Ya ce da Kwankwaso bai yi tunanin samar da jami’ar Wudil ba, da wannan alherin ba za a same shi ba, suna gode wa sauran wadanda suke ba da gudummawa wajen habakar wannan jami’ar.

Alhaji Abdukadir ya yi kira ga magoya baya da masu tasowa cewa idan suka sami dama su yi koyi da jagoran Kwankwasiyya, wanda ya kafa jami’o’i guda biyu a Jihar Kano bayan makarantu na gaba da sakandare guda 24 da ya samar da kuma tura dalibai talakawa karatu kasashen waje da mafi yawa sun gama suna amfanar da ci gaban al’umma.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kwankwaso

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.

’Yan ta’addan sun kai hari makarantar  ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.

Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.

An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.

Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.

Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.

“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro  yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar