. A jawabin da ya gabatar kai tsaye kan sabbin ci gaban da ake samu a hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma ci gaban yanki da na duniya, Sayyed al-Houthi ya yi nuni da cewa, yawan hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai cikin...
Kungiyoyin kasa da kasa guda 100 sun koka kan yadda gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi watsi da bukatu har 60 kan ba da damar shigar da agaji zuwa Gaza Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 100 ne suka bayyana a wata wasika ta hadin gwiwa da aka buga jiya alhamis cewa, ana kara amfani da sabbin dokokin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta tsara kan ayyukan kungiyoyin agaji na kasashen waje wajen kin amincewa da bukatarsu ta shigar da kayayyaki zuwa zirin Gaza. Wasikar ta ce: “Hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila sun yi watsi da bukatar da kungiyoyi masu zaman kansu da dama suka gabatar na kawo kayayyakin ceton rai, lamarin da ya bar miliyoyin daloli na agajin jin kai da suka...
Laifukan da ake gudanarwa a gabar tekun Siriya: Cin zarafin ya kai ga laifukan yaki! Rahotonni sun bayyana cewa; Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Siriya ya fitar ya ce: Rikicin kabilanci da ya faru a gabar tekun Siriya ya kunshi cin zarafi da ya kai ga laifukan yaki. Rahoton ya kara da cewa; Rikicin addini ya shafi mabiya darikar Alawiyya ne, inda aka kashe fiye da mutane 1,400 Alawiyyawa a rikicin addini da suka hada da daukacin iyalai da mata da yara da kuma tsofaffi a gabar tekun Siriya. Bugu da kari, an samu rahotannin kone-kone, sace-sace da kuma wulakanta gawarwakin da wasu ‘yan bindiga suka aikata. Rahoton ya bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Siriya da ta fadada kokarin...
Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Mutane 40 ne suka mutu a Sudan sakamakon barkewar cutar kwalara mafi muni cikin shekaru Kungiyar likitocin ba da agaji ta “Doctors Without Borders” ta sanar da mutuwar mutane 40 sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Sudan cikin mako guda kacal, tare da tabbatar da cewa a halin yanzu kasar na fama da barkewar cutar mafi muni cikin shekaru da dama, sakamakon yakin da ake yi. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar ta bayyana cewa, kungiyarta ta yi jinyar mutane fiye da 2,300 masu fama da cutar kwalara a yankin Darfur kadai a cibiyoyin da ma’aikatar lafiya ta kasar ke kula da su, inda ta yi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alkaluman sun nuna cewa, cikin wa’adin, yawan sakwannin da aka yi jigilarsu a cikin birni daya sun kai biliyan 9.26, adadin da ya karu da kaso 6.5 bisa dari a mizanin shekara, yayin da wadanda aka yi jigilarsu daga birni guda zuwa wani na daban, suka kai biliyan 100.43, karuwar da ta kai ta kaso 19.9 bisa dari cikin wa’adin na watanni bakwai. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ahmed Maiyaki da Sadiq Mamman Legas a madadin gwamnatin jihar Kaduna sun ce ofishin babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a zai yi nazari kan kalaman da kungiyar hadaka ta ADC ta yi tare da baiwa gwamnatin jihar shawara kan mataki na gaba. Tun da farko a wani taron manema labarai, jam’iyyar African Democratic Congress da hadin gwiwarta sun zargi gwamnatin jihar Kaduna da daukar hayar ‘yan baranda sama da 4000 tare da cire naira miliyan 30 daga asusun kowace karamar hukuma domin kawo cikas ga zaben da ke tafe.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut. A cewarsu, sun aika da koke...
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025. An zabi sabuwar firaminista a Luthuania Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC A cewar Gwamna Radda, hutun zai ba shi damar samun kulawar likitoci da kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin koshin lafiya. “Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi. “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.” ...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi. “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.” ...
Shugaban ƙasar Lithuania, Gitanas Nauseda, ya zabi ’yar majalisa Inga Ruginiene ta jam’iyyar Social Democrat, a matsayin firaminista, bayan Gintautas Paluckas ya yi murabus sakamakon binciken rashawa da ake gudanarwa a kansa. Sai dai Ruginiene ta taba fuskantar suka kasancewar tana da alaka da ’yan uwa a Rasha, wadanda ta ziyarta a shekarun 2015 da 2018. Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi Sai dai ta ce yanzu daina kai musu ziyara, kuma ta jaddada cewa tun farko Ukraine take mara wa baya a yakin da take yi da Rasha, wadda ta kaiwa mamaya a 2022. Majalisar dokokin ƙasar za ta amince da nadinta tare da ministocinta kafin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da kammala duk shirye-shiryen zaben ciki gurbi a kananan hukumomin Bagwai, Shanono da kuma Ghari (Kunchi) da ke Kano wanda za a gudanar a ranar Asabar. Kwamishinan INEC a Kano, Zango Abdu, wanda ya tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai, ya ce an riga an raba kayan zabe masu muhimmanci da wadanda ba su da muhimmanci a kananan hukumomi da abin ya shafa. Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi An kama Mai Unguwa kan yi wa yarinya fyaɗe a Gombe Ya ce, “Tun kusan makonni uku da suka gabata aka riga da tura kayayyakin da ba su da muhimmanci wadanda aka tanadar wa mazabu da rumfunan zabe....
Bugu da kari, idan an lura da yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki, yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin a shekarar 2024 ya kai kusan 42000, wanda ya karu da kusan kashi 9 bisa dari a shekarar 2023. A farkon rabin wannan shekara, masana’antar lantarki ta kasar ta ci gaba da kiyaye ingantaccen yanayin ci gaba. Kudaden shiga da manyan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki suka samu ya kai yuan triliyan 8.04, wadanda suka karu da kashi 9.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
“Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.” Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na daga cikin shirin gidauniyar na bunƙasa tattalin arziki, da kuma kyautata ci gaban al’umma. “Wannan shi ne karo na huɗu da wannan gidauniyar ta ke rabon taki duk shekara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya sayen takin a irin wannan lokacin da gona ke buƙata ba.” “An ware buhun taki guda 6,000 da za a rabar wa manoma masu...
Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin ƙasar nan da yake ci gaba da yi. Okonjo-Iweala ta shaida wa manema labarai hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja. Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu har lahira a Bayelsa Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar “Shugaban ƙasa [Tinubu] da muƙarrabansa sun yi ƙoƙari sosai wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya. “Wannan namijin ƙoƙarin na Tinubu abu ne da ya zama dole a yaba masa da ba kowa zai iya yi ba. Tsohuwar Ministar Kuɗin ta Nijeriyar ta ƙara da cewa, yanzu aikin da ke gaban...
Miliyoyin musulmi daga ko ina sun taru a hubbaren Imam Hussain (a) da ke birnin Karbaka na kudancin kasar Iraki, don girmama limami na 3 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wanda ya zama a bin buga misali a duk tsawon tarihin musulunci na nuna turjiya da kuma fada da azzalumai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Iran ta bayyana cewa miliyoyin musul daga cikin kasar Iraki da kuma wajensa ne suke tattaki da kafa daga ko ko ta ina a cikin kasar zuwa hubbaren Imam Hussain (a). Sannan a kan hanyarsu ta zuwa Karbala akwai dubban mutane masu sa kai, suna raba ruwa da abinci da samarda wuraren hutawa da kuma magani ga wadanda suke bukata....
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyeed Abdulmalik Badruddeen Huthi , a jawabinsa na mako-mako da ya saba gabatarwa, dangane da Falasdinu da kuma sabbin al-amura da suka faru ko suke faruwa a yankin da kuma duniya gaba daya ya tabo al-amura da dama. Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta da harshen larabci a nan Tehran ta bayyana cewa, shugaban Ansarullah, ya yi gargadi kan cewa, ida HKI tana son dabbaka shirinta na Isra’ila babba, a cikin wannan halin da kasashen larabawa suke rarrabe, hakan zai zama musiba babba. Labarin ya kara da cewa sojojin kasar Yemen sun aiwatar da ayyukan soje a kan HKI a dama a cikin makon da ya gabata, daga cikin cilla makamai...
Jami’an kwana-kwana a birnin London na kasar Burtaniya sun bukaci marasa lafiya da likitoci da sauran masu aikin a asbitin Guy da su fice daga asbitin saboda hatsarin samuwar wasu sinadarai masu cutarwa a cikinsa. Jaridar da Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa , da masalin karfe 8.49 ne aka shaidawa jami’an kwana-kwana batun hatsarin, sannan a lokacinda suka karasa cikin asbitin sun yi kokarin samar da iska ne a cikin sa don baje sinadarai masu hatsari ga lafiyar mutane da suke zatun sun sulale sun shiga wurare da dama daban a cikin asbitin. Labarin ya bayyana cewa na fidda mutane kimani 150 daga cikin asbitin. Kuma hotunan da aka watsa ta wayoyi sun nuna mutane a wajen asbitin...
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar. Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin adalci a rabon arzikin kasar. Ana fatan masana daga ciki da wajen kasar zasu gabatar da ra’ayinsu ta shafukan sadarwan da za’a samar a cikin taron. A halin yanzu fiye da shekaru 30 kenan da fita karkashin mulkin wariya na launin fata tsiraru a kasar, amma har yanzun kasar tana fama da matsalolin talauci, rashin aikin yi aikata laifuka da sauransu. Mutane da dama suna...
A yankin Arewa-maso-Gabas, ya ce sojojin, sun kawar da ‘yan ta’adda da dama, sun lalata sansanonin kayan aikinsu, sun kwato makamai, sun wargaza hanyoyin hada-hadarsu tare da samar da amintaccen wuri don sake tsugunar da ‘yan gudun hijira. A cewar Kangye, sojojin sun kama mutane 37 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, tare da kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai, alburusai, kayayyakin masarufi, motoci da babura, sannan kuma sun warware wasu bama-bamai cikin nasara a yankin. Da yake ba da rahoto kan yankin Arewa maso Yamma, Kangye ya ce sojoji sun kama mutane 11 da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da kubutar da mutane 17 da aka yi...
Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wani Mai Unguwa mai shekara 55 a garin Zambuk da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Buhari Abdullahi ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana wanda ake zargin Mohammed Tukur da ke ƙauyen Sabon Gari da ke Zambuk. Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu har lahira a Bayelsa An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun A cewar rundunar ’yan sandan, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Agusta, da misalin ƙarfe 9 na dare, inda ake zargin Mai Unguwar ya yaudari yarinyar (wacce...

‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin
Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin ta ce nan ba da jimawa ba, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar, za su gudanar da zagaye na 3 na ayyuka a wajen cibiyar. ‘Yan sama jannatin 3 da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da irin wannan aiki har sau biyu, a watannin Mayu da Yuni. Baya ga haka, sun kammala ayyukan nazarin muhalli da kula da tantance da kayayyakin aiki a cikin cibiyar da jigilar kayayyaki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Wasu mutum biyu da ake zargin ɗaliban jami’a ne a Jihar Bayelsa sun mutu bayan wata mota ƙirar tifa ta murƙushe su lokacin da suke kan babur mai ƙafa uku a kan hanyar Tombia zuwa Ammassoma. Daily Trust ta samu rahoton cewa haɗarin wanda ya afku a ranar Talata, ya kuma sa wasu fasinjojin da ke cikin babur ɗin sun samu munanan raunuka. Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun A cewar wasu mazauna yankin, haɗarin ya afku ne a kusa da wani lanƙwasa mai haɗarin gaske a kan babbar hanyar, sakamakon rashin kyan hanyar da kuma gudun wuce ƙima. Sun ce babbar motar...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi. “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, sai an biya kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, sai ka bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.” Dan majalisar ya kuma yi...
Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa ayyukan UNRWA, yana mai cewa a shirye Sin take ta yi abun da zai kawo karshen rikicin da samar da mafita mai adalci da dorewa bisa manufar kafa kasashe biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sabuwar mai bada shawara kan harkokin lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan_islam) ta bayyana cewa samar da dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne fatansu. Maryam ta bayyana hakan ne a lokacin da babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ke maraba da ita a ofishin majalisar da ke Abuja. An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Mohammed ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, yana mai cewa zaman lafiya wani abu ne da ake buƙata don jin daɗin rayuwar ɗan Adam, kuma idan ba a same shi ba, ci gaban dimokuraɗiyya da...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙon kan mutane uku. Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata. Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ Odutola ta ce, binciken da jami’an ’yan sandan tafi da gidanka suka yi a jakar wanda ake zargin, ya kai ga gano wasu kan mutane guda uku. Ta ce, jami’an tsaro ne suka gudanar da aikin bincike na yau da kullum daga rundunar ’yan sanda na tafi da gidanka na 71 PMF,...
“Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar ‘yan bindiga,” in ji shi. Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ɗauki matakaki a kan waɗanda suka aikata wannan kisan gilla, sannan ya roƙi jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin kawo ƙarshen duk wata ɓarna a Zamfara. Sarkin Kauran Namoda, Dokta Sunusi Ahmad Rashad, wanda ya raka gwamnan, ya yaba masa bisa saurin ɗaukar mataki bayan faruwar lamarin. “Wannan ziyara tana da...
Gwamnatin Tarayya ta amince a kafa karin sababbin jami’o’i masu zaman kansu guda guda tara a fadin Najeriya. Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya sanar da hakan ranar Laraba lokacin da yake jawabi ga ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa jim kadan da kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa. Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron wanda aka gudanar a Abuja. A cewar ministan, sababbin jami’o’in da aka ba lasisin sun hada da Jami’ar Tazkiyah da ke Kaduna, Jami’ar Leadership da ke Abuja, Jami’ar Jimoh Babalola da ke Kwara da Jami’ar Bridget da ke Mbaise a...
Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne. Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji. Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons Ya ce: “Turji bai miƙa wuya ba. Har yanzu muna neman sa.” Turji na daga cikin manyan ’yan bindigar da ake nema ruwa a jallo a Najeriya. Turji ya jagoranci kai wa al’umma hare-hare a Jihohin Zamfara da Sakkwato, inda suka...
Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19. Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya. Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma. Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba. “Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan...
Dukkanin mutanen biyu na Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike. Kwamishinan ’Yansandan jihar, Emmanuel Olugbemiga Adesina, ya gargaɗi masu aikata laifi su daina ko su bar jihar. Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da masu laifi sun fuskanci hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata al’umma. Bayanin Araqchi, wanda aka yi da sanyin safiyar Alhamis a shafinsa na yanar gizo na dandalin sada zumunta na X, yana mai mayar da martani ga kalaman fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu game da batun kafa “Babban kasar Isra’ila.” A cikin shafinsa na yanar gizo, Araqchi ya yi tambaya cewa: “Shin suna daukan furucin Netanyahu kansa a matsayin mai adawa da wata...

Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da ake kira “Kafa kasar babban Isra’ila”. Wadannan kalamai tana nuna karara aniyar gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasashe masu cin gashin kansu da suka hada da Masar, da Jordan, da Lebanon da kuma Syria, tare da la’akari da su a matsayin babban misali na keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa. A cikin wani rubutu da...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar fari a yankunan da aka mamaye na Falasdinu, ya bayyana cewa; ‘Yan Nazi na karni na 21, wadanda suka kai hari kan babbar tashar ruwa da ke arewacin birnin Tehran a dandalin Tajrish da makami mai linzami, a yanzu haka suna kokarin yaudarar al’ummar Iran da kofin ruwa da aka yi masa magani. Amma al’ummar Iran a tsawon tarihi, sun dauki ko da mafi gogaggen...
Gwamanatin Sudan ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin Allah wadai da shirin kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan Sudan ta yi marhabin da sanarwar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Laraba, inda ta yi watsi da shirin dakarun kai daukin gaggawa na kafa gwamnatin hadaka a yankunan da ke karkashinta. Sanarwar ta yi gargadin cewa wannan matakin na barazana ga hadin kan kasar, kuma yana iya yin kasadar kara ta’azzara rikicin, yayin da aka dakile wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na kungiyar Rapid Support Forces suka kaddamar a yankin kudu da kudu maso yammacin birnin El Fasher. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar...
Lauyan Maïga, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana cewa kamun bai dace ba saboda Maïga ba shi da niyyar guduwa ko lalata shaidu, yana kuma zargin cewa wannan wani mataki ne na siyasa saboda tsohon Firaministan ya daɗe yana sukar gwamnatin soja tun bayan tsawaita mulkinsu ba tare da gudanar da zaɓe ba. Maïga, ya hau kujerar Firaminista a watan Yulin 2021 bayan gwamnatin sojoji ta yi juyin mulki, inda ya goyi bayan dakatar da shirye-shiryen zaɓe don bai wa gwamnatin soja ƙarin lokaci. Sai dai daga baya ya fara sukar wasu matakan gwamnati, musamman bayan an dakatar da shi daga kujerarsa a watan Nuwamban 2024. Tun bayan juyin mulkin 2020 da na 2021, Mali ta kasance ƙarƙashin mulkin soja, kuma...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi mai shekara 18 bisa zargin aikata fashi da makami a jihar. An kama shi ne a garin Kwadon bayan samun sahihin bayani daga jama’a. NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama matashin ne ranar 9 ga watan Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 2:30 na rana. Hakazalika, ya ce an samu ƙunshi ganyen da ake zargin tabar wiwi ne. Bincike ya nuna cewa matashin na cikin mutanen da ’yan sanda ke nema game da aikata fashi da makami, waɗanda ake shari’arsu a babbar kotun jihar. A cewar DSP Abdullahi,...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Gombe ta ce ta lalata wata babbar gonar Tabar wiwi a Karamar Hukumar Kaltungo a jihar Gombe. Hukumar ta kuma ce ta kama miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025. ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Kwamandan Hukumar a jihar, Mallam Maijama’a Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar kulla zumunci da ya kai wa Darakta-Janar na kafar yada labarai mallakar jihar Gombe (GMC), Ibrahim Isa. Ya ce an kama mutum 69 maza da mata da suke kokarin shigar da miyagun kwayoyi cikin jihar a wasu lokuta. Muhammad...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo cutar Amurka mai matukar wahalar magani. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule ya yaba wa jami’an gidan yari da sauran jami’an tsaro saboda sake kama wasu daga cikin waɗanda suka tsere. Ya kuma roƙi jama’a da su kasance cikin shiri su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani mai kama da wanda ake nema. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...