Aminiya:
2025-10-13@18:07:12 GMT

Layya: Farashin raguna na iya tashin gwauron zabo

Published: 16th, May 2025 GMT

A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin raguna da sauran dabbobin lauya zai yi tashi gwauro a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen dabbobi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A farkon watan nan na Mayu ne Gwamnatin Nijar ta sanar cewa matakin na da nufin daidaita farashi dabbobin layya a cikin gida da kuma tabbatar da wadatarsu ga al’ummarta —waɗanda mafi rinjaye Musulmi ne — kafin zuwan Babbar Sallah a farkon watan Yuni.

Haramcin ya shafi fitar da shanu da tumaki da awaki da raƙuma, tare da alƙawarin tsauraran matakan aiwatar da dokar daga hukumomin tsaro.

Ƙungiya mai alaƙa da Alƙa’ida ta yi iƙirarin kashe sojoji 200 a Buarkina Faso Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin Sambisa NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027?

Ana fargabar wannan matakin zai yi mummunar illa ga ƙasashe kamar Najeriya da Kwaddibuwa, waɗanda suka dogara da shigo da dabbobi daga Nijar, musamman ma raguna da raƙuma a lokutan da buƙata ta yi yawa.

’Yan kasuwan Najeriya na neman mafita

’Yan kasuwar dabbobi a manyan kasuwannin Kano da Jigawa na fargabar cewa matakin na gwamnatin Nijar zai iya kawo ƙarancin dabbobin da hauhawar farashi a Najeriya a lokacin Babbar Sallah.

Wani tsohon ɗan kasuwar dabbobi a kasuwar dabbobi ta Wudil a Jihar Kano, Malam Abdullahi Abdul, ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Nijar muhimmiyar ƙasa da ke samar da raguna, musamman a lokacin sallar Layya.

Wannan lamari ya sa ’yan kasuwan Najeriya da dama neman hanyoyin samar da dabbobi daga ƙasashe kamar Kamaru da Chadi.

Yayin da ake ƙoƙarin cike giɓin, ’yan kasuwa na tunanin za a samu hauhawar farashi saboda  bambancin canjin kuɗade ƙasar waje.

Alhaji Bello Guri, wani ɗan kasuwar dabbobi, ya buƙaci jama’a da kada su firgita, yana mai cewa sun fara shigowa da dabbobi Najeriya daga wasu ƙasashe.

Ya kuma yi nuni da cewa yadda mutane ke ƙara yawaita kiwon dabbobinsu na Layya zai iya rage dogaro a kan na kasuwa.

Kasuwar Maigatari ta shiga rashin tabbas

Kasuwar Dabbobi ta Duniya ta Maigatari a Jihar Jigawa, wadda muhimmiyar cibiya ce ga kasuwancin dabbobi daga Jamhuriyar Nijar da kuma cikin Najeriya, tana fuskantar koma baya.

Malam Dauda Babandi Gumel ya bayyana kasuwar a matsayin “kufai,” saboda ƙarancin dabbobi, a yayin da ’yan kasuwar Najeriya masu lasisin fataucin dabbobi daga Nijar ke fuskantar rashin aikin yi.

Wannan lamari ya haifar da damuwa game da yiwuwar samun ƙarancin dabbobi gabanin Babbar Sallah ta bana.

Tsadar ta damu masu saye

Alamomin kasuwa na yanzu sun nuna farashin dabbobi sun tashi sosai idan aka kwatanta da bara.

Ragon da aka sayar N120,000 a shekarar 2024 yanzu farashinsa ya kai tsakanin N170,000 zuwa N200,000. Farashin ɗan maƙi kuma ya ɗaga daga N600,000 zuwa N850,000 zuwa miliyan ɗaya.

Abbas Idris, wani mazaunin Kano, ya nuna damuwarsa cewa mutane kaɗan ne za su iya yin layya a bana idan farashin bai sauka daga yadda yake yanzu ba.

Mutane da yawa, kamar Alhaji Shehu Sharu kuma, sun zaɓi su haɗa kuɗi tare da abokansa su sayi dabbar layya saboda hauhawar farashin.

Malam Idris Isma’ila Zango, wani ma’aikacin gwamnati, ya nuna takaici cewa layya ta fi ƙarfinsa, yana mai cewa raguna sun yi tsada idan aka kwatanta da albashinsa.

Matasalar ta fi haka —Masana

Bayan haramcin da Nijar ta sanar, ƙwararru irin su Dakta Aminu Rimi, masanin kasuwancin dabbobi, sun danganta hauhawar farashin ga wasu dalilai kamar yawaitar sace-sacen dabbobi da kuma gazawar manoma wajen amfani da dabarun kiwo na zamani.

Ya jaddada muhimmancin cikakken aiwatar da Shirin Zamanantar da Kiwo na Ƙasa (NLTP) don inganta samar da dabbobi.

Ibraheem Muazzam, manazarcin harkokin kasuwanci da ke Kano, ya bayyana takunkumin da Jamhuriyar Nijar ta sanya a matsayin mataki da aka yi da lissafi da dabarun siyasa daga gwamnatin sojin Nijar don tabbatar da muhimmancin ƙasar a fannin tattalin arzikin yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Babbar Sallah kasuwa Layya Najeriya Nijar raguna Jamhuriyar Nijar kasuwar dabbobi Babbar Sallah

এছাড়াও পড়ুন:

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar.

 

Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya kamata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tarihin Hassan Usman Katsina (1) October 11, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique October 11, 2025 Daga Birnin Sin Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
  • Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara