Minista Ya Ƙaryata Ji-ta-ji-tar Mayar Da Taron Bayanin Ministoci Zuwa London
Published: 16th, May 2025 GMT
“Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.
“Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”
Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.
Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba ne.
Idris ya kuma taɓo batun tattalin arzikin ƙasa, inda ya yi nuni da Rahoton Nuna Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025 da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta fitar.
Ya ce: “Yau, ina farin cikin bayyana wani labari mai daɗi daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, wadda ta fitar da Rahoton Nuna Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025, jiya. Bisa ga rahoton, adadin hauhawar farashin kayayyaki na watan Afrilu ya tsaya a kashi 23.71, wanda ke nuna ragin kashi 0.52 daga 24.23 da aka rubuta a watan Maris 2025.
“Haka kuma, idan aka kwatanta wata da wata, hauhawar farashin ya ragu sosai da kashi 2.04, daga 3.90 a Maris zuwa 1.86 a Afrilu.
“Wannan ba ya faruwa haka ziƙau. Tsare-tsaren Shugaban Ƙasa da aka mayar da hankali a kai su ne suke haifar da ɗa mai ido. Fa’idar gyare-gyaren da ake yi, ko da yake a hankali suke zuwa, tabbatattu ne kuma mutum zai iya auna su.”
Ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyakin abinci – wanda ke ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi – ya fara raguwa sakamakon tsare-tsaren Shugaban Ƙasa Tinubu.
Ya ce: “Ɗaya daga cikin manyan alamu na sauƙin da ake samu shi ne ƙimar hauhawar farashin abinci. Duk da cewa farashin abinci har yanzu yana damun mutane da dama a Nijeriya, hauhawar farashin abinci daga shekara zuwa shekara ya ragu zuwa kashi 21.26 a watan Afrilu.
“Idan aka duba wata zuwa wata kuwa, ya ragu zuwa kashi 2.06, daga kashi 2.18 da aka samu a Maris. Wannan cigaba mai kyau ya samo asali ne daga ragin farashin muhimman kayan abinci irin su garin masara, hatsi, garin doya, kuɓewa, gyaɗa, shinkafa, da wake.
“Jama’a, mun san cewa har yanzu ba mu kai inda muke fatar kaiwa ba. Amma waɗannan alƙaluman da aka samu kwanan nan suna ba mu cikakken dalili na yin fatan alheri. Suna nuna cewa matakan da muka ɗauka masu wahala sun fara haifar da kyakkyawan sakamako. Kuma yayin da farashi yake sauka, muna sa ran ganin sauƙi a ƙarfin sayen kayan masarufi da kuma rayuwar jama’a gaba ɗaya.”
Ministan ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da ɗaukar matakan da ke mayar da hankali kan rayuwar jama’a don kawo sauƙi, da dawo da daidaiton tattalin arziki, da inganta walwala ga kowa da kowa.
Ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da ba da labarin irin wannan cigaban cikin gaskiya, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da zama mai gabatar da komai a bayyane kuma amintacciya ga ‘yan ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: hauhawar farashin a watan Afrilu
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”.
Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa.
Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA