2025-05-13@14:17:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3707
«Damboa zuwa Maiduguri»:
Shugaban Amurka, Donald Trump ya isa ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda tuni ya sauka a Riyadh a jirgin Air Force One. Shugaban na Amurka ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri. Bom ya kashe jami’an ilimi 2 a Borno...
Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karba-karba a tsarin shugabancin Najeriya. Kudurin dokar na neman wajabta yin karba-karbar kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin yankunan siyasan Najeriya guda 10.
Jaridar “Telegraph” da ake bugawa a Birtaniya ta buga labarin dake cewa; gwamnatin Benjamine Netanyahu ta bai wa kungiyar leken asiri ta waje, umarnin bin diddigin abubuwan da gwamnatin Amurka take yi a cikin sarari da boye. Rahoton ya kuma kara da cewa; Netanyahu yana kokarin fahimtar abubuwan da gwamnatin Donald Trump take yi ne...

Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka da larabawan yankin tekun Pasha kamar...
Wasu ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan motarsu ta taka bom a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri a Jihar Borno. Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bom din a wani hari da kungiyar ta kai a kan babbar hanyar a ranar Litinin. Shaidu sun bayyana cewa, wadanda suka mutun...
A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya. Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin...
Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki. Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai...
Idan aka ga tana da tasiri, ana iya tsawaita ko kuma daidaita matakin. Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa wannan ci gaba zai iya taimakawa wajen farfaɗo da cinikayya tsakanin manyan ƙasashen biyu, kuma zai taimaka wa ƙasashe masu tasowa da ke dogara da su wajen kasuwanci da kayan masarufi. Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici...
Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno. Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa...
Amma sai yanzu gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa a hukumance. Masana tattalin arziƙin sun bayyana cewa kammala biyan wannan bashi wata alama ce ta daidaituwar tsarin kuɗi na ƙasar da kuma yunƙurin rage dogaro da lamuni daga ƙasashen waje. Wasu sun ce hakan na iya ƙara jawo amincewar ƙasashen duniya da hukumomin ba da...
Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero. Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya. NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma...
An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano. Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka. Ya yi wa matar wannan aika-aika ne...
Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasin ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai don takurawa da kuma matsin lambar da takewa gwamnatin kasar Lebanon don kawo karshen kungiyar ba. Tashar talabijin ta Almanar ta nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a jiya litinin, a wanijawabinda ya yi ta tashar talabijin ta...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya. Trump zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta gabatarwa majalisar dokokin kasar sabbin tsare-tsare na shigar kasar ta hanyoyi daban-daban. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Firai ministan kasar ta Burtania Keir Starmer yana fadar cewa abinda yake gabatarwa Majalisar don neman amincewarta, wani tsari ne wanda zai kawo tsabta a harkokin bada Visar shiga kasar Burtaniya daga...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin ratayewa ga wani mutum da ta samu da laifin kashe abokinsa saboda hula. Kotun da ke zamanta a kan titin Miller ta yanke wa mutumin mai suna Adamu Isma’ila Arzai hukuncin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin soka wa abokinsa mai suna Auwal Shehu Kabara wuƙa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da umarnin da Hukumar Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bai wa kamfanonin rarraba wutar da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A. NERC ta bai wa kamfanonin wannan umarni ne sakamakon rashin samar wa...
Dangin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin. Harin ya zo ne a lokacin da ake samun ƙaruwar ayyukan ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar, musamman a yankin Arewa-Maso-Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 2 da miliyan 300 domin sayo na’urar binciken cututtukan zuciya (cardiac catheterization machine) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato. Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan zaman...
Mahaifin tsohon Gwamnan Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Masarautar Zazzau ta tabbatar. Alhaji Ramalan Yero, wanda ɗaya ne daga cikin dattawa kuma mai riƙe rawanin Turakin Dawakin Zazzau ya rasu ne da yammacin wannan Litinin ɗin bayan fama da doguwar jinya. Marigayi Alhaji Ramalan Yero mahaifi ne ga tsohon...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera. Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran...
Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol. ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a...
A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya tare da fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, hakan wani muhimmin mataki ne da bangarorin biyu suka dauka na warware sabaninsu...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za...
Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da...
Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar...
Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na kungiyar Rapid...
Jami’ar Maryam Abacha MAAUN ta rufe wasu gidaje biyu da ke zaman ɗakunan kwanan ɗalibanta mata a Jihar Kano. Hukumar gudanarwar jami’ar ta rufe ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Hotoro da titin UDB a Kano saboda zargin rashin ɗa’a. Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Za mu ci...
Yayin da ake cika shekaru 10 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka watau China-CELAC Forum, kafar yada labarai ta CGTN da hadin gwiwar jami’ar San Martin de Porres da cibiyar nazarin siyasa da tattalin arzikin kasar Sin ta Latin Amurka da jami’ar Santiago de Chile, sun fitar da wani sakamakon...

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari...
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya...
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja. Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar...
Sojojin sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyar da sauran makaman yaki daga a yayin artabun. Majiyoyin sojin sun bayyana cewa, farmakin wani sabon shiri ne na sake tarwatsa shirin ‘yan ta’addan da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su wajen kai muggan hare-hare a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Masana kimiyya suna ƙoƙarin fahimtar yadda garken awaki ke rayuwa a wani tsibiri da ke Arewa maso gabashin Brazil fiye da ƙarni biyu (shekara 200) ba tare da samun tsaftaccen ruwan sha ba. Ba a fayyace yadda ainihin awakin suka hau saman tsaunin Santa Barbara tun a farko ba, wanda ɗaya ne daga cikin tsibirai...
Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar...
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita. Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin...
Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai ci gaba da aikin haƙa danyen mai a Arewa da ke yankin Kolmani. Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ne ya sanar da aniyar kamfanin na ci gaba da aikin haƙar mai a yankunan arewa da gwamnatin Buhari da ta gabata ta fara. Bayo Ojulari ya kuma addada...
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar...
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata....
Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500. Dr. Abdussalam ya kuma yi gargadin cewa da akwai wasu Falasdinawa da sun kai 4000 da suke fuskantar barazanar rasa idanunsu saboda rashin kayan aiki a asibiti da kuma magani. Likitan...
Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba. Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu. ...
Dubun wani ɗan daba da ƙwacen waya da satar babura a cikin shigar mata mata wajen aikata ayyukan laifinsa a unguwar Ɗorayi da ke Jihar Kano ta cika. An kama matashin mai suna Abdullahi, wanda aka fi sani da “Audu Manye,” ne bayan tsawon shekaru ana zargin sa da tunzura faɗan ’yan daba, fashi da...
Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu. Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar. Gwamnatin jihar Bauchi ce ta...
Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar...
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna...
’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara. Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar....
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna...
Kwamitin ya kuma haɗa da Honarabul Sulaiman Adamu Gummi, Kwamishinan Al’amuran Addinai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba, sai kuma Alhaji Habibu Balarabe, Babban Sakataren Hukumar Zakka, a matsayin sakatare. Yayin ƙaddamar da kwamatin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana sa ran tawagar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara...