Aminiya:
2025-09-17@23:11:48 GMT

Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa

Published: 6th, February 2025 GMT

A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi.

A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da gargaɗin da mahaifiyarta ta yi mata.

Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga

“Lokacin da mahaifiyar ta samu ’yarta a bakin kogin, sai ta fusata. Duk da gargaɗin da aka yi mata na ƙauracewa kogin, Rachael ta ƙi, wanda hakan ya sa mahaifiyar tashin hankali ta fusata,” in ji wani ganau.

A cikin fushi, an samu rahoton cewa Madam Stella ta kama hannun Rachael kuma ta jefa ta a cikin wuri mai zurfi a kogin sau biyu, wanda ya kai ga mutuwar ‘yarta.

Bayan faruwar lamarin, jama’ar yankin unguwar da abin ya shafa sun tunkari mahaifiyar, inda ta amsa aikata laifinta, inda ta ce ba ta yi niyyar kashe ɗiyarta ba.

Lamarin da ya jefa jama’ar yankin Ukubie cikin firgici, inda wani ɗan uwansu mai suna Jeph Nation ya bayyana ra’ayinsa.

“Na riga na rasa ‘yan uwa guda biyu a wannan shekara, amma wannan shi ne mafi zafi da ban tausayi,” in ji shi.

Hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna Madam Stella ta furta wannan iƙirari da yaren ƙabilar Ijaw, inda jama’a suka kewaye ta.

A wani  bidiyo, an ganta zaune a cikin kwale-kwale da gawar ɗiyarta a gefenta, tana ɗauke da ita.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa, ta bakin kakakinta, DSP Musa Mohammed, ya bayyana cewa har yanzu ba a kai ga sanar da rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda ba a hukumance.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bayelsa Ijaw Mahaifiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin