Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Gombe, Asma’u Muhammad Iganus, ta ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa ’yar shekara biyu, Maryam Buba da ake zargin mijin mahaifiyarta, Muhammad Magaji mai shekara 47, da yi mata fyaɗe.

Kwamishiniyar tare da tawagarta sun kai ziyara gidan iyalan yarinyar da ke unguwar Jauro Innayo a Gombe, inda ta tausaya mata tare da ba su kayan tallafi kamar su pampers, sabulai da kuma kuɗi.

’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 26 a ƙauyukan Zamfara Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su

Asma’u ta sha alwashin cewa za a bi duk matakan shari’a domin ganin wanda ake zargi ya fuskanci hukunci.

Ta ce gwamnati na mara wa ɓangaren shari’a baya don ganin an samu adalci.

Ta jaddada ya kamata a yi wa wanda ake zargi hukuncin ɗaurin rai da rai matuƙar an same sa da laifi, domin hakan zai zama izina ga masu irin wannan ɗabi’a.

Mahaifiyar yarinyar, Hauwa’u Usman, ta gode wa Kwamishiniyar bisa goyon bayan da ta bayar da kuma addu’a a gare ta.

Ta kuma buƙaci gwamnati ta hukunta mijinta da tsauraran hukunci.

Daga bisani Kwamishiniyar, ta nufi hedikwatar ‘yan sandan Jihar Gombe don ganawa da Kwamishinan ‘yan sanda Bello Yahaya.

Sai dai ba ta same shi ba saboda yana bakin aiki.

Duk da haka, ta bar saƙo masa na gudanar da bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a kotu.

Muhammad Magaji, wanda ake zargi da laifin, yana hannun ’yan sanda kuma suna kan bincike.

Rundunar ’yan sandan ta tabbatar da cewa za a gurfanar da shi a kotu da zarar ta kammala bincike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda fyaɗe Kwamishiniya yarinya zargi wanda ake zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu Ta Daure Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Mutum A Gidan Yarin Adamawa

Wadanda ake tuhumar dai, a cewar rahoton farko, sun yi wa mamacin dukan tsiya har sai da ya suma, inda aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Hong inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

 

 

Dukkan wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.

 

Kotun da ke karkashin Alkali Uwani Danladi, ta bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a gidan gyaran hali don bai wa ‘yansanda damar kammala bincike tun da har yanzu akwai sauran mutum daya da ake tuhuma.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu Ta Daure Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Mutum A Gidan Yarin Adamawa
  • Kwamishiniya ta nemi a hukunta wanda ake zargi da yi wa ’yar matarsa fyaɗe a Gombe
  • Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su
  • Mawaƙan APC sun zargi gwamnati da watsi da su a Jigawa
  • Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200
  • Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya ba su kyautar Riyal 200
  • APC Ta Zargi Gwamnan Zamfara Da Shirga Karya Tare Da Kiran Ya Nemi Afuwar Zamfarawa
  • Iran Ta Jaddada Kawo Karshen Bakar Siyasar gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Kan Al’ummar Falasdinu
  • Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara