Riƙaƙƙun ’yan daba da dilolin ƙwaya 31 sun shiga hannu a Kano
Published: 17th, May 2025 GMT
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Tsaro da Gyaran Matasa, ya kama ’yan daba 31 a wani samame da ya gudana a unguwanni bakwai a jihar.
An kai samamen ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayu, 2025 ƙarƙashin jagorancin Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata.
Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a BornoUnguwannin da aka kai samamen sun haɗa da Ɗorayi, Ja’in, Sharada, Unguwar Dabai, Dukawa, Kabuga, Kofar Mata da sauransu, wuraren da suka yi ƙaurin suna wajen aikata laifuka.
Daga cikin waɗanda aka kama, mutum 25 ana zargin ’yan daba ne, yayin da shida ake zarginsu dallacin miyagun ƙwayoyi.
A cikin kayan da jami’an suka ƙwato akwai bindigogi na gargajiya guda huɗu, wuƙaƙe da adduna tara, sanduna uku, tabar wiwi da kuma ƙwayoyi irin su Exol guda 173 da wasu miyagun ƙwayoyi daban-daban.
Haka kuma, jami’an sun kama wasu riƙaƙƙun ’yan daba da suka daɗe suna addabar al’ummar Dorayi, ciki har da Dan Abba, Bola, Baka Kashi, Ramos, Abba Maciji da Abdul Baki.
“Dukkanin ’yan daban 25 da muka kama an gurfanar da su a gaban Kotun Majistare mai lamba 16 da ke kan titin Zungeru, kuma an tasa ƙeyarsu zuwa gidan gyaran hali.
“Sauran masu sayar da ƙwayoyi guda shida, ciki har da Rabi’u Hamza, an miƙa su ga hukumar NDLEA don ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a kotu,” in ji Dokta Kofar Mata.
Ya bayyana wannan samame a matsayin babban ci gaba wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya ce unguwanni kamar Dorayi sun sha fama da rikice-rikicen faɗan daba sama da shekaru 20.
Kama waɗannan ɓata-gari zai iya kawo ƙarshen wannan matsala.
Ya ƙara da cewa kwamitin ya ƙunshi jami’an tsaro da jami’an gwamnati domin haɗa kai wajen tsaftace birnin Kano da kuma taimaka wa matasan da suka ɓace su koma turbar gaskiya.
“Kwamitin Haɗin Gwiwa zai ci gaba da jajircewa domin ganin an samar da ingantaccen tsaro da kuma zaman lafiya ba tare da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ba a Kano,” in ji kwamitin.
Ga hotunan wasu daga cikin kayan da kwamitin ya ƙwato:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamiti kwayoyi Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan.
A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton.
Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba.
Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa a ayyukan tsaro da ake gudanarwa a fadin jihar.
A wani labari mai nasaba da haka, Kungiyar Matan Sojoji da ‘Yansanda (DEPOWA) ta yaba da jajircewa da sadaukarwar dakarun rundunonin sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro, wadanda ke ci gaba da sadaukar da rayuwarsu domin kare kasar.
Kungiyar ta kuma yi addu’a ga Allah domin kare mazajensu, wadanda ke kwana suna tashi a kan bakin aiki domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya.
Shugabar kungiyar DEPOWA, kuma matar Babban Hafsan Tsaro na Kasa (CDS), Mrs. Oghogho Musa, ta bayyana wannan godiya tare da yin addu’o’i a birnin Abuja yayin gudanar da wasan motsa jiki na rawa (Dance Aerobics Edercise) da aka gudanar a makarantar DEPOWA da ke sansanin Mogadishu.
Shugabar DEPOWA ta kuma jaddada kudirin kungiyar na gudanar da yakin addu’a da godiya na tsawon shekara guda ga dakarun da ke bakin daga, domin nuna yabo da godiya ga jajircewarsu wajen kare kasar Nijeriya, duk da hadarin da ke tattare da aikin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA