A lokacin musayar wuta, sojojin sun harbe biyu daga cikin ‘yan bindigar kuma suka ƙwato shanun da suka sace.

An dawo da shanun zuwa ƙauyen Jebjeb, kuma rundunar sojojin ta ce za tantance su domin mayar da shanun ga masu su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.

Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Hari Taraba Yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 5 sun jikkata yayin da gidan mai ya ƙone ƙurmus a Ribas

Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas.

Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi.

Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba  Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro

Ma’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya.

Ya kuma ce shi da matarsa mai ɗauke da juna biyu sun kuɓuta da ƙyar daga gobarar.

“Na shirya domin ɗaukar fasinjoji zuwa Jihar Ebonyi. Ina buɗe but ɗin motata sai na ji ƙarar gobara.

“Nan take na kwanta a ƙasa, na tashi da sauri na gudu kafin fashewar. Motata ta ƙone, wasu mutane sun jikkata, ni ma na samu rauni.

“Amma cikin ikon Allah babu wanda ya rasa ransa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa motar asibiti ta Sojojin Sama ta zo, inda aka dinga kula da waɗanda suka jikkata, sannan aka ɗauki wasu zuwa asibiti.

A cewarsa jami’an kashe gobara sun isa wajen amma ruwansu ya ƙare, sai da Sojojin Sama suka kai ɗauki sannan suka iya kashe wutar gaba ɗaya.

Wani wanda abin ya shafa, Anthony Ofoke, wanda shi ne mai kula da ayyukan Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi a Jihar Ribas, ya ce gobarar ta lalata motocinsu guda biyu.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 5 sun jikkata yayin da gidan mai ya ƙone ƙurmus a Ribas
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba 
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi
  • An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda
  • ‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi
  • Yadda ’yan bindiga suka kashe jarirai, suka bai wa karnuka namansu a Zamfara 
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi
  • Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte