Jagora: Jamhuriyar Musulunci Ba Ta Bukatar Izinin Wani Mahaluki Domin Tace Sanadarin Uranium
Published: 20th, May 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda yake mayarwa da Amurka martani ya bayyana cewa: Ya kamata su daina yin Magana maras ma’ana, fadin cewa Iran ba ta da izinin tace sanadarin Uranium, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci ba ta da bukatar izinin wani mahaluki.
Jagoran juyin musuluncin na Iran wanda ya gana da iyalan shahid Ra’isi da sauran shahidan hidima, da safiyar yau Talata, ya kara da cewa: Manufar girmama shahidai da kuma jinjinawa ayyukan da su ka yi, shi ne daukar darussa daga rayuwarsu.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Abinda ake fada dangane da shahid Ra’isi shi ne cewa ya kasance mai dukkanin siffofin jami’in da yake wakiltar hukumar da ta ginu akan bin tsarin Allah, wanda ya kasance ya yi aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba.” Haka nan kuma jagoran ya bayyana shugaban kasar ta Iran da ya yi shahada da cewa, mutum ne wanda ya kasance mai hidima ga al’umma da daukaka matsayinta, wanda hakan wani darasi ne mai girma na samari da matasa da zuriyar da za ta zo a nan gaba.
Haka nan kuma Ayatullah Sayid Ali Khamnei ya yi ishara da tattaunawar da ake yi da Amurka ta hanyar shiga Tsakani, yana mai kara da cewa; Abinda Amurka ta furta cewa ba za ta bai wa Iran damar tace sanadarin uranium ba, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci za ta gaba da tafiyar akan tafarkin da take kansa.”
Jagoran na juyin musulunci ya ce, a nan gaba za yi wa al’umma bayani akan manufar da ta sa suke bijiro da wannan Magana da nanatawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aragchi Ya Musanta Zargin Da Jamus Take Watsawa Dangane sa Shirin Nukliyar Kasar
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi, ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan.
Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar koli ta tsaron kasar Iran ne, don haka ita ce zata fayyece yadda huldar shirin zai kasance tare da hukumar IAEA. Sannan Iran bata fice daga yarjeniyar NPT ba.
Kasar Jamus dai tana goyon bayan hare=hare da HKI da AMurka suka kaiwa JMI a yakin kwanaki 12, dagan cikin harda hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar. Ya ce aiki ne da bai dace ba wacce JKI ta yi madadin kasashen yamma.