Sojoji Sun Kashe Na Hannun Daman Bello Turji A Sokoto
Published: 19th, May 2025 GMT
Rundunar Sojin ƙasar nan ta tabbatar da kashe shahararren ɗan bindiga kuma na hannun daman Bello Turji, Alhaji Shaudo Alku a wani hari da aka kai da jiragen yaƙi.
Rundunar Operation Fasan Yama ce ta kai harin a ranar Lahadi 18 ga wannan watan nan na Mayu a wata maɓoyar ƴan bindiga da ke kusa da makarantar firamare a garin Tunfa da ke ƙaramar hukumar Isa a jihar Sokoto.
A cewar rundunar sojin, ɗan bindiga Alku, ya zo Nigeriya ne sakamakon wata gayyatar taro da ƴan bindiga suka yi masa inda aka far musu a hanya tare da wasu kwamandodin ƴan bindigar.
Bello Turji dai yana cikin jerin sunayen ƴan bindigar da hukumomin tsaro a kasar nan suka bayyana suna nema ruwa a jallo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp