Tehran ta yi kakkausar suka kan tsare Iraniyawa a Birtaniya
Published: 19th, May 2025 GMT
Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Birtaniya a birnin Tehran, biyo bayan tsare wasu ‘yan kasarta da dama ba bisa ka’ida ba a kasar.
Shugaban bangaren kula da sashen yammacin turai a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi kakkausar suka da nuna adawa da matakin na gwamnatin Birtaniyya, da kuma zarge-zargen da ba su dace ba da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Jami’in ya ce tsare ‘yan kasar Iran ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da kuma hakkokin bil’adama da aka amince da su, saboda an tuhume su ba tare da wata hujja ba.
Ya kara da cewa ‘yan kasar Iran da ake tsare da su, an kuma hana su harkokin ofishin jakadanci da kuma ba su kariya…
Jami’in na Iran ya jaddada cewa gwamnatin Birtaniyya ce ke da cikakken alhakin irin wadannan ayyuka, wadanda ake ganin suna da alaka da siyasa domin matsin lamba kan Iran.
A ranar Asabar an kama wasu mutane hudu ‘yan kasar Iran, kuma An tsare su ne a karkashin dokar ta’addanci, kamar yadda kafafen yada labaran Burtaniya suka ruwaito.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Yuraniyom Don Aikin Cikin Gida
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kiyaye ci gaba da sarrafa sinadarin yuraniyon da tushen kayan aikin makamashin nukiliya ba abubuwa ba ne da za a tattauna a kansu
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta samar da kwarin gwiwa dangane da ci gaba da zaman lafiya a shirinta na makamashin nukiliya, amma ba za ta iya tauye hakkin jama’ar Iran na halal da kuma hakkinsu na samar da makamashin nukiliya cikin lumana ba, ciki har da inganta sinadarin yuraniyom domin zaman lafiya ba.
A wata ganawa ta hadin gwiwa da tare da tawagar babban taron kasa da kasa na Pugwash da hukumar makamashin nukiliya ta Iran ta shirya a yammacin jiya Juma’a, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya jaddada matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da bukatar Iran ta aiwatar da hakkokinta na shari’a a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.