Mawaƙan APC sun zargi gwamnati da watsi da su a Jigawa
Published: 19th, May 2025 GMT
Wasu mawaƙan jam’iyyar APC da ke Jihar Jigawa, sun bayyana ɓacin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.
Mawaƙan wajen su 35, sun gudanar da wani taro, inda suka bayyana damuwarsu da kuma sanar da cewa sun janye daga duk wata hulɗa da gwamnatin jihar, har sai an ba su kulawar da ta dace.
Shugaban mawaƙan jihar, Lawan Gujungu Mai Babban Gandu ne, ya jagoranci taron, inda ya shaida wa manema labarai cewa tun bayan da sabon gwamnan ya hau mulki sama shekara biyu, har yanzu ba su sharɓi romon dimokuraɗiyya ba.
Ya ce mawaƙan sun yi haƙuri na tsawon lokaci suna sa ran za a saka musu, amma abin ya gagara.
A cewarsa: “Mun shiga mawuyacin hali. Muna cikin APC tun asali, mun yi wa jam’iyya hidima sosai a lokacin yaƙin neman zaɓe, mun ƙirƙiri waƙoƙi da dama don tallata manufofin jam’iyyar da kwatanta cancantar ’yan takararta.
“Amma yanzu da muka ci zaɓe kuma muka kafa gwamnati, an watsar da mu tamkar ba mu da wata ƙima.”
Lawan, ya ƙara da cewa daga yanzu mawaƙan za su nisanci duk wani taro ko aikin da ya shafi gwamnati, har sai an saurare su tare da mutunta su da irin gudunmawar da suka bayar.
Wannan bore ya fito fili ne a daidai lokacin da ake buƙatar jituwa da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar da kuma gwamnatin jihar domin ci gaban al’umma.
Wasu daga cikin mawaƙan da suka halarci taron sun bayyana cewa suna fatan gwamnan zai ji ƙorafinsu kuma ya ɗauki matakin da ya dace, domin ci gaba da gina jam’iyya da gwamnatin da kowa ke alfahari da ita.
Tuni dai wannan batu ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, inda wasu ke ganin cewa ya kamata gwamnati ta sake duba rawar da waɗanda suka ba da gudunmawa kafin kafa gwamnati, domin gudun fuskantar tawaye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Jigawa Ƙorafu Mawaƙa taro
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidar Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Noma Ga Mata Manoma
Hakazakika, an zakulo Mata dalibai daga wasu zababbun makarantun sakandare a jihar da kuma wasu daidaikun Mata a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
Da yake kaddamar da Rabon Kayan, Shugaban Ma’aikatar Fadar Gwamnatin jihar Kaduna Malam Liman Sani Kila, ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu na tallafawa Mata Da Matasa a fadin kasar baki daya.
Hakazakika, ya jinjinawa Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani bisa bubbasar da takeyi wajen tallafawa Mata Da dalibai Mata Da masa abin a Yaba ne Yana Mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta himmatu wajen ciyar da aikin Noma a jihar Kaduna.
Kila ya kuma jinjinawa Hajiya Hafsat Uba wajen jajircewata wajen Tabbatar da cewa duk wani tallafi na uwargidar shugaban kasa take aikowa Kaduna Yana kaiwa ga mata.
Yace Gwamnatin Uba Sani ta ware Kashi 70 cikin dari na kasafin kudin jihar wajen harkar bunkasa aikin Noma Wanda a tarihin jihar Kaduna ba’a taba samun Gwamnatin da tayi irin haka ba.
Ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin da suyi amfani da Kayan wajen dogoro da kansu maimakon su sayar dasu.
Shugaban yace Babu shakka wannan Shirin zai taimakawa ci gaban rkyuwar Mata. Yace Rabon Kayan na wannan karon ba Mata zalla kadai bane Zasu amfana yarda dalibai maza da mata a fadin jihar Kaduna baki daya.
Da take nata jawabin uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani ta bayyana cewa uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu tana da burin tallafawa ci rkyuwar Mata da Yara domin farfado da tattalin arzikin jihar Kaduna Ta bangarori da dama.
Tace wannan Shirin zai tamaka wajen bunkasa ci gaban rkyuwar Mata da Yara a fadin jihar Kaduna tana Mai cewa ya zama wajibi daukacin matan jihar Kaduna su nuna goyon bayansu da uwargidar shugaban kasa a kokarin da take da inganta rayuwarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp