An tafka asara bayan gobara ta ƙone Kwalejin Sheikh Dahiru Bauchi
Published: 18th, May 2025 GMT
Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta.
Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu.
An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.
Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun gode wa Allah da ba a rasa rai ko samun rauni ba.
“Lamarin ya faru ne bayan an kammala karatu da yamma, kuma muna godiya ga jami’an kashe gobara da suka kwashe sa’o’i suna ƙoƙarin kashe wutar,” in ji shi.
Ya ce makarantar na da alaƙa da Jami’ar Azhar da ke ƙasar Masar, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo ne ya ƙaddamar da ita.
A cewarsa, makarantar kwana ce da ke bayar da ilimin boko da na Islamiyya tare da koyar da sana’o’i.
Kowace shekara ana yaye mahaddatan Alƙur’ani da dama a makarantar.
Ya ce an rasa litattafan Sheikh Dahiru Bauchi da na sauran malamai da dama, ciki har da kwamfutoci da kayan aikin makaranta.
Hukumar kashe gobara ta Jihar Bauchi ta bayyana cewa gobarar ta ƙone littattafai kusan 7,228, suturar ɗalibai kusan 583, gadaje 250, darduma mai faɗin mita 355, kujerun cin abinci 324, katifu, jakunkuna, kayan girki da sauran muhimman takardu da hotuna guda 150.
Ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai Gobara Kayan Karatu
এছাড়াও পড়ুন:
Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina
Bayanai daga makusantan fitaccen attajirin nan da ya riga mu gidan gaskiya, Alhaji Aminu Ɗantata sun nuna cewa an ɗage jana’izarsa da aka shirya gudanarwa bayan sallar La’asar a ranar Talata.
Yanzu an mayar da jana’izar zuwa bayan Magariba a haramin birnin Madina.
Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautuA wata zantawa da ya yi da BBC, Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya bayyana cewa tuni gawar Alhaji Aminu ta isa birnin na Madina.
“Alhamdu lilLah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya shi kafin daga bisani a kai shi haramin Madina domin gudanar da sallah kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince,” in ji Mustapha Junaid.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ake sauya lokacin jana’izar mamacin wanda da farko aka ruwaito cewa za a gudanar a ranar Litinin kamar yadda Ministan Labarai, Mohammed Idris ya tabbatar.
A karon na farko dai, Ministan ya ce an ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.
A cewarsa, “akwai ƙa’idoji da Gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar.
“Saboda haka yanzu ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin Gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,” in ji Ministan.
Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya.
Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.
Alhaji Aminu Ɗantata yana da burin binne shi a birnin Madina, inda kuma ’yan uwansa suka nemi amincewar hukumomin Saudiyya game da buƙatar kuma aka sahale musu.
Tun da safiyar Litinin ce tawagogin Gwamnatin Tarayya da na Gwamnatin Kano suka tafi Saudiyyar domin halartar jana’izar da aka shiryi yi a ranar Litinin din.
Daga cikin tawagogin akwai Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Haka kuma, akwai tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da kuma malamai irinsu Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Dakta Bashir Aliyu.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Asabar da ta gabata ce dai bajimin ɗan kasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa.