Gwamna Abdulrazaq Ya Jajanta Wa Wadanda Hatsarin Jirgin Ruwan Gbajibo Ya Rutsa Da Su
Published: 19th, May 2025 GMT
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya aika ta’aziyya ga iyalan mutane 37 da hatsarin kwale-kwalen Gbajibo ya rutsa da su daga jihar Neja a karshen mako.
A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja kan wannan lamari mai ban tausayi.
Gwamnan ya bukaci ma’aikatan jirgin da fasinjoji da su bi ka’idojin tsaro domin amfanin kowa.
Ya bayyana a matsayin al’ada mai raɗaɗi kuma ba za a yarda da ita ta rashin amfani da na’urorin kariya da gwamnati ta bayar akai-akai.
Yana rokon Allah ya jikan wadanda aka kashe.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria