Yanzu-Yanzu: Ana Zargin Makiyaya Sun Kashe Mutane 15 A Benuwe
Published: 19th, May 2025 GMT
Ana zargin wasu makiyaya sun kashe mutane 15 a yankunan Ogwumogbo da Okpo’okpolo na ƙaramar hukumar Agatu dake jihar Benuwe.
Majiyoyinmu sun bayyana cewa waɗanda aka kashe sun kasance ‘yan kasuwa ne da ke dawowa daga kasuwar Oweto a Agatu lokacin da maharan suka fito daga daji suka harbe su, inda suka kashe 15 nan take.
Tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da harin da aka kai wa ‘yan kasuwar a ranar Asabar da yamma, inda ya bayyana cewa maharan sun kwace kuɗaɗe da kayayyakin waɗanda aka kashe kafin su gudu cikin daji.
“Har yanzu wasu mutane sun ɓace ba a same su ba, yayin da waɗanda suka jikkata an kai su wani asibiti a yankin,” in ji Ikwulono.
Kakakin Ƴansandan jihar, Catherine Anene, ta ce har yanzu ba a sanar da ita cikakken bayani kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe ‘Yan Kungiyar Shabab 19 A Kasar Somaliya
Sojojin kasar Somaliya sun sanar da kai wani farmaki a kudancin kasar da ya yi sanadiyyar kashe 19 daga cikin ‘yan kungiyar ‘al-shabab’.
Sanarwar wacce tashar talbijin din ‘almayadin’ ta nakalto ta ce, sojojin na Somaliya sun kai harin ne a jiya Litinin da dare a yankin Jubayi, wanda kuma bayan kashe ‘yan kungiyar an kuma jikkata wasu da dama.
Ma’aikatar tsaron kasar Somaliya ta kuma ce; sojojin kasar sun yi nasarar kama makamai masu yawa a tare da kungiyar ta ‘al-shabab’.
A cikin watan Disamba na shekarar da ta shude ma dai sojojin na Somaliya su ka yi nasarar kashe ‘yan kungiyar su 130 a jahohin Gulmadag, da Jubaland.