2025-05-15@22:56:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2730

«Sheikh Alƙali Zariya»:

    Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya...
    Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya mayar da martani ga shugaba Donald Trump na Amurka, yana mai cewa Iran kasa ce son zaman lafiya ba yaki ba. Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba; Su ne ke haifar da rikici. Muna fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar nan da ma makwabtanmu,...
    Iran ta bayyana cewa za ta yi zama gobe Juma’a da kasashen nan na turai guda uku da ake kira E3, wato Biritaniya, Jamus da kuma Faransa kan shirinta na nukiliya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa, a ranar Juma’a 16 ga watan Mayu ne za a yi shawarwari karo na...
    Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Aljeriya su hada kai wajen kai kayan agaji a zirin Gaza da yaki ya daidaita. Qalibaf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar al’ummar kasar Aljeriya Ibrahim Boughali a ranar Laraba a birnin Jakarta na...
    A ranar Alhamis din nan, wasu hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai sun kai ziyara hedikwatar hukumar ta NOA inda suka yi amfani da damar wajen lekawa daya daga cikin kayayyakin tarihin Nijeriya a baya – ofishin marigayi shugaba Shagari. Bayan kammala ziyarar, daya daga cikin hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai,...
    A makon nan ne aka ga hotunan Sheikh Alƙali Zariya ya halarci zauren tattaunawa na fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, wanda ake kira ‘Gabon Talkshow’, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Gabon Talkshow dandali ne da jaruma Hadiza ke gayyatar mashahuran jarumai da mawaƙa domin tattauna game da rayuwarsu da ayyukansu...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron daji a faɗin ƙasar nan domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a cikin dazukan Najeriya. A ƙarƙashin wannan sabon shiri, za a ɗauki sama da mutane 130,000 aiki da za su samu horo na musamman da kayan yaƙi na zamani domin...
    Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. ’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai...
    An ce, ‘yan bindigar sun yi galaba a kan masu gadin fadar, inda suka tafi da sarkin zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.   Da take tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ‘yansandan jihar Kogi ta ce, an fara gudanar da bincike, inda ta ce rundunar hadin gwiwa da ta kunshi...
    Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara jihar. A watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, ya mari Minista Tuggar a cikin mota yayin da suke kan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini. Dr. Baka’i ya yi ishara...
    Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita. Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da...
    A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar. Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban Jami’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, sun riƙe mutanen da suka kai musu kuɗin fansarsa, sa’annan suka ƙara ƙudin fansar da suka nema da ninki shiga. A ranar Litinin da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Honorabul Nelson Adepoyigi...
    Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan...
    A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya, – amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban Amurka...
    Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar hukumar kula da manyan makarantu ta jihar Kaduna, ta shekarar 2025, ya zama doka. Dokar dai na da nufin daidaita harkokin gudanar da manyan makarantun sakandire a fadin jihar domin daidaita tsarin ilimin zamani.   Da yake jagorantar zaman majalissar, mataimakin kakakin majalisar Mista Henry Magaji Danjuma...
    Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano, domin bayar da takardar shaidar difloma ga masu amfani da shafukan sada zumunta da ke da hannu wajen tallata manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf.   Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan...
    A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki. Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar. “Ina ganin idan...
    Jagoran juyin juyala halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, ya zargi kasashen yamma da goyon bayan kissan kare dangin da ke faruwa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da wadanda suka shirya taro na farko don...
    Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa kasarsa bata boye wani wuri inda take sarrafa makamashin Nukliya wanda bata fadawa hukumar IAEA ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Laraba, kuma don kare matsayin Iran na mallakar fasahar nukliya ta...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai,...
    Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar. Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata...
    A nasa bangare kuwa, shugaba Boric ya ce, kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ga kasarsa, kuma hadin gwiwarsu ya ba da tallafi ga al’ummomin kasashen biyu. Kazalika kasar Chile tana fatan yin hadin gwiwa da Sin wajen kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka da kiyaye karfin MDD, tare da kuma kare yanayin adalci na kasashen...
    Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.   Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma...
    Kasafin kudi na birnin tarayya Abuja (FCT) na shekarar 2025, kimanin naira tiriliyan 1.78 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisa, ya tsallake karatu na biyu. Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin FCT na 2025 ta wata wasika da ya aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen...
    Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani kan ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Siriya, Ali al-Julani, a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar Laraba. A cikin...
    A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51 Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51,...
    Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana.   “Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga...
    Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan...
    Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin...
      Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.   Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni...
    Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta...
    A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa...
    Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu. Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da...
    A yau Laraba ne dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya birnin Jakarta na kasar Indonesia, da zummar halartar taron wakilan majalisun kasashen da suke mambobi a kungiyar kasashen musulmi. Taron na wannan karon a kasar Indonesia shi ne karo na 19 da kungiyar ta kasashen musulmi take yi a matakin...
    Makaman sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu. CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami. Ya ce wasu jami’an da suka halarci wani horo...
    Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da...
    Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar...
    Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare. Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an...