2025-11-28@00:11:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 292

«maniyyaciya»:

    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya...
    Sudan ta yaba da kokarin zaman lafiya da Amurka da Saudiyya suka yi na dakatar da zubar da jini a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, Majalisar Mulkin Sojan Sudan ta yi maraba da “kokarin Saudiyya da Amurka na kawo zaman lafiya mai ga Sudan.” Ta gode wa Washington da...
    Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar...
    Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare...
    Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar...
    El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan...
    Bayan hukunci, kwamitin gudanarwa karkashin shugabancin Damagum ta dakatar da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature na tsawon wata guda saboda zargin ayyukan da ke goyon bayan abin da ya saba wa jam’iyya. Bayan awanni 24, Anyanwu da magoya bayansa...
    A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu...
    Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace  uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban...
    Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake...
    Fidan ya ci gaba da cewa akwai bukatar fara aiwatar da kudirin da aka cimma yayin taron kasashen Musulmi na OIC da kuma Arab League dangane sake gina Gaza don karfafa da kuma tallafar rayuwar dimbin Falasdinawan da Isra’ila ta tagayyara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga November...
    Dangane da fargaba game da karancin abinci na amfanin gona da aka canza jinsinsu (GMOs), farfesan ya ce domin tabbatar da lafiyar abinci da kare lafiyar jama’a, dole ne kowace iri da za ta shigo kasar ta bi matakan doka da ka’idoji da ke tabbatar da cewa tana da aminci. Ya ce, dokokin da ake...
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa  dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai  kara karfafa zaman lafiya a yankin...
    Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice  daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.   Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa...
    Ministan Babban Birnin Tarayya , Nyesom Wike, ya yi gargadin cewa irin yadda gwamnonin jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta a yanzu, zai iya sanadin rushewar jam’iyyar. Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnonin PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar yadda...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN), a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) na shida da aka tabbatar da shi. An gudanar da wannan gajeren bikin rantsarwa ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. NAJERIYA A YAU: Me Dawowar...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar...
    “Sanata Wadada yana cikin rijistarmu tun da farko, kawai mun sake ba shi sabon katin zama mamba ne. Don haka, barka da dawowa gida,” in ji shi. Dakta Bello ya ce APC za ta ci gaba da karɓar duk wanda ke son dawo wa jam’iyyar kuma yana kishin ƙasar nan. A nasa ɓangaren, Sanata Aliyu...
    Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon...
    Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai. Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi. Shugaban hukumar ta IAEA ya...
    Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara...
    Jam’iyyar ADC ta ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohi suka yi zuwa jam’iyya mai mulki ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, ke ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya. A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ba su damu da abin...
    Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina...
    “Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki.   “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,”...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara....
    Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar...
    “Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima.   Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda...
    Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-ker ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki. Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere (ASUP) reshen makarantar ta fara yajin aikin ne daga yau Talata, 39 ga Satumba, 2025. Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne bayan zaman da ta yi da wakilan gwamnatin jihar, inda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.   Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya...
    Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci. A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita...
    Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin...
    Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba. Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama. Yadda...
    Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan...
    Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing. Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas. Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar. NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025...
    Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba...
    Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma...
    Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar...
    Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Saudiyya na iya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin sahayoniyya ba za ta kuskura ta kai hari ko kai wa wata kasa ta Musulunci hari ba matukar kasashen musulmi suka hade kansu; kuma Saudiyya za ta iya taka...
    Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000 Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan...
    Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a...