2025-05-18@09:55:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9

«sarki mai daraja ta ɗaya»:

    A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki. Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar. “Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a yi hakan a wasu jihohi sama da 20. Matsalar tsaro ta zama ta ƙasa baki ɗaya, ba na yanki guda ba. Wannan ba siyasa ba ce. Idan ba mu ɗauki mataki yanzu ba, lamarin na iya shafar ƙasa gaba ɗaya,” in ji shi. Dangane da kiraye-kirayen amfani da dakarun haya daga ƙasashen waje...
    Khalifa Aminu, matashi ne mai shekaru 19 wanda ya ƙirƙiri na’urori da abubuwan ban mamaki waɗanda hatta mutanen da suka zurfafa karatu a fannin kimiyya da kere-kere ba su sami irin wannan nasarar ba. A tattaunawarsa da Aminiya, Khalifa wanda ya ce da kyar ya iya kammala karatunsa na sakandare, ya bayyana yadda ya kirkiro wata sabuwar na’ura da ke iya gano ma’adinan karkashin kasa ko bam a cikin dakika guda, da kuma tabarau da ya kirkiro mai taimaka wa makafi wajen yin tafiya ba tare da sun yi karo ko sun fada cikin wani hadari ba. Hajjin Bana: Gwamnatin Jigawa ta aika wa NAHCON Naira biliyan 6  ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe  Ɗan asalin Jihar Kano,...
    Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu, 2025, Sarki Sanusi II ya sanar da ɗaga likafar baffansa kuma Wamban Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, zuwa  matsayin sabon Galadiman Kano. Kasa da makonni biyu bayan haka, a ranar 21 ga Afrilu, 2025, Sarki Aminu Ado Bayero ya mayar da martani ta hanyar naɗa babban yayansa kuma ɗan fari ga marigayi Sarki Ado Bayero, Sanusi Ado Bayero, a matsayin nasa Galadiman Kano. Wannan sabon...
    Duk da kasancewarta matar aure kuma uwa daga Arewacin Nijeriya, sannan kuma ga karatu tana yi, a lokaci guda, amma hakan bai hana ta samun nasarar zama gwarzuwar ɗalibar da ta kafa sabon tarihin da sai da aka shekara 35 rabon da a samu wani mahaluki da ya kafa irinsa a fannin ilimin shari’a. A yayin da take karatu, A’isha Widad, mai shekara 24 a duniya, ta fuskanci ƙalubalen da suka danganci haɗa karatu mai zurfi da kuma rayuwar aure — kama daga ɗawainiyar kula da gida zuwa na juna biyu da na jego da kuma shayarwa — amma duk da haka, ta kafa tarihin zama mutum ɗaya tilo da ta kammala digirinta na farko da Daraja na ɗaya (First...
    Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna. An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa. Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu...
    Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23. Fulham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa. Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta...
    Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
    Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
    Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
۱