2025-05-18@22:23:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 231

«sojojin mamayar»:

    Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa. Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038. An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Kuɗin mallakin Maimuna Salihu, wata maniyyaciya daga Jihar Taraba da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana. Jami’in ya mayar mata da kuɗin a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025. An gudanar da bikin miƙa kuɗin a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ciki har da jami’in Taraba, Daraktan...
    Mai Magana da yawun masu ayyukan ceto a yankin Gaza, ya sanar da cewa; Daga safiyar yau Lahadi zuwa marece adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 150. Mahmud al-Basal ya fadawa tashar talabijin din ‘almayadin’ cewa; hare-haren na HKI sun fi tsanani ne a arewacin zirin Gaza, kuma kai tsaye suke kai wa sansanonin ‘yan hijira hari. Da yake Magana akan kayan aikin da suke amfani da su domin ceto, al-Basal ya ce, kaso 75% na kayan aikinsu sun lalace, musamman motoci, kuma rashin makamashi ya sa ba za su iya amfani da su ne. Haka nan kuma ya yi ishara da amfani da yunwa da HKI take yi akan falasdinawa,sannan ya kara da cewa; Da akwai...
    Hukumomin kasar za su fitar da gamsasshen bayani mai dauke da sababbin tsauraran matakan, wadanda za su kunshi na mallakar izinin karatu da aiki a Birtaniya. Sakataren harkokin baki na Birtaniya Ybette Cooper ta bayyana wa BBC cewa lokaci ya yi da za su rage daukar ma’aikatan jinya daga kasashen waje. Ta ce wannan matakin zai taimaka wajen rage kusan mutum 50,000 wadanda ba kwararru ba ne sosai da suke shiga kasar daga kasashen ketare a duk shekara. Firaministan ya ce sababbin matakan za su taimaka wajen “sake mallake bakin iyakokin kasarmu.” Idan aka dabbaka sabbin matakan nan da gwamnatin kasar za ta dauka, ‘yan kasashen mutane daga kasashen Nijeriya da Pakistan da Sri Lanka za su fuskanci kalubale wajen...
    Dare da aka zubar da jini mafi muni a Gaza: Sama da Falasdinawa 80 ne suka yi shahada a sassa daban-daban na Zirin Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka yi sanadiyyar shahadan sama da Falasdinawa 80, kuma mafi yawansu a wani kisan kiyashi da aka yi wa ‘yan gudun hijira a yankin Al-Mawasi na Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, bayan da aka jefa bama-bamai da kona tantunansu a kusa da Asibitin kwararru na Kuwait, baya ga kisan kiyashi a duk fadin yankin. Majiyoyin Falasdinawa sun ce an kona mutane 36, yawancinsu mata da kananan yara, bayan da sojojin mamayar Isra’ila suka yi...
    Asusun kula da kananan yara “UNICEF” na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe yara 45 a Gaza cikin kwanaki biyu kacal Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe kananan yara 45 a Zirin Gaza a cikin kwanaki biyun da suka gabata, kuma wani abin tunatarwa shi ne cewa: Yara a Gaza na shan wahala da farko, suna fama da yunwa kowace rana kuma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri da muggan makamai kan mai uwa da wabi.” A cikin wata sanarwa da Asusun ya fitar a ranar Juma’a, ya jaddada yi kira da a kawo karshen wahalhalu da kashe-kashen yara a kullum....
    “Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.   “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”   Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.   Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye, kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da kare kansu ta hanyar gudanar da gwagwarmaya har sai sun kwato dukkanin Falastinu tare da kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci kai wacce Qudus zata kasance a matsayin babban birninta. A yayin bikin cika shekaru 77 da kafuwar Nakba, -boren Falasdinawa na farko- kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: “Ba za a yi wani sabon...
    A cewarsa, yanzu haka ana sayar da shinkafa kimanin naira 60,000 kan kowane buhu, buhun fulawa kan naira 55,000, da masara a kan Naira 30,000.   Ya yi bayanin cewa, kafin zartar da umarnin rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci, ‘yan kasuwa kan sayen kayan abinci tun yana gona su boye, sannan su sayar da shi a farashi mai tsada. Ya kara da cewa, “Amma a yanzu, wannan shirin ya kare, yanzu masu irin wannan halin, asara kawai suke kirgawa Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da Iran Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurka ita ce ta kawo cikas ga ci gaban al’ummar Iran ta hanyar kakaba takunkumai, matsin lamba da kuma barazanar soji da ba na soji ba, don haka ne Amurka ke haddasa matsalolin tattalin arzikin Iran. A gefen taron majalisar ministocin a yau Laraba, Araqchi ya bayyana cewa, abin da Trump ya fada game da kasashen yankin da suke son bin hanyar samun ci gaba da wadata shi ne, a hakikanin gaskiya irin tafarkin da al’ummar Iran suka bi a lokacin juyin juya halinsu, da kuma tafarkin da suka zaba na...
    A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51 Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51, ciki har da 45 a arewacin zirin Gaza. Wannan sabon tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke gudanar da ziyarar aiki a yankin gabas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran Falasdinawan “WAFA” ya watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudanci da arewacin zirin Gaza...
    Jiragen yaki marasa matuka ciki sun kai hare-hare kan sansanin sojin ruwa mafi girma a Port Sudan Sojojin tsaron saman Sudan sun dakile wani harin da jirgin sama maras matuki ciki ya yi niyyar kai wa kan mafi girman sansanin sojin ruwan kasar da sanyin safiyar Laraba, in ji wata majiyar soji. Wannan dai shi ne rana ta hudu a jere da ake kai hare-hare kan birnin Port Sudan da ke karkashin ikon gwamnati. Majiyar wadda ta bukaci a sakaye sunanta ta ce, jiragen saman yakin marasa matuka ciki sun kai hari kan sansanin sojin ruwa na Flamingo, kuma na’urorin kakkabo makamai masu linzami suna kakkabo makaman da aka harba. Tsawon rabin sa’a ana jin karar makaman roka masu linzami...
    Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”. A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu. Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza. A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza. Sojojin HKI suna ci...
    A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi.   “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri.   “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141.   “Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala,...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da matsugunan ‘yan gudun hijira da suke Gaza, a matsayin matakin farko na hare-harensu a yau Litinin. Bayan nan Sojojin mamayar sun farma garin Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza, inda suka kai wasu munanan hare-hare kan garin da jiragen saman yaki da suka aiwatar da mummunan kisan kiyashi a makarantar Fatima Bint Asad, da ya zama mafaka ga ‘yan gudun hijira. Hare-haren bama-bamai biyu da...
    ’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya. Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa. A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki. Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke yi na daƙile ayyukan ’yan ta-da ƙayar baya. “Na bayar da umarnin haramta sayar da da man...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni.   A gun gudanar da ayyukan jinyar kyauta, kwararrun likitocin kasar Sin daga bangaren aikin tiyata na gama-gari, da aikin kasusuwa, da aikin kula da mata da na sauran sassa sun gudanar da gwaje-gwajen lafiya da gano cututtuka da kuma ba da jinya cikin tsari a wurin bayar da jinya na wucin gadi da rarraba magunguna kyauta, tare da ba da cikakken jagora kan yadda...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai.  A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro. ’Yan sanda sun ƙaddamar da ƙwararrun Jami’an tsaro saboda makarantu a Bauchi An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna ƙoƙarin kare ƙasarsu sosai”. Ya bayar da tallafin Naira miliyan 2m ga kowane iyalan...
    An gudanar da taron musayar al’adu da cudanyar al’umma na murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya na jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kamfanin gidajen talabijin da rediyo na kasar Rasha suka shirya a birnin Moscow.   An karanta wasikun taya murna daga shugaban kasar Sin Xi Jinping da na Rasha Vladimir Putin a wajen taron. A jawabinsa, babban darektan CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, yayin da bikin shekarar al’adun Sin da Rasha ya kankama, bari mu dauki ruhin sakon wasiku na taya murna a matsayin jagora, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu....
    Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Nijeriya. Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa a ziyarar jaje ga gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a kan harin da aka kai wa rundunar sojijin barikin soja da ke Buni Gari. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan sun sha ‘Kayan Mata’ Ganduje ya ce dole ne yaƙi da ’yan tada ƙayar baya da ’yan fashi da makami su tafi tare da haƙiƙanin lokaci domin samun nasara....
    Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
    Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...
    “Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.”   Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro. A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a.   Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri...
    Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere.   Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da...
    A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram. Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira don jan hankalin ɗan Adam kamar intanet. Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa ’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC Haka kuma idan aka zo fannin ƙirƙirar sabuwar fasaha, ba da yawa ba ne ke irin wannan a cikin Indiyawa. Na baya-bayan nan shi ne ƙirƙirar da wani mutumin West Bengal – “motar gado” inda ya mai da gadonsa ya koma...
    “Mun rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri. Yanzu haka saura biyu da ba na hukuma ba. Mun riga mun dawo da kashi 75 na ‘yan sansanin Muna gida, saura kashi 25 za su koma cikin kwanaki masu zuwa.” Kowane iyali sun samu tallafin abinci, kayan gini da kulawar lafiya. Haka kuma, kowane magidanci mace ko namiji za a ba shi Naira 100,000, yayin da matan gidan za su ƙara samun Naira 50,000 don taimaka musu da buƙatunsu na yau da kullum. Za a Ƙara Inganta Cibiyar Koyo Sana’o’i a Gidan Gyaran Hali Tun da safiyar ranar Litinin, Gwamna Zulum ya kai ziyara gidan gyaran hali na manyan laifuka da ke Maiduguri. Ya ce za a inganta...
    Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan  sahayoniyya suke yi, ko da kuwa wani mataki ne da ya sabawa ‘yancin kai, ko cikakken amincin Iran ko kuma muhimman muradun kasa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, za a mayar da martani cikin gaggawa, da ya dace kuma halastacce. Wannan dai ya zo ne a cikin wata wasika da Amir Sa’ed Irawani, jakada kuma wakilin din-din-din na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aikewa babban...
    Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu. Daga cikin hare-haren har da hare-haren da jiragen mamayar Isra’ila suka kai kan wani gini mai yawan jama’a a unguwar Al-Karama da ke arewacin Gaza, wanda ya yi sanadin kisan kiyashi kan mutane ciki har da mata da kananan yara 20 da kuma fararen hula na daban. A wani labarin kuma, Falasdinawa a yankin Al-Karama...
    A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan. Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata. Bugu da kari, majiyar Falasdinawan ta ce, ‘yan mamayar sun kuma aike wa da wasu cibiyoyin da gidaje 46 gargadin cewa za su rushe su, da yin kira da  su fice daga cikinsu. Wata cibiyar ta Falasdinawa ta ce fada wa kamfanin dillancin labarun “Anatoli’ cewa; ;yan mamayar sun rushe gidaje 96 da mutane suke rayuwa a cikinsu, sai kuma wasu gidaje 10 da babu mutane a...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.  A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci saboda lamirinsu na ‘yan adamtaka da kuma taimako na musulunci ga ‘yan’uwansu Falasdinawa.” Bayanin ya kuma ci gaba da cewa; Jinginawa jamhuriyar musulunci ta Iran abinda mutanen na Yemen suke yi, ba shi da tushe, kuma manufar hakan ita ce, rufe laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi a Falasdinu.” Bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci tana sake jaddada matsayarta akan wajabcin kiyaye da karrama kasashe...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya caccaki tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi da cewa maƙaryaci ne da ba shi da “kunya”. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya yi tare da ilahirin kansiloli 484 da ke fadin jihar a ranar Lahadi da maraice. Kotu za ta rataye matashi kan kisan karuwa Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ba wajen zaman ɓarayi ba ce sabo da jajircewa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa. Da ya ke jawabi a wajen taron da kansilolin, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci satar kudin al’umma ba. A cewarsa, yana jagorantar gwamnati mai tsafta da kaffa-kaffa...
    Ministan Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Za su mayar da martani mai tsanani da karfi kan duk wani ta’addanci da kasarsu za ta fuskanta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake mayar da martani ga barazanar Amurka, ya tabbatar da cewa Iran za ta mayar da martani mai karfi tare da kai hare-hare kan dukkanin wasu muradun Amurka da sansanoninta da suke wannan yankin. Birgediya Janar Nasirzadeh ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da tarin makamai masu linzami, kuma idan aka kakaba mata yaki, to za ta yi amfani da su ba tare da bata lokaci ba, ko kuma a duk kan muradun makiya. Ministan ya jaddada cewa: “Ba su da wata...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya.   Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo na 35 a Ilorin.   A cewarsa, magance rashin tsaro bai kamata ya zama matsala ga kasar da ta hada karfi da karfe a ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa domin murkushe ‘yan tawaye ba.   Ya kuma shawarci gwamnati da kada ta rinka yi masu tada kayar baya ta hanyar yi musu afuwa, ya kara da cewa kada gwamnati ta tausayawa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga irin sadaukarwar da ‘yan jarida suka yi, wadanda suka rubuta irin wahalhalun da al’ummar Falastinu suke yi da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi a tsawon shekaru biyu da suka yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya rubuta a shafin sada zumunta na “X” a jiya Asabar cewa: Ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta tuna da jarumtakar ‘yan...
    Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara. Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis. Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma. Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga...
    Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin Jabaliya da al-Balad da ke arewacin zirin Gaza. Haka zalika hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 6 sannan wasu 8 suka jikkata a wani harin da jiragen saman yakin mamayar Isra’ila suka kai kan taron fararen hula da ke kusa da mahadar Abd al-Aal da ke kan titin al-Jala’a da ke arewacin birnin Gaza. A cewar majiyoyin cikin gida,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
    Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran. Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar. Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za su gudanar da cikakken binciken lafiyar maniyata kafin tafiyar su zuwa kasa mai tsarki da zai gudana a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna. Sannan kuma za su bayar da taimakon gaggawa a kasar Saudiyya tare da haɗin gwiwar Ayarin likitocin daga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON). Shugaban hukumar ya ce mambobin ayarin za su kasance cikin tsari na duba lafiyar mahajjata a tsawon lokacin...
    A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
    Rahotonni sun tabbatar da cewa: Da tsakar daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila dauke da motocin soji guda hudu da wasu sojoji masu tafiyar kafa sun kutsa cikin yankunan kasar Siriya daga titin Al-Hurriya, inda suka wuce titin Al-Kassarat, zuwa Talat Jabata Al-Khashab. Majiyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta bayyana cewa: Sojojin mayar sun kafa shingen binciken ababen hawa inda suka tsaya suna binciken ababan hawa da ke wucewa, sannan suka haska wuta don gano hanyar kafin su fita ta hanyar da suka shiga. Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma suna shawagi a sararin samaniyar birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya. A jiya Litinin ma, sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai...
    Guo Jiakun ya bayyana cewa, a ranar 26 ga wannan wata, hukumomin Sin masu ruwa da tsaki sun gabatar da sabbin matakan mayar da kudin haraji ga baki masu yawon bude ido, lamarin da ya kyautata manufar mayar da kudin haraji tun daga lokacin sayayya da kawo sauki ga baki masu sayayya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba. Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka,...
    Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Sai dai asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto. Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce “abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda.” Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar. Har yanzu dai ba a san abin...
    Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun. A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga. “Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka...
    Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki.   Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da shakatawa da wuraren raya al’adu da filayen jiragen sama da otel-otel da tashoshin tafiye-tafiye. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu. Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan Naira 70, kafin samun wannan karancin wutar lantarki, wanda a halin yanzu kuma ake sayar da ita kan Naira 120. “Muna wahalar samun ruwan sha da arha a wannan yanki namu, manyan hanyoyin samun ruwa a Kano su ne, ta hanyar rijiyoyin burtsatsai (Boreholes), sannan ana iya samun ruwan ne ta hanyar amfani da wutar lantarki. Don haka, da zarar an ce babu wutar lantarki,...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi. An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin  Zamba da ke Abuja, yayin da...
    Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas za su zaɓi cikakken sakatare wanda Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar zai amince da shi. Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke kan wanda ya cancanci ya riƙe muƙamin tsakanin Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, ta ba jam’iyyar ikon yanke shawara kan shugabanninta. Sai dai a wata takarda da Alhaji Gurama Bawa, jami’in gudanarwa na mukaddashin shugaban jam’iyyar ya fitar, ta ce...
    Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.   Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.   Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.   A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan...
    Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne  bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
    Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.   A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin Mamayar Isra’ila ta tabbatar da cewa ba za a amince da ita ba a duk wani bincike laifukan sojojinta Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake tabbatar da rashin sahihancinta wajen binciken laifukan da sojojinta suka aikata. A yayin da take tsokaci kan binciken da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi kan harin da aka kaiwa ma’aikatan jinya a Gaza, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 21 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025: Akwai zabi daya tilo na yin adalci, ta hanyar kotun hukunta manyan...
    Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma yana gudanar da wannan ta’asa ne tare da goyon bayan siyasa da na sojan Amurka, sannan kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashe sun daukin matakin yin shiru da rashin gwada wani yunkurin kalubalantar wannan danyen aiki. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama tare...
    Shugaban NDLEA, Brig.-Gen. Mohamed Buba Marwa, ya yaba wa jami’an hukumar bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da magungunan da kwayoyi na haram, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu da ke shafar safarar magunguna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi kan batun kwance damara, yayin da Hamas ta dage kan hakan a matsayin wani muhimmin hakki na kare Falasdinu. Mahmoud Mardawi na kungiyar Hamas ya jaddada cewa kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa abu ne da ba zai yiwu ba. Ya bayyana kudurin na Isra’ila a matsayin wani dabarun yahudawan sahyoniya da Amurka na kwacewa Falasdinawa karfin kare kansu da kuma tinkarar mamaya.
    Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9. Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar...
    Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su iya bin tafarkin zamanantarwa da ya sabawa na yammacin duniya.   A nasa bangare kuwa, daraktan hukumar lura da harkokin waje na kasar Masar Ezzat Saad, cewa ya yi shawarar da Sin ta gabatar ta aiwatar da manufofin zamanantar da duniya, ta samar da karin sassan hadin gwiwarta da kasashen Afirka, tare da yayata kusancin sassan biyu ta fuskar amincewa da juna da hadin gwiwarsu....
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom. Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata...
    Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin. A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya ya bayyana cewa, kungiyar Hamas a shirye take ta sako dukkan fursunonin da ‘yan gwagwarmaya ke tsare da su domin samun adadin fursunonin Falasdinawa da aka amince da su a halin yanzu da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila. Ya jaddada cewa, dole ne irin wannan yarjejeniyar ta hada da dakatar da yakin gaba daya, da janyewar sojojin Isra’ila baki daya daga Gaza,...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku. Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce kidayar na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma tsare-tsare na gaskiya.   Ya lura cewa ingantaccen bayanan yawan jama’a yana da mahimmanci don yanke shawara mai inganci a cikin manyan sassan kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da kuma tsara tattalin arziki. Shugaban ya jaddada cewa, an gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2006, wato kusan shekaru ashirin da suka wuce,...
    Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata. Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya Hakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani matashi, Umar Auwal, mai shekaru 20 da ya yi iƙirarin kashe mutane ya miƙa kansa ga rundunar ’yan sanda a Jihar Kano. Matashin mai inkiyar ‘Abba Dujal’ ya ce ya miƙa kansa ga mahukunta ne sakamakon rashin samun kwanciyar hankali tun bayan ta’addancin da ya aikata a bayan nan. Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon murya da kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook. Da yake amsa tambayoyi, Abba Dujal ya yi iƙirarin aikata manyan laifuffuka da suka haɗa da kisan kai, fashi da makami da kuma satar babur...
    Haka kuma a ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, ya amsa cewa ya kashe wani mutum sannan ya sayar da babur ɗinsa wanda ya sace a kan kuɗi Naira 300,000. Rundunar ‘yansanda ta ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kansa a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), don tabbatar da gaskiyar iƙirarin da ya yi da kuma gano ko akwai wasu da suke tare da shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da matakin da Umar ya ɗauka na miƙa kansa, tare da kira ga sauran masu laifi da su kwaikwayi irin wannan mataki. Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kawar da masu aikata laifi a faɗin...
    Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da sharudan sakin dukkan fursunonin Isra’ila da take tsare da su Wani jami’in Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: Kungiyar a shirye take ta sako daukacin fursunonin Isra’ila domin tsagaita bude wuta da ficewa daga Gaza, kamar yadda wani rahoto da tashar talabijin ta Alkahira ta fitar. Jami’in na kungiyar Hamas ya kara da cewa: A ranar litinin din nan ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma yin watsi da alkawurran da ta dauka, yana mai cewa kungiyar Hamas ta tabbatar wa masu shiga tsakani da “bukatar bayar da lamuni don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar.” Yana mai bayyana cewa,...
    Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu.   Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan Sinawa. A ganinsa, Xi Jinping babban jagora ne dake matukar mai da hankali kan abubuwan dake shafar zaman rayuwar jama’a. Ya ce duniya na bukatar musanyar al’adu sosai don kawar da bambancin ra’ayi, ta yadda za a tabbatar da wadata cikin hadin gwiwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi? HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi...
    Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2025, domin samun rahoto kan sulhun, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa. Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.” Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta...
    Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku. Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki daga sashen ilimi. Da take jawabi a wajen taron, Minista a ma’aikatar Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed Sa’id ta bayyana cewa, a ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi na ƙarfafa tsarin ilimi, ya amince da kashe Naira biliyan 120 don bunƙasa shirin fasaha da koyon sana’o’i (TVET) a Najeriya. Ministar ta kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da...
    Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin Baptist da ke birnin Gaza, lamarin da ya janyo dakatar da aiki a cikinsa Wakilin gidan talabijin na Al-Alam Mohammed Al-Balbisi ya ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu gine-gine na asibitin Baptist, da suka hada da ginin sashin kula da marasa lafiya cikin gaggawa da kuma motocin daukar marasa lafiya da wasu sassa da tantuna da ke ba da hidima ga wadanda suka jikkata. Ya yi nuni da cewa da sanyin Safiya yau Lahadi, sojojin mamayar Isra’ila sun harba makamai masu linzami da dama kan wadannan gine-gine lamarin da ya tilastawa marasa lafiya da likitoci ficewa daga asibitin tare da fakewa a...
    Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin arziki da gobarar tankar mota da ambaliyar ruwa da gobara, abin da yake biyo baya shi ne gwamnati ta raba tallafin shinkafa da sauaran kayan abinci, tamkar shinkafa ita ce maganin duk wata matsala. A wasu lokutan, a kan raba babura masu kafa uku da dabbobi a matsayin tallafi. Makudan kudaden da gwamnatoci suke kashewa da sunan bayar da tallafi, inda ba a ganin tasirin...
    Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa. Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar. Ya koka da...
