Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso
Published: 18th, May 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da wani hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga muƙaminsa.
Abba ya dakatar da hadimin ne wanda yake ɗauko masa rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalamai da ya furta kan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo AwoniyiHakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Asabar, 17 ga watan Mayun 2025.
Dawakin Tofa ya ce Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya fitar da sanarwar dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take.
Baya ga haka, gwamnatin ta umarci a rubuta takardar neman bahasi daga hadimin da aka dakatar, bisa kalamansa masu tsauri da suka shafi raɗe-raɗin shirin sauya sheƙa da ake zargin Kwankwaso zai yi.
Gwamnatin ta kuma ja kunnen dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da kada su riƙa fitar da bayanai ba tare da izini ba, tana mai jaddada cewa duk wata sanarwa daga gwamnati sai an tabbatar da ita kafin a bayyana ta ga jama’a.
Gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da hannu cikin kalaman da Rabi’u Ibrahim ya fitar, tana mai cewa wannan magana tasa ce kawai, kuma ra’ayinsa ne shi kaɗai, bisa wasu dalilai da shi kaɗai ya bar wa kansa sani.
Sanarwar ta kuma tunatar da al’umma cewa, Kwamishinan Yaɗa labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Wayya, shi ne kaɗai ke da hurumin yin magana a madadin gwamnatin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ibrahim Rabi u Jihar Kano Rabi u Musa Kwankwaso
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure
Samar da kyakkyawar sadarwa a tsakaninku
Yawan magana da sadarwa mai kyau na hana matsala girma. Idan wani abu ya dame ku, kada ku boye, ku gaya wa juna ta hanya mai dadi da girmamawa.
Gujewa kwatanta rayuwarku da ta wasuKowanne aure yana da nasa halin. Kada ku kwatanta rayuwarku da ta wasu, domin hakan yana iya jefa ku cikin damuwa ko rashin godiya.
Hana magulmata samun damar shiga tsakaninkuMagulmata da masu kyashi suna iya haddasa matsala a aure. Kada ku bari mutane su rarrashe ku da magana mara amfani ko su haifar da rashin fahimta.
Bai wa Juna hakkokiAure yana da hakkoki. Miji yana da nasa, haka ma mata. Ku rika bai wa juna hakkin da shari’a ta tanada, kamar girmamawa, kulawa, da soyayya.
Mutunta ra’ayin juna idan bai kauce hanya baKowa yana da ra’ayi da tunani. Idan ba saba wa addini ko al’ada ya yi ba, yana da kyau a girmama ra’ayin juna domin samun zaman lafiya.
Rashin boyewa juna sirriMa’aurata ya kamata su rika yarda da juna. Idan aka fara boye sirri, hakan yana iya kawo rashin yarda da rashin zaman lafiya. Duk wata matsala, ku tattauna tare.
Allah ya sanya albarka cikin zamantakewar aure.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp