Kungiyar Hizbullah Ta ce Marigayi Shahid Ra’isi Ya Kasance Mai Taimakawa Kasar Lebanon Da Kuma Falasdinawa Ne
Published: 19th, May 2025 GMT
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa.
Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike makamai da dama a rayuwarsa a JMI amma wannan bai canza shi ba, ya kasance yana tambaya ta dangane da gwagwarmaya da HKI a yankin Hizbullah da kuma sauran mujahidai a yankin.
A lokacin shugabancinsa ya taimakawa kungiyar Hizbullah, sosai kamar yanda wadanda suka gabaceshi suka yi. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ce. Sayyid Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran yayi hatsari da jirgin sama mai saukar ungulu a kan hanyar dawowarsa daga makobciyar kasar Azerbai jan inda da shi da ministansa na harkokin waje da kuma limamin masallacin jumma’a na birnin Tabriz duk suka rasa rayukansu a hatsarin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba, don tattaunawa kan yadda gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kai harin wuce gona da iri kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran, cewa: Wannan farmakin da aka kai kan Iran, wani rauni ne ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da kuma nuna cewa dokar daji ta mamaye duniya, kuma wadanda ba su da karfi ba za su iya ci gaba da rayuwarsu ba lamarin da tuni al’ummar Iran suka fahimci hakan da kyau.