Isra’ila Ta Kai Hari Ga Rumbun Magungunna A Kudancin Gaza
Published: 19th, May 2025 GMT
Hukumar da ke bayar da agajin magungunna ga Falasɗinawa ta ƙasar Birtaniya ta ce Isra’ila ta kai wani hari da ya afkawa rumbun ajiyar magungunna na Asibitin Nasser da ke yankin Khan Younis a tsakar daren da ya gabata a kudancin Gaza .
Hukumar ta ce harin ya auku ne “lokacin da ake kwashe Falasɗinawan da aka kashe da waɗanda aka jikkata zuwa asibiti, bayan wasu jerin hare-haren da Isra’ila ke kai”.
Daga cikin magungunnan da harin ya lalata sun haɗa da waɗanda hukumar ta samar wa asibitin na Nasser. “A yanzu dai muna kallo dukan magungunna da muka bayar tallafi sun ƙone ƙurmus” in ji kakakin hukumar.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da hotunan wuraren da harin ya shafa. Kafar yaɗa labaran Falasɗinawa ta bayar da rahoannin cewa hare-haren da aka kai a birnin sun yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane.
Rundunar sojojin saman Isra’ila ta fitar da wata sanarwa cewa a cikin kwana guda kaɗai ta kai hare-hare har 160 a wurare daban-daban da ta ke hara.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Allah Ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa
Allah Ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa.
Wannan na cikin wani saƙo da fitacciyar marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a daren ranar Lahadi.