    Wadda aka tsara a cikin babi shida, takardar matsayar ta gwamnati ta sake tabbatar da yanayin moriyar juna ta cinikayya tsakanin Sin da Amurka.   Ta kara da bayyana cewa, kasar Sin ba ta neman cin bulus a harkar kasuwanci, kuma bangarorin biyu sun samu riba mai yawa daga hadin gwiwar tattalin arziki da suke yi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka. Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi. ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Ma’aikatar Kuɗi ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce wannan ba mataki ne na wucin-gadi ba, sai dai tsari ne da ake son ya ɗore wanda Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, ta aminta da shi. “Wannan manufa za ta taimaka wajen bunƙasa tace mai a gida, rage...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da shirin don kula da lafiyar al’ummar jihar musamman masu karamin karfi. Dr Abdullahi Kainuwa yana mai cewar a yanzu haka gwamnatin jihar tana gudanar da aikin Dandamalin sabon asibitin kashi na garin Gumel kan naira miliyan 380. A cewar sa, za a bada kwangilar sayen kayayyakin asibitin Kashi na naira miliyan dari shida. Kwamishinan ya kara da cewar gwamnatin jihar ta kammala aikin gina dakunan...
    Kwanan nan wani mai kiwon karnuka a Indiya ya biya Rupee miliyan 500 — kwatankwacin Naira biliyan 8 da miliyan 949 da dubu 481 da 589 domin sayen wani karen kerkeci na jinsin karen Shephard Caucasian, wanda hakan ya sa karen ya zama mafi tsada a duniya. Karen mai suna Cadabomb Okami, an bayar da rahoton cewa, an yi kiwon karen mafi tsadar ne a Amurka kuma S. Satish, wani mai sha’awar kiwon kare a birnin Bengaluru da ke Indiya kuma shugaban kungiyar masu kiwon karnukan Indiya ne ya saya. NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi? ACF ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen kisan jama’a a Filato Ya shahara saboda tarin...
    Mista Abel Olumuyiwa Enitan, Sakataren dindindin na ma’aikatar Ilimi, ya tabbatar da cewa ma’aikatar tana shirye don ƙara yin haɗin gwuiwa tare da NYSC domin inganta tsarin ilimi a Nijeriya.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar da ayyukan gwagwarmayar Yeman na goyon bayan al’ummar Gaza ko kuma kare jiragen Isra’ila a tekun Bahar Rum. A wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a, Abdul-Malik al-Houthi ya ce Amurka ta zafafa kai hare-hare a kan kasar Yemen, inda wasu lokutan ta kai hare-hare sama da 90 a kowace rana, a wani bangare na goyon bayan da take baiwa kasar Isra’ila a yakin kisan kare dangin da ta ke yi a zirin Gaza. Duk da haka, ya jaddada cewa, hare-haren na Amurka “sun kasa dakatar da ayyukan soji da ke tallafawa al’ummar Falasdinu,...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Al’ummar musulmi suna fuskantar manyan hatsari guda biyu,  da su ka hada laifukan da HKI take tafkawa a Gaza, da kuma kokarin shafe hakkokin falasdinawa baki daya. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma tabo batun keta tsagaita wutar yaki da HKI take yi a kasar Lebanon yana mai kara da cewa, keta hurumin kasar Lebanon da ‘yan sahayoniyar suke yi, ya isa har birnin Beirut. Akan kasar Syria ma, jagoran na kungiyar Ansarullah na Yemen ya yi ishara da hare-haren da ‘yan sahayoniya su ka kai  a cikin biranen Damascus, Hums da Dar’a. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce,abokan gaba sun mayar da keta hurumin kasashen al’umma abinda za...
    Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
    Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama. Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin. An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba. Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu. A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu. Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara Wang, ya yi...
    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari. Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka “Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi. Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran...
    Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi.   Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen maidowa tare da kiyaye wuraren tarihi, kayayakin tarihi, da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in cikin gida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...