HausaTv:
2025-05-19@12:35:00 GMT

Iran : zamu ci gaba da inganta uranium ko da yarjejeniya ko babu

Published: 19th, May 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya gargadi Amurka game da gabatar da “bukatun da ba su dace ba” a tattaunawar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da inganta sinadarin Uranium tare da ko ba tare da wata yarjejeniya da Washington ba.

Abbas Araghchi na mayar da martani ne ga furucin da manzon shugaban kasar Amurka a yankin Steve Witkoff ya yi cewa, Washington ba za ta bar Iran ta samu karfin sarrafa sinadarin Uranium ba, ko da kashi 1%.

Mista Araghchi, wanda shi ne babban mai shiga tsakani na Iran, ya shaida wa manema labarai cewa, irin wadannan kalamai sun kauce wa tattaunawar.

Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa Tehran a shirye take ta nuna cewa ba ta da niyyar kera makaman kare dangi idan Amurkawa suka so.

A wata hira da gidan talabijin na ABC na “Wannan Makon,” Witkoff ya ce “Jan layi” na gwamnatin Trump a tattaunawar nukiliya da Iran shi ne cewa Tehran ba ta da ikon inganta makamashin Uranium.

“Idan Amurka na son tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makaman nukiliya ba, yarjejeniya tana kan gaba, kuma a shirye muke mu shiga tattaunawa mai mahimmanci don cimma matsaya da za ta tabbatar da wannan sakamako a cikin dogon lokaci.

Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya ce nan ba da jimawa ba za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran da E3 sun kuduri aniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran

Iran da kasashen turan nan guda uku sun da ake wa lakabi da E3 sun kudiri anniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar kasar ta Iran.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran da kasashen Turan uku Birtaniya da Faransa da Jamus (EU-3) sun kuduri aniyar yin amfani da diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Gharibabadi ya bayyana hakan ne a shafinsa na X bayan ganawarsa da wakilan kasashen Turan uku na yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi shi ma ya halarci taron.

Ya ce, wakilan Iran da daraktocin siyasa na EU-3 sun yi musayar ra’ayi tare da tattauna halin da ake ciki na shawarwarin nukiliya tsakanin Iran da Amurka da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.

Ya ce Iran da EU-3 za su sake haduwa, idan akwai bukata, don ci gaba da tattaunawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Fatan Tattaunawar Kasarsa Da Amurka Ta Cimma Yarjejeniya Ta Gaskiya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Kasarsa Ta Jajirce Kan Harkokin Diflomasiyya Domin Kare Hakkokinta   
  • Taron Tehran ya bukaci tattaunawa cikin gaggawa kan kalubalen yankin  
  • Tehran ta yi kakkausar suka kan tsare Iraniyawa a Birtaniya
  • Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Ginin Babban Asibitin Anka Da Aka Inganta
  • Ayatullah Khamenei : “Ba inda Rundunar Amurka ta taba shinfida zaman lafiya “
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Yuraniyom Don Aikin Cikin Gida
  • Iran da E3 sun kuduri aniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran
  • Iran ta ce babu wata rubutaciyar shawara da ta samu daga Amurka