HausaTv:
2025-10-13@17:12:17 GMT

CAN U20 : Afirka ta Kudu ta lashe kofi na farko

Published: 19th, May 2025 GMT

Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa na ‘yan kasa da shekara 20 ta Afrika ta Kudu ta lashe kofin gasar CAN a karon farko bayan da ta doke takwararta ta Morocco (1-0) a wasan karshe da aka buga a birnin Alkahira jiya Lahadi.

Kafin hakan Najeriya ta samu matsayi na uku a gasar bayan da ta doke Masar mai masaukin baki a bugun fenariti (1-1; 4-1 a bugun fenariti).

Kasashen guda hudu da suka fafata a wasan kusa da na karshe wato (Afirka ta Kudu, Morocco, Najeriya, Masar) sun samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 a kasar Chile da za’a gudanar daga ranar 27 ga Satumba zuwa 19 ga Oktoba, 2025.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi birnin Rome na Ƙasar Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan sha’anin tsaro.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya ce za a fara taron ne a ranar 14 ga watan Oktoba, kuma zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar yankin Yammacin Afirka.

’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina

Taron na ‘Aqaba Process’ an kafa shi ne a shekarar 2015 ta hannun Sarki Abdullah II na Ƙasar Jordan, kuma ana gudanar da shi tare da haɗin gwiwar Jordan da ƙasar Italiya.

Taron na nufin tattauna hanyoyin yaƙi da ta’addanci da kuma magance matsalolin tsaro da ke adabbar ƙasashe daban-daban, musamman a yankin Yammacin Afirka.

Taron zai haɗa shugabannin ƙasashe na Afirka, jami’an leƙen asiri da na tsaro, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na ƙungiyoyin fararen hula, domin tattauna yadda za a magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Za a tattauna kan yadda ƙungiyoyin ta’addanci ke yaɗuwa a Yammacin Afirka, alaƙa tsakanin masu laifi da ’yan ta’adda, da kuma alaƙar da ke tsakanin ta’addanci a yankin Sahel.

Hakazalika, za a tattauna yadda za a daƙile yaɗuwar aƙidar ta’addanci a Intanet da kuma lalata hanyoyin sadarwar da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen yaɗa ra’ayoyinsu da ɗaukar sababbin mabiya.

Shugaba Tinubu zai kuma tattauna da wasu shugabannin ƙasashe don neman hanyoyin daƙile matsalar tsaro da ke addabar yankin.

Tinubu ya samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu–Ojukwu; Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Sauran sun haɗa daMai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed; da wasu manyan jami’an gwamnati.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
  • Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola
  • Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
  • Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta
  • Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar .