Crystal Palace ta lashe kofin FA na farko a tarihinta
Published: 17th, May 2025 GMT
Crystal Palace ta doke Manchester City da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasa na Wembley a ranar Asabar, inda ta lashe Kofin FA karo na farko a tarihinta.
Eberechi Eze ne, ya zura ƙwallo ɗaya tilo tun da aka fara wasan, yayin da mai tsaron ragar Crystal Palace, Dean Henderson ya taka rawar gani a wasan wajen hana Man City zura ƙwallo.
Man City ta rasa damar yin kunnen doki a wasan bayan Omar Marmoush ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Henderson, ya tsallake rijiya da baya, bayan duba VAR kan yiwuwar ko hannunsa ya taɓa ƙwallon a wajen yadi na 18.
Wannan nasara ce ta farko da Palace ta taɓa samu a gasar manyan kofuna cikin shekaru 120.
Man City kuwa, wannan na nuna cewar kakar wasanninta ta bana an yi uwa kwance ɗa kwance, wato ba ta lashe kowane kofi ba, hakan na iya ƙara wa kocinta, Pep Guardiola matsin lamba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Crystal Palace Ƙwallo Wasan Ƙarshe
এছাড়াও পড়ুন:
Gini ya kashe Ba’indiye a Zariya
Wani ɗan ƙasar Indiya, Harpal Singh, ya rasa ransa bayan katangar rumbun ajiya ta kamfanin ATCO da ke Zariya ta rushe a kansa ranar Talata.
Mutumin dai daya ne daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke unguwar Cikaji a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai Ana shirin mayar da rantsar da Shugaban Nijeriya zauren majalisaWani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa Aminiya cewa Ba’indiyen ya gamu da ajalinsa ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Talata, bayan tashin guguwa gabanin a fara ruwan sama.
Ma’aikacin ya ce sai dai ba a san musabbabin rushewar katangar ba, sakamakon lokacin da lamarin ya faru ba lokacin aiki ba ne kuma ba a san abin da ya kai mamacin wurin ba.
Tuni dai aka garzaya da gawar marigayin Harpal ɗakin adana gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya.
Sai dai wakilin namu ya yi ta ƙokarin tuntuɓar Kakakin Rundunar ’Yan Sandar jihar Kaduna DSP Mansur Hassan kan lamarin, amma wayarsa ba ta shiga.