Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya
Published: 17th, May 2025 GMT
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar cewa, za a fara jigilar maniyyatan jihar a ranar Lahadi 18 ga wannan wata na Mayu, 2025, zuwa Ƙasa Mai Tsarki.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Badaru Bello Karofi, ya shaida wa wakilinmu, cewa maniyyatan da suka fito daga Malunfashi da Bakori, Ƙanƙara, Dandume, Ƙafur da Ɗanja sune rukunin farko da ake sa ran za su tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa da ke cikin babban birnin jihar.
Tun farko sai da jagoran mahajjatan jahar, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Joɓe ya bayyana cewar, gwamnatin jihar ta ɗauki duk wasu matakan da suka wajaba tun daga gida har zuwa Ƙasa Mai Tsarki domin ganin cewa mahajjatan jihar sun samu duk wata kulawa a hukumance don gudanar da aikin ibadar cikin jin daɗi da walwala.
Sai dai Amirul Hajjin ya ja hankalin maniyatan da su kiyaye duk wata doka, tun daga nan gida har a can Saudiyya inda suke ɗaukar hukunci mai tsanani ga wanda ya saɓa, musamman shiga da duk wani nau’in abin da zai sa maye da sauransu.
Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aure ISWAP ta yi wa manoma 15 yankan rago a Bornoউৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ƙasa Mai Tsarki maniyyata Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina
Wani mazaunin Safana, Iliyasu Sani, ya ce sulhun ya kawo sauƙi ga rayuwar jama’a, domin yanzu suna iya zuwa kasuwa da yin noma ba tare da fargaba ba.
Masani a fannin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce talauci da rashin tsaro ne suka sa jama’a neman mafita da kansu.
Ya kuma bayyana cewa idan duk ɓangarorin suka tsaya kan alƙawarin da aka yi, wannan sulhu na iya zama mataki na farko na samun zaman lafiya na dindindin a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp