Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba
Published: 16th, May 2025 GMT
Sojojin da suke aiki a ƙarƙashin rundunar birget ta 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu guda dubu ɗaya daga hannun ɓarayin shanu.
Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojoji ta birget ta 6 da ke garin Jalingo, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Jalingo a ranar Juma’a.
Ya ce, nasarar ƙwato shanu tare da kashe ’yan bindigar ya kasance ne biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu dangane da shuguban wasu guggun ’yan bindigar akan bubura talatin inda suka shiga wani yanki na Ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo domin satar shanun makiyaya.
Kyaftin Oni ya bayyana cewa, yan ta’addan sun shigo Jihar Taraba ne daga Jihar Filato domin aikata ta’addanci tare da sace shanu.
Ya ƙara da cewa, ’yan ta’addan sun shiga yankin Jebjeb ne domin satar shanu a wasu rugagen Fulani, amma dubunsu ta cika inda sojojin suka kashe biyu daga cikinsu kuma suka fatattaki sauran tare ƙwato shanu har dubu ɗaya waɗanda su ’yan ta’addan suka sace.
Ya ce, a halin yanzu sojojin na tantace masu shanu domin a mayar masu da shanun su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Karim Lamido Taraba ƙwato shanu
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Mai A Legas
A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso da tabbatar da tsaron jama’a yayin aikin kashe gobarar.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, Shakiru Amodu, ya tabbatar da cewa an samu nasarar kashe gobarar kafin ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.
Kafin ƙarfe 6 na yamma, jami’an agajin gaggawa sun shawo kan lamarin gaba ɗaya, tare da killace yankin da abin ya shafa domin kaucewa wata barazana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp