Ƙungiya mai alaƙa da Alƙa’ida ta yi iƙirarin kashe sojoji 200 a Buarkina Faso
Published: 16th, May 2025 GMT
Wata ƙungiyar ’yan ta’adda mai alaƙa da ƙungiyar Alƙa’ida ta ɗauki alhakin kashe sojoji 200 a ƙasar Burkina Faso.
Ƙungiyar mai suna Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), ta ɗauki alhakin kai hari a Djibo, arewacin Burkina Faso, tana mai cewa ta kashe sojoji 200.
Wannan ikirarin, wanda cibiyar SITE Intelligence Group mai hedkwata a Amurka ta ruwaito a ranar Alhamis, ya biyo bayan iƙirarin JNIM na baya da ta yi na kashe sojoji 60 a harin.
SITE Intelligence Group, wacce ke sanya idanu kan ayyukan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ta intanet, ta nuna cewa harin wani bangare ne na ƙaruwar ayyukan JNIM a Burkina Faso a cikin watan da ya gabata, wanda ya haifar da asarar rayuka da dama.
Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin Sambisa An kama wata mata kan safarar makamai zuwa KatsinaDuk da cewa babu wani adadi na asarar rayuka a hukumance daga gwamnatin Burkina Faso, rahotanni sun ruwaito mazauna yankin Djibo sun nuna cewa an kashe sojoji da fararen hula da dama.
Sai dai, wata majiyar sojojin Burkina Faso, da take magana da Al Jazeera, ta nuna cewa ƙungiyar ’uan tayar da ƙayar bayan na iya aringizon da adadin waɗanda suka mutu.
Gwamnatin Burkina Faso har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.
Burkina Faso tana fama da ƙaruwar rikicin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin Sahel.
Tun daga shekarar 2019, ƙaruwar tashe-tashen hankula ya raba sama da mutane miliyan da gidajensu, kuma ya nakasa muhimman ababen more rayuwa na farar hula, kamar asibitoci da makarantu.
Duk da alkawuran da gwamnatin mulkin soja, ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Traore, ta yi na inganta yanayin tsaro da ƙulla sabbin ƙawance na tsaro da Rasha, ƙalubalen tsaro na ƙasar sun ƙara tabarbarewa a tsawon lokaci.
Burkina Faso ce ta kan gaba a jerin ƙasashe masu fama da ta’addanci na duniya (Global Terrorism Index) na shekarar 2024, inda ta zama kasa ta farko cikin sama da shekaru goma, baya ga Afghanistan ko Iraƙi, da ta mamaye matsayi na farko.
A shekarar 2023, kusan mutane 2,000 aka kashe a hare-haren ta’addanci 258 a ƙasar, wanda ya kai kusan kashi ɗaya cikin huɗu na mutuwar da ta shafi ta’addanci a duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda hare hare Ibrahim Traore
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar Falasdinu
Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.
A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan yara.
M. Baghai ya bayyana cin zarafi da keta hakkin bil’adama da ka’idojin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a yankunan Falasdinawa da gwamnatin sahyoniyawa ta mamaye a matsayin wani babban cin zarafi ga muhimman ka’idoji da dokokin kasa da kasa.
Ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da shari’o’i a kan gwamnatin Sahayoniya da wakilanta da ke gaban kotun kasa da kasa (ICJ) da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan laifukan yaki da kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama.